Allahu akbar: Ahmad S. Nuhu ya yi shekaru 13 da rasuwa, Ali Nuhu yayi ta'aziyya

Allahu akbar: Ahmad S. Nuhu ya yi shekaru 13 da rasuwa, Ali Nuhu yayi ta'aziyya

A ranar daya ga watan Janairu ne na shekarar 2007 Allah yayi wa jarumi Ahmad S. Nuhu Rasuwa. A halin yanzu jarumin yayi shekaru 13 da komawa ga Ubangiji ta sanadiyyar hatsarin mota.

Wannan lamarin kuwa yayi matukar girgiza zukatan masoyansa, 'yan uwa, abokan aiki da kuma abokan arziki.

Masana'antar Kannywood da kuma ma'abota kallon fina-finai kuwa sun dade suna jimamin mutuwar matashin jarumin.

A ranar daya ga watan Janairu na wannan shekarar ne jarumi Ali Nuhu ya garazaya shafinsa na Instagram, tare da wallafa hoton marigayin inda yake kara ta'aziyya a cikarsa shekaru 13 da barin duniya.

Babu jimawa kuwa abokan sana'arsa suka dinga tururuwa wajen addu'o'i tare da rokar masa rahama wajen Ubangiji.

DUBA WANNAN: Ma'aikata sun harbe wasu Zakuna uku da suka yi kalaci da gawar wani mutum

Jarumi Ahmad s. Nuhu kuwa ya rasu ya bar matarsa daya wacce ita ma tsohuwar jaruma ce a masana'antar. Bayan gama takabar Hafsat Shehu, ta kara aure a garin Abuja amma sai auren bai yi nisan kwana ba.

A wani labari da Tashar Tsakar Gida ta YouTube ta wallafa, ta bayyana cewa a wata ranar Juma'a ne aka daura auren jaruma Hafsat Shehu wacce ta kasance tsohuwar matar ga marigayi jarumi Ahmad S Nuhu, haka kuma ta kasance tsohuwar jaruma a masana'antar Kannywood.

Muna fatan Ubangiji yaji kan jarumi Ahmad S. Nuhu, ya gafarta masa. Mu kuwa ya kyautata tamu idan tazo.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng