'Wata ce Ta Musulunta': Jarumar Kannywood Ta Faɗi Dalilin Shigar Ta Harkar Fim

'Wata ce Ta Musulunta': Jarumar Kannywood Ta Faɗi Dalilin Shigar Ta Harkar Fim

  • Jarumar Kannywood, Nusaiba Muhammad Ibrahim wacce aka fi sani da Sailuba, ta ce musuluntar wata ce ya ja hankalinta zuwa fim
  • Ta ce fim yana burge ta tun da farko, amma ganin yadda wani fim ya sa wata ta karɓi Musulunci ne ya ƙarfafa niyyarta
  • Nusaiba ta bayyana cewa tana harkar fim kusan shekaru takwas yanzu, kuma tana fatan zama mai bayar da umarni nan gaba

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Kano - Fitacciyar jarumar fina-finan Kannywood ta yi magana kan dalilin shigar ta masana'antar da take sha'awa tun tana ƙarama.

Jarumar Kannywood, Nusaiba Muhammad Ibrahim ta bayyana yadda ta taso da sha'awar harkar fina-finai a rayuwarta.

Jarumar Kannywood ta fadi dalilin shigar ta fim
Sailuba Dadin Kowa ta fadi shekarun da ta shafe a fim. Hoto: Maldax Textiles.
Source: Facebook

Jaruma Sailuba ta fadi dalilin shiga harkar fim

Nusaiba wacce aka fi sani da Sailuba Dadinkowa ta bayyana haka yayin hira da Leadership Hausa wanda aka wallafa a jiya Asabar 26 ga watan Yulin 2025.

Kara karanta wannan

'Abin da ya sa gwamnonin PDP da APC ba su sauya sheƙa zuwa jam'iyyar ADC ba'

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sailuba ta bayyana Musuluntar wata ce dalilin fim musabbabin shigar ta harkar wanda daman tun tuni tana sha'awar shiga.

Ta ce a lokacin ta fara sha'awa saboda idan sai fim zai sanya mutum ya musulunta to abin alheri ne.

Mamakin jaruma Sailuba game da tasirin fim

Ta ce ba ta taba tsammanin har darasin da ake dauka zai sa wata ta musulunta dalilin fim ba a wancan lokaci.

Ta ce:

"Wato batu na gaskiya, fim yana burge ni kwarai da gaske, amma dalilin shiga ta sana’ar ita ce; wani fim aka yi sai wata ta musulunta.
"Daga nan ne na ce in dai har fim yana isar da sako, har ya zama silar gyaruwar al’umma, gaskiya zan zama daya daga cikin wadanda za su isar da wannan sako.
"Tun da da ma raina yana so matuka gaya sai kuma na samu dalilin shiga."
Yar Kannywood ta yi mamakin yadda fim ke da tasiri
Jarumar Kannywood ta faɗi dalilin shigarta harkar fim. Hoto: Kannywood Update.
Source: Facebook

Burin jaruma Sailuba a masana'antar Kannywood

Kara karanta wannan

Ummi Nuhu: Tsohuwar 'yar fim ta rusa kuka a idon duniya, ta fadi halin da ta shiga

Game da tsawon lokaci da ya dauka tana harkar fim, jarumar ta ce aƙalla ta kai shekaru takwas tana fafatawa.

Jarumar ta ce yanzu kawai tana fitowa a jaruma ce amma tana fatan zama bai ba da umarni a nan gaba.

"Ina ga kamar zan samu kamar shekaru takwas da fara harkar fim a masana'antar Kannuwood.
"Ina fitowa ne a matsayin jaruma kawai, amma kuma ina da niyyar zama mai bayar da umarni a nan gaba kadan in sha Allah."

- Nusaiba Muhammad Ibrahim

Dattijo ya fadi dalilin shiga fim a Kannywood

Mun ba ku labarin cewa fitaccen jarumi a Kannywood, Malam Inuwa Ilyasu, ya bayyana cewa ya shiga harkar fim ne domin fadakar da jama'a da kuma koyar da addinin Musulunci.

A cewar Malam Inuwa, bai zabi fitowa a matsayin malami a fina-finai ba, sa'a ce kawai ta sa yana samun waɗannan ɓangare wanda kuma yana jin dadin haka.

Ya ce masana'antar fim ta taka muhimmiyar rawa wajen wayar da kan matasa, musamman wurin koyar da ɗabi'a, tarbiyya da kuma al'adar Hausawa gaba daya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.