Manyan Mata da Wasu Finafinan Kannywood 4 da Suka Yi Tashe a Shekarar 2024
- An samu canji sosai a masana'antar Kannywood; daga CD zuwa sinima, zuwa YouTube da kuma neman shiga manhajojin duniya
- A shekarar 2024, masu shirya finafinai sun yi kokari wajen samar da finafinan da suka kayatar da masu kallo fiye da a baya
- Legit Hausa ta zakulo wasu finafinan Kannywood biyar masu dogon zango da suka yi tashe a 2024 ciki har da Labarina da Manyan Mata
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Kano - An samu ci gaba sosai a masa'antar Kannywood, inda yanzu furodusoshi suka fara mayar da hankali kan tsara finafinan da za su dace da duniya
A shekarar 2024, masu shirya finafinan Kannywood sun yi rawar gani wajen samar da finafinai masu jan hankali, wadanda akasarinsu masu dogon zango ne.
Komawa ɗora finafinai a YouTube ya taimaka wajen dawo da martabar Kannywood, bayan masana’antar ta fuskanci durƙushewa sakamakon daina kallo a CD.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Finafinan zango na lokaci a Kannywood
Legit Hausa ta zakulo wasu manyan finafinai da suka yi tashe a 2024, waɗanda suka bayyana irin sauyin da ke aka samu a masana’antar Kannywood.
Yawancin finafinan shekarar da ta gabata suna da dogon zango, alamar yadda masana’antar ke kokarin yin gogayya da sauran kasashen duniya.
A baya, ana ganin finafinan zango na da cin lokaci amma yanzu manyan furodusoshi sun shiga harkar ka'in da na'in, inda suke samar da finafinai masu inganci.
Finafinan Kannywood 5 da suka shahara a 2024
Daga cikin finafinan 2024 da muka zaƙulo, akwai waɗanda ba a shekarar ne aka fara haska su ba, amma duk da haka sun yi tashen da ya ja hankalin mutane sosai.
Ga yadda muka yi nazarin fina-finan Kannywood na shekarar 2024:
1. Labarina
Labarina fim ne mai dogon zango daga fitaccen darakta, Aminu Saira, wanda ya shahara sosai a masana’antar Kannywood, har ba ya buƙatar wata gabatarwa.
An gina Fim ɗin ne a kan tsarin labari mai bangarori daban daban, shigen littafin 'Dare Dubu da Ɗaya', wanda ya sa fim ɗin ya gaza salamcewa.
An fara haska shirin Labarina a 2020 da labarin Sumayya (Nafisa Abdullahi), kafin daga bisani Fati Washa ta koma taka rawar Sumayya.
Bayan ƙarshen zango na bakwai, an ɗauki hutu, sannan aka dawo da sabon labari daga zango na takwas.
Zango na takwas ya fara da labarin Alhaji Mainasara (Sadiq Sani Sadiq). Labarin ya nuna yadda Mainasara ya yi basaja da talaka don nemo soyayya ta gaskiya, har ya haɗu da Jamila (Amina Uba Hassan).
Amma lokacin da direban Mainasara ya nunawa Jamila kudi, sai ta bijirewa soyayyar Mainasara, lamarin da ya sa Maryam (Fatima Hussaini) ta karbi soyayyar Mainasara har ta aure shi.
Bayan auren ne aka gano ashe Mainasara hamshakin mai kudi ne wanda ya rasa iyalansa a hatsarin mota, lamarin da ya jawo wasu suka yi kokarin kashe shi.
Ana tsaka da shan soyayya ne aka gano Mainasara da Maryam su na dauke da jinin AS, wanda ya sa tilas ya kara aure, inda Maryam ta nemar masa auren Dokta Asiya (Diamond Zahra).
Fim ɗin ya jawo hankalin masu kallo tare da fitar da sababbin jarumai mata kamar Firdausi Yahaya, Fatima Hussaini da Amina Uba Hassan.
2. Manyan Mata
Fim ɗin Manyan Mata ya shiga sahun fina finan da hankalin masu kallo sosai a shekarar da ta gabata duk da cewa ba a 2024 aka fara shi ba.
Fim ɗin yana dauke da jarumai da dama, wanda ba kasafai yanzu ake ganin irin hakan ba, duk da cewa a shekarun baya, ana yawan hada jarumai masu yawa a fim daya.
Furodusa Abdul Amart Maikwashewa ne ya shirya wannan fim. A tashin farko, Sadiq N. Mafia ne ya ba da umarni amma daga baya Ali Gumzak ya ci gaba da bayar da umarnin fim din.
A cikin fim ɗin, an nuna yadda wasu mata ke fuskantar kalubale a gidajen mazajensu da kuma yadda wasu ke amfani da 'yan gudun hijira wajen cimma muradunsu.
A wani ɓangare na fim ɗin, akwai Laila (Hadiza Gabon) da Nadia (Aisha Tsamiya), wadda aka maye gurbinta da Rabiatu Ƙafur, wadanda kawaye ne da ke fafutukar neman kare 'yancin mata.
Sai dai sun samu sabani a kokarin tafiyar da ƙungiyarsu ta 'Manyan Mata' da kuma tayin da minista ta yiwa Laila na fitowa takara.
Fim ɗin yana samun kimanin mutane miliyan daya da doriya a kowane mako, kasancewar ya na taba abubuwan da suke faruwa a zahiri, musamman a yankunan Arewacin Najeriya.
A cikin fim ɗin, an haɗa manyan jarumai na masana'antar Kannywood, har da waɗanda aka jima ba a ji duriyarsu a harkar fim ba.
