Fitattun jarumai mata guda 9 da suka shahara sanadiyyar Adam Zango, jarumin yayi alkawarin karrama daya daga cikinsu

Fitattun jarumai mata guda 9 da suka shahara sanadiyyar Adam Zango, jarumin yayi alkawarin karrama daya daga cikinsu

- Fitaccen jarumi Adam A Zango ya tuna da wasu fitattun jarumai mata guda tara

- Jarumin ya tuna da su ne saboda ta sanadiyyar sa suka fito har duniya ta san da su

- Hakan yasa ya sanya wata gasa a shafinsa na Instagram ya bayyana cewa duk wacce ta cinye a cikinsu zai ba ta kyauta

A yau jarumi Adam A Zango ya tuna baya inda ya wallafa hotunan jarumai mata guda tara wadanda dukkansu ya bayar da muhimmiyar gudummawa wajen shahara da karbuwar su a duniya wasu daga cikin su sunyi aure wasu kuma suna nan ana cigaba da damawa da su wasu kuma ba a fiya jin duriyar su ba.

Jaruman dai sun hada da Fati Shu'uma, Fati Ladan, Zainab Indomie, Zainab Raga, Maryam Malika, Maryam Babban Yaro, Maryam AB Yola, Fati S.U, Aisha Hubbi, inda Fati Ladan, Maryam Malika da Zainab Raga sun riga sunyi aure, tsohuwar matar sa Maryam Ab Yola kuwa tayi auren da jarumin ne kuma ta fito ta dawo harkar ta.

Adam A Zango ya wallafa hotunan wadannan jarumai da yabawa gudummawa a cikin sana'ar su har sukayi shuhura gami da rubuta: "Kowa ya ga zabuwa...Ku nuna mini wacce kuka fi so a cikin jarumai na, jaruman masana'anta ta na da dana yanzu."

KU KARANTA: Wata sabuwa: Bana madigo so suke kawai su bata mini suna - Jaruma Bilkisu Salisu

"Duk wacce tafi masoya a cikinsu zata sami kyauta sabuwar waya mai kirar Techno Phantom 9 da da katin waya na naira dubu ashirin (N20,000) da kwalin taliyar Indomie guda 20."

Yanzu dai haka ana can ana fafatawa a shafin jarumin inda za a fitar da guda daya da zata karbi wadannan kyaututtuka da ya shirya badawa inda kowa ke fadin jarumar da ta fi buge shi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel