Bayan Dogon Jira, An Sanya Ranar Fara Haska Fim din 'Gidan Badamasi' Zango na 6

Bayan Dogon Jira, An Sanya Ranar Fara Haska Fim din 'Gidan Badamasi' Zango na 6

  • Kamfanin Dorayi Films ya sanar da dawowar shirin Gidan Badamasi zango na shida bayan gama zango na biyar a karshen 2022
  • Masu kallon wannan shirin sun kasance cikin tsumayin ganin zango na shida tun a 2023, amma ba su dace ba sai a shekarar nan
  • Falalu Dorayi ya bayyana cewa zango na shida zai kawo sababbin salo na barkwanci, yayin da ya saki wasu jerin tallace-tallace

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kano - A Disambar 2022, kamfanin Dorayi Films ya sanar da fitar shirin Gidan Badamasi zango na biyar, kashi na 13, wanda ya zama kashin karshe a zangon.

Tun da shekarar 2023 ta shiga, masu kallo ke ta tsumayin ganin zango na shida na shirin, amma babu labari har sai a watan Disambar 2024 da muke ciki.

Kara karanta wannan

An shiga tashin hankali a Kaduna yayin da wata mata ta kashe ƴarta da maganin ɓera

Falalu A Dorayi ya yi magana yayin da ake shirin dawo da shirin Gidan Badamasi.
Za a dawo haska shirin Gidan Badamasi zango na 6 daga 19 ga Disambar 2024. hoto: falalu_a_dorayi
Source: Instagram

Gidan talabijin din Arewa24 ya yi sanarwa a shafinsa na Facebook, cewa zango na shida na shirin Gidan Badamasi zai dawo a tsakiyar Disamba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gidan Badamasi zango na 6 na nan tafe

A cewar sanarwar:

"Albishirin ku. Shirin Gidan Badamasi Zango na shida yana nan tafe a ranar 19 ga watan Disamba da misalin karfe 6:00 na yamma."

Sai dai kuma, gidan talabijin din ya nuna cewa shirin zai rika zuwa ne a kan manhajarsa ta Arewaondemand, ba tare da fadin ko za a rika haskawa a talabijin ba.

A mafi yawan lokuta, Arewa24 ba ta haska fina finan da take dorasu kacokan a kan manhajarta, misali shi ne shirin 'Wata Rana a Kano' na Abubakar Bashir Maishadda.

Kadan daga shirin Gidan Badamasi zango na 6

Mai shirya shirin Gidan Badamasi, Falau A. Dorayi ya wallafa wasu gajerun tallace tallace a shafinsa na Instagram da ta yi tsokaci kan shirin zango na shida.

Kara karanta wannan

'Yana da kwarin guiwa a 2027'; an fadi shirin da Tinubu ya yi game da zabe

A talla ta farko, an ga Tijjani Asase (Adamahama) da jaruma Hadiza Kabara (Hauwa) a cikin kayan gidan yarin, yayin da Falau ya wallafa cewa:

"Adahama da Hauwa an yi abin kunya, an tafi gidan yari."

A wata tallar kuma, an ga Yaya Dan Kwambo a cikin mota yana yiwa su Bazuka tsiya tare da barazanar daure su, yayin da Falalu ya yi bayani cewa:

"Wannan gudu ne tsakanin kare da zomo, wane ya saci kudi, wane na neman ya za ayi ya karbi kudinsa."

Jarumi kuma mai ba da umarni, Falalu A Dorayi ya nuni da cewa Gidan Badamasi zango na shida zai zo da abubuwan salo na barkwanci da ba a gani a baya ba.

Gidan Badamasi ya fito da jaruma Azeema

A wani labarin, mun ruwaito cewa jarumar Kannywood, Hauwa Ayawa ta sanar da cewa shirin Gidan Badamasi ne ya fito da tauraruwarta har ta yi haske.

Hauwa da a yanzu aka fi sani da Azeema Gidan Badamasi ta taka rawar 'yar Alhaji Badamasi a shirin, kuma ta nuna kwarewa a matsayin da aka ba ta.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com