Jarumar Kannywood Radeeya Jibril Ta Yi Aure, Ta Lissafa Mutane 7 da Suka Taimaka Mata

Jarumar Kannywood Radeeya Jibril Ta Yi Aure, Ta Lissafa Mutane 7 da Suka Taimaka Mata

  • Jaruma Radeeya Jibril ta yi aure tare da bayyana alfaharin kasancewarta 'yar Kannywood, inda ta gode wa Allah da masoyanta
  • Jarumar ta ce aure ya kawo karshen zamanta a Kannywood, tana rokon yafiya daga kowa da addu’ar Allah ya cika musu burinsu
  • Legit Hausa ta ji ta bakin jarumi, TY Shaba kan yadda ya fara aiki da Radeeya da kuma abin da zai faru da shirin 'Lulu da Andalu'

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kano - Daya daga cikin fitattun jarumai mata na masana'antar Kannywood, Radeeya Jibril ta yi aure, kamar yadda ta shaidawa masoyanta a ranar Asabar.

Jaruma Radeeya Jibril ta fito a manyan finafinai, amma dai ta fi kaurin suna a fim din 'Lulu da Andalu' wanda mawaki TY Shaba ya shirya.

Kara karanta wannan

Sojojin saman Najeriya sun saki bama bamai a Neja, an halaka 'yan ta'adda da dama

Jarumar Kannywood, Radeeya Jibrin ta yi magana yayin da ta yi Aure
Jarumar Kannywood, Radeeya Jibrin ta yi aure, ta aika sako ga wasu 'yan masana'antar. Hoto: radeeya_jibril
Asali: Instagram

Jarumar Kannywood Radeeya ta yi aure

A wata sanarwa dauke da hotunanta da ta wallafa a shafinta na Instagram, 'yar wasa Radeeya Jibrin ta ce ta yi alfahari da kasancewarta 'yar fim din Hausa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jaruma Radeeya ta ce

"Zanyi anfani da wannan damar tawa ta yau domin sanar da ku cewa na yi aure.
"Nagode wa Allah da ya nunamin wannan rana ranar da zan bar Kannywood lafiya kamar yadda na shigo lafiya."

'Yar wasar ta yiwa TY Shaban godiya marar adadi da ya kasance bango a gareta tsawon zamanta a Kannywood, sannan ta lissafa wasu mutane da suka taimaka mata.

Radeeya ta aika sako mai ratsa zuciya

Kadan daga sakon Radeeya na ce:

"Sunana RADEEYA JIBRIL kamar yanda kuka sani, sannan kuma ni matashiyar jaramur kannywood ce kamar yadda kuka sani, to alhamdulillah ina alfahari da kasance wa ta yar fim.
Sannan kuma zan yi anfani da wannan damar tawa ta yau domin sanar daku cewa (NAYI AURE).

Kara karanta wannan

Magana kan Bello Turji ya jawo matsala, an zargi yan APC da kai hari kan jigon jam'iyyar

Nagode wa Allah da ya nunamin wannan rana ranar da zan bar Kannywood lafiya kamar yinda na shigo lafiya. Alhamdulillah Alhamdulillah Alhamdulillah."

Radeeya ta yi godiya ga mutane 7

Jarumar ta roki duk wanda na yi wa ba daidai ba ya yafe mata yayin da ta ce 'Uncle' Ty Shaba ya zame mata jigo, bango kuma gwarzo a Kannywood.

Ta yi godiya ga Ty Shaba wanda ya taimake ta sosai tana mai addu'ar Allah ya saka masa da alheri, ya kara daukaka darajarsa duniya da lahira.

Hakanan, ta gode wa Abubakar Bashir Maishadda da Umar UK saboda gudunmawa da shawarwari masu amfani da suka ba ta.

A karshe, ta gode wa Abdul Amart Mai Kwashewa, Ahmad Bifa da Mujahid M. Soja tana mai yi masu addu'ar ya ci gaba a rayuwarsu.

TY Shaba ya yi tsokaci kan Radeeya

Legit Hausa ta tuntubi TY Shaba, jarumi, mawaki kuma mai shirya finafinai wanda Radeeya ta kira da 'bango' a wajenta domin jin ta bakinsa kan tafiyar jarumar.

Kara karanta wannan

Bidiyon da ake zargin ya jawo aka dakatar da jaruma Samha M Inuwa daga Kannywood

TY Shaba ya shaidawa wakilinmu, Sani Hamza Funtua cewa sai da ya tabbatar Radeeya ta kasance mai kamun kai, mai ladabi da biyayya sannan ya fara sanya ta a fim.

"Lokacin da Radeeya ta zo Kannywood ta ce tana so ta yi aiki da ni, na ce mata to sai ta mutunta kanta, ta zama mai ladabi da biyayya, mai hakuri da kuma kamun kai.
"Sai da na ba ta lokaci, na tabbatar ta ginu a kan wannan abu sannan na jawota muka ci gaba da harkar arziki. Kuma duk wata dama da take bukata na zama jaruma na ba ta."

Tasirin Radeeya a shirin 'Lulu da Andalu'

Sani Hamza ya tambayi TY Shaba ko akwai wani tasiri da Radeeya ta yi a shirinsa mai dogon zango na 'Lulu da Andalu', sai cewa ya yi:

"A matsayinta na sabuwar jaruma, kusan shi ne fim din farko da ya fara haskakata. Ya kasance fim mai tsauri saboda akwai daji da sauransu, amma ta jajirce ba tare da gajiya ba.

Kara karanta wannan

Rahama Sadau ta faɗi sunan wanda ya kama hannunta, ya shigo da ita Kannywood

"Kuma ta taimaka wajen tattaro jarumai da kara masu karfin guiwar har abin na ba ni mamaki yadda take taimako na a matsayin mai shirya fim din Lulu da Andalu."

Me zai faru yanzu da Radeeya ta yi aure?

Da aka tambayi TY Shaba a kan abin da zai faru da shirin 'Lulu da Andalu' da sauran shirye shiryen da jarumar ke ciki tun da ta yi aure, sai ya ce:

"Ni fatana a kullum, duk wanda na jawo shi sanadiyya ya zama wani abu a masana'antar nan shi ne ya samu ingantacciyar rayuwa, kullum ina bukatar mutum ya ci gaba.
"Shi da ma fim din 'Lulu da Andalu' mai dogon zango ne, wanda ko wane irin al'amari zai iya shiga ya fita, idan an sauya da wata mai kallo zai fahimta."

TY Shaba ya ce akwai yadda masu shirya fim da daraktoci suke yi na yadda za a cire jarumi ko jaruma daga fim a maye ta da wani ko wata ba tare da ya shafi fim din ba.

Kara karanta wannan

Tinubu: Kalaman Peter Obi sun yi wa APC zafi, ta zarge shi da son tunzura jama'a

TY Shaba ya yiwa Radeeya nasiha

A karshe TY Shaba ya ce ya yiwa Radeeya nasiha yayin da za ta je gidan mijinta.

"Ina godiya ga Allah da ya kawo wannan rana da Radeeya Jibril ta yi aure, kuma na yi mata nasiha a matsayin 'uncle' kuma 'uba' a wajenta, aure dai sai ta yi hakuri ta yiwa mijinta biyayya."

Jarumin ya kuma lissafa wasu daga cikin 'yan Kannywood da Radeeya ba ta kama sunansa a sanarwarta ba, yana mai ba kowa hakuri musamman Kamilu Dan Hausa.

Fitaccen mawakin Kannywood ya yi aure

A wani labarin, mun ruwaito cewa Auta Waziri, fitaccen mawakin Kannywood ya yi aure da sahibarsa Halima Mustapha (Marmah) a jihar Kaduna.

An daura auren Auta Waziri, wanda asalin sunansa Abdullahi Abubakar a ranar 6 ga watan Disambar 2024, wanda aka daura a masallacin Jumma’a da ke SMC Unguwan Dosa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.