Abin da ya sa muka tara wa Ciroki kudi – Aisha Falke

Abin da ya sa muka tara wa Ciroki kudi – Aisha Falke

Shafin sada zumunta na Instagram na Northern_hibiscuss ya bayyana abin da ya sa suka tara wa Bashir Bala Ciroki kudi sama da naira 200,000 a ranar Talata, 22 ga watan Janairu.

An fara tara wa daya daga cikin `yan wasan farko da suka shahara a masana'antar fina-finan Hausa ne bayan da aka samu labarin cewa yana tallan kunun aya.

Aisha Falke, mai shafin Northern_hibiscuss ta ce sun tallafa wa dan wasan ne saboda tausayi.

A baya dai Ciroki ya kasance daya daga cikin wadanda suka yi tashe a zamanin lokacin su Ibro, Kulu da sauransu.

Abin da ya sa muka tara wa Ciroki kudi – Aisha Falke
Abin da ya sa muka tara wa Ciroki kudi – Aisha Falke
Asali: UGC

A wata hira da gidan talabijin na Arewa24 , Ciroki ya yi ikirarin cewa masu shirya fina-finai da jaruman Kannywood sun daina sanya shi a fim, shi ya sa a yanzu yake sayar da kunun aya domin ya tallafa wa kansa da iyalansa.

A nashi bangaren Ciroki ya yi jawabin godiya ga shafin Northern_Habiscuss wadda a cewarsa babu na dayansu. Yace ya gode da Allah ya sa tausayinsa a zuciyoyinsu.

KU KARANTA KUMA: An lakada wa wani mutun duka bayan an kama shi yana cin burodi da kashi

Yace jarin da suka bashi na N215,000 zai tallafa masa matuka wajen siyan injin nika da sauran kayayyaki da kuma daukar Karin ma’aikata da za su samu su ci abinci a karkashinsa.

Sannan kuma ya mika godiya ga Hajiya Malika daga kungiyar matan Arewa, Babanchinnedu da kuma Rarara mawakin Buhari cewa ya ji shigan kudin a asusunsa wanda suka tura masa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel