Gidajen Sarauta 10 Da Suka Fi Yawan Dukiya A Duniya, Adadin Kudin Da Suka Mallaka, Da Sanadin Kudinsu
- Gidan sarautar Birtaniya tana cikin wacce ta fi shahara a gidajen sarauta na duniya amma ba ita ce ta fi arziki ba
- Jimillan dukkan dukiyan gidajen sarauta na duniya da aka kiyasta shi ya kai $2.6 tiriliyan, mafi yawancinsu sun mallaki kamfanoni
- A cewar rahotanni, mafi yawancin yan gidajen sarautan daga Gabas ta Tsakiya suka fito kuma sun samu arzikinsu ne galibi daga danyen man fetur
Rasuwar Sarauniya Elizabeth ta II na nadin Sarki Charles III ya sa mutane sun samu karin bayanai dangane da gidan sarautar Birtaniya da wasu gidajen sarautan a fadin duniya.
A cewar rahotanni, gidajen sarauta mafi arziki a duniya suna mallaki tarin dukiya a kalla $2.4 tiriliyan tsakaninsu a shekarar 2021.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Rahoton fallasa na Pandora Papers ya kara saka ayoyin tambaya kan yadda gidajen sarautan ke samun kudinsu da kashewa.
10. Gidan Sarauta na Liechtenstein: $4.4 biliyan
Gidan sarauta na Liechtenstein a kasar Austria ya ke kuma suna da dukiya da ta kai $4.4 biliyan. Mafi yawancin dukiyar na iyalan na hannun Yarima Hans-Adam II, basarake da ke mulki a yanzu.
Tun a 1906 aka kafa gidan sarautan. Ba su biyan haraji kuma sun samu arzikinsu ne daga LTG Group, wani banki mai zaman kansa da gidan sarautan suka mallaka.
Baya ga bankin, gidauniyar Yariman Liechtenstein na da hannun jari a gidaje, kamfanoni da wasu kasuwanci masu riba.
9. Gidan Sarautan Morocco: $8.2 Biliyan
Iyalan Alaouite ne gidan sarautan da ke mulki a Morocco a yanzu, an kafa ta ne a 1631 amma ta samo asali a karni ta 13.
Sarki Mohammed VI ne ke jagorantar gidan, ya zama sarki a 1999.
2023: Ban Taba Satar Ko Sisi Ba, Daidai Da Naira 10, In Ji Dan Takarar Shugaban Kasa Daga Arewacin Najeriya
Wasu kididigan sun ce arzikin gidan sarautan na Morocco ya kai $8.2 biliyan, sune gidan sarauta na 9 cikin jerin mafi arziki a duniya.
Suna da kadarori da biliyoyin dala, kuma gwamnati na biyan su albashi saboda ayyukan da suke yi.
8. Gidan Sarauta na Dubai: $18 Biliyan
Gidan sarautan Dubai sun fito ne daga tsatson Gidan Maktoum, da ya samo asali daga 1933.
Jimillan dukiyarsu ta kai $18 biliyan.
Wanda ya fi arziki a gidan sarautan shine Sheikh Mohammed bin Rashin Al Maktoum. Tun 2006 ya ke mulki kuma shine mataimakin shugaban kasar UAE kuma farai minista.
Shine ke da Dubai Holdings kuma an san shi da kyauta.
7. Gidan Sarauta na Brunei: A kalla $28 Biliyan
Gidan Bolkiah ne ta kafa gidan sarauta na Brunei a 1363, kuma sune ke mulkar kasar tun lokacin.
Sultan Hassanal Bolkiah ne ke jagoranci, ya yi mulki tsawon shekaru 54 kawo yanzu.
Sun samu arzikinsu ne saboda danyen mai da Brunei ke da shi. Forbes ta rahoto cewa Sultan na da $20 biliyan a 2011, amma wasu sun kiyasta dukiyarsa ta kusa kai $28 biliyan.
6. Gidan Sarauta na Thailand: Kusan $60 Biliyan
Gidan sarauta na Chakri ne suke mulkin Thailand tun 1782 kuma an girmama su a kasar.
Sarki na yanzu, Maha Vajiralongkorn, ya dare gadon sarauta ne a 2016 bayan rasuwar mahaifinsa, Sarki Bhumibol Adulyadej.
Ba za a iya bayyana adadin dukiyar da gidan sarautan da mallaka ba a fili saboda an kare ta da wani doka mai suna lese-ma-jeste, ma'ana, yi wa mai martaba laifi, a karkshin dokar an sha daure mutane da dama har da laifuka irin na wallafa hoton karen sarki a soshiyal midiya.
An yi hasashen arzikinsu ya kai $30 biliyan zuwa $60 biliyan, wacce aka mika wa Sarkin a 2018 bayan kamfanin Crown Property ta kula da kudin na tsawon shekaru 80.
5. Gidan Sarauta na Birtaniya: $88 Biliyan
A Oktoban 2021, Kamfanin da ke kula da kadarorin gidan sarautan Birtaniya na cikin wadanda aka ambata a Pandora Papers, wacce ya nuna kamfanin ta siya wani gida na $91.2 miliyan daga shugaban Azerbaijani IIham Aliyev, da ake hasashen cewa ya kai $545.
4. Gidan arauta na Abu Dhabi: $150 Biliyan
Tsatson gidan sarautan Al Maktoum ne suka kafa gidan sarauta na Nahyan a Abu Dhabi kuma suke mulkar kasar tun 1973.
Sun samu arzikinsu, da aka kiyasta ya kai $150 biliyan, tun a shekarun 1970s daga man fetur na kasar.
Shugaban gidan, Sheikh Khalifa bin Zayed Al Nahyan, shine sarkin Abu Dhabi kuma shugaban UAE tun 2004. Shine shugaban Abu Dhabi Investment, wacce ke kula da kadara da aka kiyasta ta kai $696.6, ciki har da otel din Burj Khalifa, gini mafi tsawo a duniya.
3. Gidan Sarauta na Qatar: $335 biliyan
Gidan Thani ne ke mulkin kasar tun tsakiyar karni na 19, shugaba na yanzu shine Sheikh Tamin bin Hamad Al Thani, da aka nada a 2013.
Gidan Al Thani sun fara rikici da makwabtansu tun 2017 kan zargin cewa sun biya kungiyar ta'addanci ta Al-Qaeda fansar $1 biliyan don sakin iyalansu 28 da aka kama a Iraqi lokacin da suka tafi farauta a 2015.
2. Gidan Sarauta na Kuwait: $360 Biliyan
Gidan Al Sabah ne ke mulki a Kuwait. Sun fara mulki tun 1752, sarki na yanzu shine Sheikh Sabah IV Ahmad Al-Jaber Al Sabah.
Mujallar Time ta kiyasta dukiyarsu ya kai $90 biliyan.
Mafi yawancin arzikinsu na hannun jarin kamfanonin Amurka.
1. Gidan Sarauta na Saudiyya: $1.4 Tiriliyan
Gidan Sarauta mafi arziki a duniya ita ce gidan Sarauta ta Saud, wacce aka kiyasta dukiyarta ta kai $1.4 tiriliyan.
Gidan Saud ne suka rika mulkar kasar tun samun sunanta a 1744.
Sarki mai ci yanzu, Salman ya hau kan karagar mulki ne a 2015, mafi yawancin arzikin na hannun sarkin da danginsa. Ana kyautata zaton sarkin ya fi kowa kudi a cikinsu.
Jerin Kananan Yara 10 Mafi Arziki a Duniya, Shekarunsu, Dukiyar da Suka Mallaka da Iyayensu
Ba manya bane kadai suke tara arziki kuma basu kadai bane darajar dukiyoyinsu ke kaiwa biliyoyin kudi.
Wasu yaran ma suna rike da nasu arzikin kuma darajar dukiyoyinsu ya kai matakin biliyoyi kama daga kadarori zuwa tsabar kudi.
Yayin da wasu suka samu kudinsu ta hanyar gada daga iyayensu masu arziki, wasu sun samu arzikinsu ne da guminsu.
Asali: Legit.ng