Bayan Bidiyon Ummi Nuhu, Mai Dawayya Ya Yi Tone Tone, Ya Faɗi Shura da Ya Yi a Baya

Bayan Bidiyon Ummi Nuhu, Mai Dawayya Ya Yi Tone Tone, Ya Faɗi Shura da Ya Yi a Baya

  • Fitaccen mawaki Aminu Lajawa Mai Dawayya ya bayyana irin nasarorin da ya samu a lokacin da ya yi fice a Kannywood da waka
  • Ya ce a wancan lokaci ya taimaki mutane da dama, kuma babu mawakin da ya yi tashe da bai amfana da shi ba
  • Yanzu kuwa ya ce Allah ya jarrabe shi da rashin arziki, hatta mota ko keke bai mallaka ba, amma yana godewa Allah

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Kano - Fitaccen mawakin Hausa da aka taba yi a jihar Kano, Aminu Lajawa Mai Dawayya ya yi magana kan rayuwarsa.

Mai Dawayya ya tabo batun shura da kuma arziki da ya yi a lokacin inda ya godewa Allah kan ni'imarsa.

Mai Dawayya ya fadi yadda ya taimaki mutane a baya
Mai Dawayya ya tuna damar da ya samu a baya. Hoto: Aminu Mai Dawayya.
Source: Facebook

Mai Dawayya ya magantu kan rayuwarsa a baya

Mai Dawayya ya bayyana haka ne a cikin wata hira a bidiyo da RFI Hausa wanda aka wallafa a shafin Facebook a yau Lahadi.

Kara karanta wannan

Jarumin fim, Don Richard ya talauce, yana neman taimakon N30m daga 'yan Najeriya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cikin bidiyon, Mai Dawayya ya bayyana yadda ya taimaki mutane da dama a lokacin da yake kan ganiyarsa a masana'antar Kannywood.

Ya yi alfahari kan yadda ya tsayar da fitattun mawaka cak a wancan lokaci saboda yadda ya faso gari.

A cewarsa:

"To Alhamdulillah, wato kamar yadda kuka sani ita rayuwa, yau gare ka gobe ga dan uwanka, kuma Allah shi ne bai badawa kuma mai karbewa.
"Lokacin da muka yi tashe gaskiya kowa sai da na tsayar da shi cak duka mawaka lokacin da na ke Mai Dawayya.
"Alhamdulillahi tun ina acaba ni masoyin Ali Nuhu ne ina zuwa ofishinsa da Rukayya Dawayya dalilin samun sunana kenan."
Mawaki a Kano ya tuna rayuwarsa ta baya
Mawaki a Kano, Aminu Mai Dawayya ya ce babu mawakin da bai more shi ba a baya. Hoto: Legit.
Source: Original

Alfaharin da Mai Dawayya ya yi kan mawaka

Mai Dawayya ya kara da cewa duk wani mawaki wanda ya ke tashe a wancan lokaci sai da ya more shi fiye da tunani.

Ya bayyana cewa a wancan lokaci yana da arziki amma yanzu Allah ya jarrabe shi da karayar arziki ko keke ba shi da shi a matsayin abin hawa.

Kara karanta wannan

'Yadda Tinubu ya ɗauko gagarumin aiki tun na zamanin Shagari saboda ƙaunar Arewa'

Ya kara da cewa:

"Lokacin da muka yi tashe, ba fariya ba duk wanda ya yi suna a mawaka idan ya ce bai more ni ba ya yi karya.
"Lokacin ina da kudi amma yanzu Allah ya kawo min karayar arziki ba ni da shi, a yanzu mota ko keke ban da shi.
"Sai da ta kai ta kawo idan na shiga Kannywood idan aka ganni ana gudu na ga Mai Dawayya nan ai dan maula ne.

Mawakin ya kuma ja kunnen masu zaginsa duk lokacin da ya je wurin jarumai ana gudunsa cewa shi ɗan maula ne.

"Duk wanda ya zage ni bari na fada musu duk wanda yake yin fim daga Katafawa, Inyamurai, Yarbawa, Fulani har ma da mu Hausawa duk yan maula ne."

- Cewar mawaki Mai Dawayya

Rarara ya magantu kan waka da amaryarsa

Kun ji cewa shahararren mawakin siyasa, Dauda Kahuta Rarara ya ce yana da ikon yanke hukuncin ko amaryarsa Aisha Humairah za ta ci gaba da waka.

Kara karanta wannan

"Ya cika su": Minista ya yi bayani kan alkawuran da Tinubu ya yi wa Arewa

Mawakin ya bayyana cewa sun saba aikin waka tun kafin aure, don haka babu matsala idan suka ci gaba da aiki tare.

Rarara ya ce wannan magana ce tsakaninsu, ba sai sun bayyana wa duniya ba, kuma ya bar masu sauraro su yi hukuncinsu da kansu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.