Furodusa Abdul Amart ya ce a yanzu haka, suna kokarin kammala ɗaukar zango na huɗu na fim ɗin, wanda ke dauke da sababbin jarumai da kuma sabon salo.
3. Gidan Sarauta
Bayan nasarar Dan Jarida, shirin Gidan Sarauta na daya daga cikin finafinai masu dogon zango da furodusa Abubakar Bashir Maishadda ya shirya, wanda ya samu karbuwa.
An fara haska wannan fim ɗin a ranar 5 ga Nuwamban 2023, kuma yanzu haka ana kan haska zango na uku na shirin.
Jarumi Umar M. Shareef da jaruma Mommee Gombe suna cikin manyan jaruman fim ɗin, tare da taimakon Garzali Miko da Aisha Najamu.
Har ila yau, film din na dauke da jarumai irinsu Ali Nuhu, Hadizan Saima, Yakubu Mohammad, Rabiu Rikadawa, da Abale.
Fim ɗin Gidan Sarauta ya mayar da hankali ne kan Umar M. Shareef, wanda a cikin labarin ya taka rawar wani yarima mai jiran gado.
Yarima ya shiga soyayya da ƴar talaka, Bintu (Momme Gombe), duk da cewa bai bayyana soyayyar ba, har sai bayan da ƙaninsa ya riga shi aurenta.
Amma daga baya, an gano cewa akwai wani sirri a tsakanin Yarima da Bintu wanda ya haifar da rikici a gidan sarautar, da ya sa ƙaninsa ya sake ta, shi kuma Yarima ya aurate.
Wannan lamari ya jawo masa fushi daga mai martaba (Yakubu Muhammad), inda aka ba shi zaɓin ko ya rabu da Bintu ko ya rasa sarauta. A ƙarshe, ya zaɓi matarsa Bintu kuma ya bar matsayin Yarima.
A cikin fim ɗin, Garzali Miko ma ya hango wata 'yar yarinya Tafida wato Badariyya (Firdausi Yahaya), wanda ya faɗa cikin ƙaunar ta, amma yana tsoron shiga irin matsalolin da yayansa ya fuskanta.
Ali Nuhu ne ya ba da umarnin wannan kayataccen fim kuma jarumai sun jajirce wajen tabbatar da cewa fim ɗin ya kayatar da masu kallo.
4. Garwashi
Garwashi wani sabon fim ne da aka fara haska shi a ranar 12 ga Agustan 2024 a dandamalin YouTube na UK Entertainment, wanda ya ja hankalin masu kallo.
Fim ɗin yana haska irin ƙalubalen da matan da mazajansu suka rasu ke fuskanta daga wurin ƴan uwa da sauran al'umma musamman dangin mazajensu.
Jarumar da ke jagorantar fim ɗin, Asma'u (Firdausi Yahaya), ta na fuskantar azabtarwa daga dangin mijinta, ƴan uwanta da kuma wuraren aikinta.
Fitacciyar marubuciyar litattafai da finafinai, Fauziyya D. Suleiman ce ta rubuta tare da shirya wannan fim wanda salonsa ya sosa inda ke yiwa al'umma kaikayi.
Darakta Yaseen Auwal ne ya jagoranci aikin, wanda ya sanya Firdausi Yahaya ta taka rawar da ya dace duk da kasancewarta bakuwa a cikin harkar fim.
Fim ɗin ya dauki hankalin masu kallo cikin gajeren lokaci, musamman saboda yadda jarumar take shan bakar wahala duk da cewa Yakubu Mohammed na son taimaka mata.
5. Allura cikin ruwa
Fim ɗin Allura Cikin Ruwa yana dauke da labarin Na'ima (Rukky Alim), wata marainiya da aka tsinta bayan kanin mahafinta Ciroki ya harbe mahaifiyarta.
Na'ima ta girma a cikin mawuyacin hali, duk da cewa iyalan Tijjani Faraga sun riketa tamkar 'yarsu, amma kullum tana son gano gaskiya game da danginta.
A cikin fim ɗin, maza daban-daban sun nuna sha'awarsu ga auren Na'ima. Daga cikinsu akwai Maina (Yakubu Mohammad), wanda ya kasance ƙanin Tijjani.
Sannan akwai Alhaji Hadi (Sani Danja), Dakta Hashim (Adam A. Zango) da Sadiq (Isa Adamu Ferozhkan), wadanda suka daɗe suna soyayya da Na'ima kuma suna neman auren ta.
Daga baya, an gano cewa Na'ima tana da tarin dukiyar da mahaifinta ya mutu ya bari, sannan kuma mahaifiyarta da dan uwanta Daddy Hikima sun bayyana.
Gano asalin Na'ima da dukiyar da ta mallaka ya canza yanayin labarin, inda ta sake shiga wata wahalar, musamman bayan auren Alhaji Hadi da kuma rayuwarta da 'Fatalwar masoyi."
Kamfanin 2Effects ne suka ɗauki nauyin fim ɗin, wanda Yakubu Mohammad ya ba da umarni. Yanzu haka ana cikin zango na biyu na fim ɗin, wanda ke ci gaba da jan hankalin masu kallo.
Mawakan da suka yi tashe a 2024
A wani labarin, mun kawo maku jadawalin mawakan Kannywood da suka yi shuhura a cikin shekakarar 2024 da ta gabata da kuma manyan wakokin da suka fitar.
Daga cikin mawakan akwai Sadiq Saleh, wanda tauraruwarsa ta fi ta kowa haske a 2024, bayan ya fitar da wakokin da suka yi tashe irinsu Mai Kishina, Ko Wuya Ko Dadi, da sauransu.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng