Mutuwa Ta Girgiza Ali Nuhu, An Ji Mahaifiyar Marigayi Ahmad S Nuhu Ta Rasu

Mutuwa Ta Girgiza Ali Nuhu, An Ji Mahaifiyar Marigayi Ahmad S Nuhu Ta Rasu

  • Shugaban hukumar fina finan Najeriya, jarumi Ali Nuhu ya sanar da rasuwar mahaifiyar marigayi Ahmad S. Nuhu a garin Jos
  • Ali Nuhu ya sanar da cewa mahaifiyar tsohon dan wasan Kannywood din ta rasu ne a ranar 1 ga watan Janairun shekarar 2025
  • Jarumai, ma'aikata da masu kallon finafinan Hausa sun aika sakon ta'aziyyar rasuwar mahaifiyar marigayi Ahmad S. Nuhu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Filato - Mutuwa ta ratsa masana'antar shirya fina finan Hausa watau Kannywood a sabuwar shekara yayin da mahaifiyar marigayi Ahmad S. Nuhu ta rasu.

Kafin rasuwarsa a ranar daya ga watan Janairun shekarar 2007, marigayi Ahmad S Nuhu ya kasance tauraron Kannywood da ke tashe a lokacin.

Ali Nuhu ya sanar da rassuwar mahaifiyar marigayi Ahmad S Nuhu.
Allah ya yiwa mahaifiyar marigayi Ahmad S Nuhu rasuwa a Jos. Hoto: realalinuhu
Asali: Instagram

Mahaifiyar marigayi Ahmad S Nuhu ta rasu

Jarumi Ali Nuhu, wanda dan uwa ne ga Ahmad S. Nuhu ya sanar da rasuwar mahafiyar marigayin a shafinsa na Instagram a ranar Laraba.

Kara karanta wannan

"Ba mu son wa'azinku": Sanusi II ya fadawa kasashen Yamma abin da Arewa ke bukata

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ali Nuhu ya sanar da cewa mahaifiyar marigayi Ahmad S Nuhu ta rasu ne a ranar daya ga watan Janairun shekarar 2025 da muka shigo.

Shugaban hukumar fina finan Najeriya ya ce za a yi jana'izar mahaifiyar marigayin da misalin karfe 9:00 na safiyar Laraba a unguwar Gadar Sogai da ke Nasarawa, Jos.

'Yan Kannywood sun mika sakon ta'aziyya

Jarumai, 'yan Kannywood da ma masu kallon finafinan Hausa, sun yi wa Ali Nuhu ta'aziyyar rashin mahaifiyar dan uwansa.

official_hairat11:

"Allah ya jikanta da rahama."

ayatullahi_tage:

"Allah ta gafarta musu dukansu, Allah ya sa Aljannah ta zama madadi garesu."

haleemaatete:

"Allahu akbar ,Allah ya jikansu ya yi musu rahama."

falalu_a_dorayi:

"Allahu Akbar. Allah ya jikansu yai musu rahma. Ya bawa iyalai hakuri."

ayshatulhumairah:

"Allah ya gafarta mata, Allah ya sa mutuwa hutu ce da rahma a gare su baki daya da su da sauran iyaye da yan uwa da suka riga mu, Ubangiji ya kyautata karshen mu."

Kara karanta wannan

Kwana ya kare: Mahaifiyar Sarki a Yobe ta riga mu gidan gaskiya

teerhmah_zahrah:

"Allah ya gafarta masu baki daya da dukan muslmai."

donbersh:

"InnalilLahi. Allah ya gafarta musu ya hada fuskokin su a gidan Aljannah."

officialabdulazizdansmall:

"Allahu akbar. Allah ubangiji ya jikanta ya sa mutuwa hutuce a gareta."

"Na shiga damuwa bayan rasuwar Ahmad"- Hafsat

A wani labarin mun ruwaito cewa matar marigayi Ahmad S. Nuhu, kuma tsohuwar jarumar Kannywood, Hafsat Shehu, ta ce ta shiga mawuyacin hali bayan rasuwar mijinta.

Hafsat Shehu ta shaida cewa farin cikinta gaba daya ya dauke tun da Ahmad ya rasu, inda har ta take mamaki idan ta ga wasu mutane suna dariya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.