Mawaki Rarara Ya Biya Kudin Sadakin Aishatul Umairah? Jarumar Ta Fadi Gaskiya
- Aishatul Umairah ta bayyana cewa alakar da ke tsakaninta da mawaki Rarara ba ta soyayya ba ce sabanin tunanin mutane
- Jarumar ta kuma karyata rade-radin cewa mawaki Dauda Kahutu Rarara ya kai kudin sadakinta, ta ce zancen jama'a ne kawai
- Umairah ta bayyana cewa cuko da mata ke yi a mazaunansu ba bakon abu ba ne, har ma wasu lokutan yana bayyana a fili
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Kano - Fitacciyar jarumar fina finan Hausa (Kannywood) Aishatul Umairah ta yi magana kan alakar da ke tsakaninta da mawaki Dauda Kahutu Rarara.
Kafofin sada zumunta sun sha daukar zafi kan alakar Aisha da Rarara, musamman ganin irin kusancin da ke tsakanin mutanen biyu.
A'isha ta magantu kan alakarta da Rarara
A wata tattaunawa da Dokin Karfe TV, wadda jarumar ta wallafa a shafinta na Instagram, A'isha ta ce alakarta da Rarara bayyananniya ce.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jaruma Aishatul Umairah ta ce mutane na zargin soyayya tsakaninta da mawaki Rarara saboda irin shakuwar da ke tsakaninsu.
"A baya na fada, komai muna yi shi tamkar mu 'yan biyu ne. Yanzu ma zan sake maimaitawa, koda yaushe muna yin abu tare, shi ya sa ake ganin haka."
Rarara ya kai sadakin Aishatul Umairah?
Mai gabatar da shirin, Bashir El-Bash, ya tambayi A'isha Umaira gaskiyar rade radin da ake yadawa cewa Rarara ya kai kudin sadakinta, sai cewa ta yi:
"Ka tambaye ni tun dazu na fada maka, karya ne ba a kai ba wallahi."
Bashir ya tambaye ta:
"Amma soyayyar akwai ta ko babu?"
A'isha ta amsa da cewa:
"Ban sani ba."
A'isha ta magantu kan mata masu ciko
Game da wata magana da ta taɓa yi a baya, lokacin da masana'antar Kannywood ta dauki zafi kan mata masu yin cuko a mazaunai.
A'isha ta ce lamarin cuko da mata ke yi ba labari ba ne kawai, wani abu ne da ya ke faruwa a fili.
"Kusan abu ne wanda ya zama ruwan dare, kusan wadanda suka yi za ka gane saboda ya bayyana kansa sosai."
- A cewar Aishatul Umairah.
Kalli bidiyon a kasa:
Aisha ta magantu kan alaka da Maishadda
A wani labarin kuma, mun ruwaito cewa jaruma Aishatul Umairah ta yi karin haske kan alakarta da babban furodusar masana’antar, Abubakar Bashir Maishadda.
Humaira ta bayyana cewa sabanin abun da mutane ke tunani, babu wani abu da ya danganci soyayya tsakaninta da Maishadda illa kawai abokin sana’arta ne da suka shaku.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng