Hamisu Breaker da Wasu Fitattun Ƴan Fim, TikTok da Kotu Ta Tura Gidan Yari a 2025

Hamisu Breaker da Wasu Fitattun Ƴan Fim, TikTok da Kotu Ta Tura Gidan Yari a 2025

  • Fitattun ’yan TikTok da jaruman Kannywood sun fuskanci fushin kotuna a 2025 bisa laifin cin zarafin Naira da tallata rashin kunya
  • Kotuna a Kano da Kaduna sun yanke hukuncin dauri da tarar kudi ga Hamisu Breaker, Murja Kunya da wasu 'yan masana'antar nishadi uku
  • Wannan ya janyo muhawara mai zafi tsakanin masu kare al’adu da masu goyon bayan ’yancin bayyana ra’ayi a soshiyal midiya

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kano - Shekarar 2025 ta zamo abar tunawa a masana’antar nishadi a Arewacin Najeriya, inda fitattun ’yan TikTok, mawaka da jaruman Kannywood suka gamu da fushin hukuma.

Wasu daga cikin shahararrun 'yan masana'antar kamar Murja Kunya, Hamisu Breaker, sun shiga hannun EFCC da hukumar tace finai-finai sakamakon cin zarafin Naira da kuma yunkurin lalata tarbiya.

Kotuna a Kano da Kaduna sun yanke wa wasu fitattun matasa hukuncin dauri a gidan yari ciki har da Hamisu Breaker
Mawakin Kannywood, Hamisu Breaker | Fitacciyar 'yar TikTok, Murja Ibrahim Kunya. Hoto: Hamisu Breaker Dorayi, Murja Ibrahim Kunya
Source: Facebook

Yayin da al’ada ke karo da shahara ta kafafen sada zumunta, shari’o’in da aka yi kan wadannan fitattun mutane sun tayar da kura a soshiyal midiya da kafafen yada labarai.

Kara karanta wannan

'An yaudare su,' Wasu tsofaffin 'yan majalisar Arewa na adawa da tazarcen Tinubu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A wannan rahoto, Legit Hausa ta tattaro bayanai game da wasu fitattun masu nishadantarwa na Arewa biyar da kotu ta yankewa hukunci

Shahararrun mutane da aka yanke wa hukunci

1. Murja Ibrahim Kunya

Murja Ibrahim Kunya, tauraruwar TikTok kuma tsohuwar ‘yar wasan Kannywood, ta gamu da fushin alkali kan laifin cin zarafin kudin Najeriya.

Hukumar EFCC ce ta kama Murja Kungiya a watan Janairun 2025 bayan wani bidiyonta ya bulla a soshiyal midiya, inda aka ganta tana watsa kudi da tattaka su a wani taro a Kano.

Da farko dai, Kunya ta tsere bayan an bayar da belinta, amma jami'an EFCC suka sake kama ta a watan Maris din 2025, a cewar rahoton hukumar.

Murja ta amsa laifinta kuma kotu ta yanke mata hukuncin daurin watanni shida a gidan yari tare da zabin biyan tarar ₦50,000.

Abin ban sha'awa, mun ruwaito cewa kotu ta kuma sanya ta a matsayin jakadiyar EFCC da CBN don taimakawa wajen wayar da kan jama'a game da cin zarafin Naira.

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun yi musayar wuta da 'yan bindiga a Katsina, an dakile hare hare 2

Murja, wadda ke da miliyoyin mabiya, ta sha shiga komar hukumar Hisbah saboda wallafa abubuwan badala a soshiyal midiya.

2. Abubakar Ibrahim (G-Fresh)

Wata kotu a Kano ta yanke wa shahararren dan TikTok, Abubakar Ibrahim, wanda aka fi sani da G-Fresh, hukuncin dauri saboda samunsa da laifin cin zarafin Naira.

An kama G-Fresh ne a bidiyo yana watsa wa da kuma tattaka takardun ₦1,000 da suka kai jimillar ₦14,000 a watan Nuwamba na 2024.

Lamarin ya faru ne a shagon Rahma Sa’idu da ke Tarauni, jihar Kano, wanda ya saba wa Sashi na 21(1) na Dokar CBN.

G-Fresh ya amsa laifinsa bayan da EFCC ta gabatar da hujjojin bidiyo, inda kotu ta yanke masa hukuncin daurin watanni biyar a gidan yari tare da zabin biyan tarar ₦200,000.

EFCC ta tuhumi Hamisu Breaker da laifin cin zarafin Naira a wani taro da ya halarta a jihar Jigawa a watan Nuwamban 2024.
Kotu ta daure fitaccen mawaki, Hamisu Breaker kan laifin cin zarafin Naira. Hoto: Hamisu Breaker Dorayi
Source: Instagram

3. Hamisu Sa’id (Hamisu Breaker)

Hamisu Sa’id, ko Hamisu Breaker, wani fitaccen mawakin Kannywood ne, wanda babbar kotun tarayya da ke Kano ta yanke wa hukunci tare da G-Fresh a ranar 24 ga Yuli, 2025, inji rahoton EFCC.

Kara karanta wannan

Dakarun sojoji sun ragargaji 'yan ta'addan ISWAP, an tura miyagu barzahu

Hukumar EFCC ta tuhumi Hamisu Breaker da laifin watsa kudi 'yan takardar ₦200 a wani taro da ya halarta a jihar Jigawa a watan Nuwamban 2024.

Legit Hausa ta ruwaito cewa wannan lamarin na Nuwamba 2024 ya saba wa Sashi na 21(1) na Dokar CBN ta 2007, wanda ya zama cin zarafin kudin Naira.

Bayan lauyan EFCC, Zarami Mohammed ya gabatar da hujjoji, Hamisu Breaker ya amsa laifinsa, wanda ya sa Mai Shari'a S.M. Shuaibu ya yanke masa hukunci.

Mai Shari'a Shuaibu ya yankewa Hamisu Breaker hukuncin daurin watanni biyar a gidan yari tare da zabin biyan tara ₦200,000.

4. Muhammad Kabir Sa’ad (@youngcee0066)

Muhammad Kabir Sa’ad, fitaccen matashi a kafofin sada zumunta daga Kaduna, wanda aka fi sani da @youngcee0066, ya fada komar EFCC da ya raina.

Hukumar EFCC ta rahoto cewa ta cafke Muhammad Sa'ad kan zargin cin zarafin Naira bayan ya kalubalance ta a kan ta kamashi idan ta isa.

Ya wallafa wani bidiyo yana watsa kudi tare da tattaka su, har ma ya kalubalanci EFCC da ta kama shi idan za ta iya, wanda ya saba wa Sashi na 21(3) na Dokar CBN ta 2007.

Kara karanta wannan

Hankula sun tashi bayan barkewar rikicin kabilanci a Abuja, an tafka barna

An kama shi a watan Afrilun 2025 kuma ya amsa laifuffukansa, wanda ya sa kotu a Kaduna ta yanke masa hukuncin daurin watanni shida a gidan yari tare da zabin biyan tarar ₦300,000.

5. Abubakar Usman (Kilina)

Mun ruwaito cwa kotu ta daure fitaccen dan TikTok kuma jarumi a Kannywood da ke Kano, Abubakar Usman, wanda aka fi sani da Kilina saboda yada dabi'ar rashin kunya a intanet.

Hukumar tace fina-finai ta jihar Kano ce ta kama Kilina saboda sanya tufafin mata da kwaikwayon dabi'unsu (Daudu) da kuma amfani da munanan kalamai a bidiyonsa, wanda ya saba wa dokokin tarbiya na jihar.

Wata kotun majistare ta yanke masa hukuncin daurin shekara guda a gidan yari tare da zabin biyan tarar ₦100,000, kuma ta umurce shi ya biya karin ₦30,000 ga hukumar.

Shari'arsa misali ne bayyananne na yadda hukumomin Kano ke tsaurara aiwatar da dokokin tarbiya a masana'antar nishadantarwa.

Hukumar EFCC ta zage damtse wajen kama wadanda ke cin zarafin Naira
Hedikwatar hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC) da ke a birnin tarayya Abuja. Hoto: @officialEFCC
Source: Facebook

Tasirin hukunce-hukuncen a masana'antar nishadi

Wadannan jerin hukunce-hukunce sun nuna cewa shaharar mutum a kafafen sada zumunta ko waka ko fim ba kariya ba ce daga fushin doka da al’adu a Arewacin Najeriya.

Kara karanta wannan

Siyasa: Rikici ya yi kamari a SDP, an tura mutanen El Rufa'i kurkuku

Ta hanyar gurfanar da wadannan fitattun matasa, EFCC da hukumar tace fina-finai sun kara nuna cewa za su dauki matakin shari'a ga duk wanda ya saba doka ko ya nemi lalata tarbiyar jama'a.

A yayin da masana’antar nishadi ke kara fadada a Arewa, wadannan shari'o'in za su iya zama jan kunne ga sauran masu tasowa a masana'antar nishadi.

Da wannan za a iya cewa, dole ne a daidaita shahara da mutunta doka da al’ada, in ba haka ba kuwa, shahara na iya kai mutum kai-tsaye gaban kotu.

Jaruman Kannywood 10 da suka fi yawan mabiya

A wani labarin, mun ruwaito cewa, jaruman masa'antar Kannywood na amfani da shafukan sada zumunta wajen tallace tallace, dora hotuna da bidiyo da kuma tattaunawa da masoyansu.

Ali Nuhu shi ne jarumin da ya fi kowa yawan mabiya a shafukan sada zumunta, inda ya tara jimillar mabiya miliyan 8.5 a dukkanin shafukansa hudu (Facebook, TikTok, X da Instagram.)

Rahama Sadau ce ke bin bayan Ali Nuhu da mabiya miliyan 6.1, sai kuma jaruma Hadiza Gabon da mabiya miliyan 6 da kuma Naziru Ahmed (Sarkin Waka) da mabiya miliyan 4.2.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com