NNPCL Ya Shirya Hadaka da Rahama Sadau, Adam Zango da Jiga Jigan Kannywood

NNPCL Ya Shirya Hadaka da Rahama Sadau, Adam Zango da Jiga Jigan Kannywood

  • Kamfanin NNPC ya gana da shahararrun ‘yan Kannywood a Abuja domin karfafa hadin gwiwa kan samar da mafita ga matsalolin makamashi
  • Manyan Kannywood kamar Sani Danja, Rahma Sadau, Hadiza Gabon, Adam Zango da sauransu sun halarci taron don tattauna batun wayar da kan jama’a
  • Ra’ayoyin jama’a sun sha bamban, wasu na goyon bayan hadin gwiwar, yayin da wasu ke ganin injiniyoyi da masana ilimin makamashi ne suka fi dacewa da aikin

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Kamfanin man fetur na kasa, NNPCL ya gudanar da wani muhimmin taro a birnin Abuja tare da shahararrun jaruman masana’antar fina-finan Kannywood.

Taron yana da nufin karfafa hadin gwiwa domin wayar da kan ‘yan Najeriya game da batutuwan da suka shafi makamashi.

Kara karanta wannan

Dan ta'adda ya yi kokuwa da soja domin kwace bindiga a cikin daji

Kannywood
NNPCL zai yi hadaka da 'yan wasan Hausa. Hoto: NNPC Limited
Asali: Facebook

Legit ta tattaro bayani kan taron ne a wani sako da kamfanin NNPCL ya wallafa a shafinsa na Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A yayin taron, NNPCL ya gabatar da bayani kan muhimman ayyukansa a bangarori hakar danyen mai, sarrafa shi da sauransu.

Rahotanni sun tabbatar da cewa taron ya samu halartar manyan jaruman Kannywood kamar Sani Danja, Rahma Sadau, Hadiza Gabon, Adam Zango, Mansurah Isah, da Umar M. Sheriff.

Hakan yana nuna yadda masana’antar fina-finai ke da niyyar amfani da tasirinta wajen kawo sauyi ta hanyar hadin gwiwa.

Dalilin hadin gwiwar NNPCL da Kannywood

Kamfanin NNPCL ya bayyana cewa yana neman hanyoyin da za su taimaka wajen isar da sakonni masu muhimmanci ga ‘yan Najeriya game da amfani da makamashi.

Matakin kamfanin ya nuna cewa fina-finai da shahararrun jaruman Kannywood na da matukar tasiri wajen yada sakonni a cikin al’umma.

A yayin taron, an tattauna kan yadda NNPCL ke taka rawa wajen fadakar da mutane kan illolin satar danyen mai da fasa bututun mai.

Kara karanta wannan

Ana zargin akwai lauje cikin naɗi da aka kama jami'in NIS ɗauke da manyan makamai

Ana sa ran cewa jaruman za su yi amfani da hanyoyin zamani wajen ilimantar da jama’a kan yadda za su amfana da makamashi cikin tsari da inganci.

Abubuwan da jama'a suka fada kan hadakar

Bayan taron, mutane da dama sun bayyana ra’ayoyinsu kan hadin gwiwar da aka kulla tsakanin NNPC da Kannywood.

Aliyu Abdullahi ya bayyana cewa:

"A maimakon hada kai da injiniyoyi don su taimaka wajen bunkasa ilimin makamashi, NNPC ta zabi Kannywood. Wannan ba daidai ba ne."

Shi kuwa Abdulganiyyi Jimoh ya ce:

"Wannan cin fuska ne ga mu injiniyoyi. Mataki ne mai matukar ban takaici."

Sai dai Nura Bala ya bayyana cewa:

"Ana bukatar wayar da kan jama’a ta hanyar fina-finai, waka da wasan kwaikwayo don isar da sakonni ga jama’a."

Deen Yashai Dabai ya yi tsokaci da cewa:

"NNPC na kokarin yada wannan sakon ga jama’a da yawa, shi ya sa suka gayyato taurarin Kannywood ba injiniyoyi ko masu ilimin kimiyya ba."

Kara karanta wannan

Yan ta'adda sun firgita, an fara neman gwamnati ta karbi tuban jigo a sansanin Turji

Ana ganin matakin zai iya canza hanyoyin da ake amfani da su wajen yada ilimi kan harkar makamashi a Najeriya.

Kamfanin MRS ya rage farashin fetur

A wani rahoton, kun ji cewa kamfanin mai na MRS ya rage kudin litar man fetur a sassan Najeriya.

Rahoton Legit ya nuna cewa kamfanin ya fitar da sanarwar ne a ranar Litinin inda ya bayyana sabon farashin mai a Arewaci da Kudancin Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

iiq_pixel