Wani Gidan Talabijin Ya Sace Bidiyon Jarumar Kannywood, Ta na Shirin Zuwa Kotu

Wani Gidan Talabijin Ya Sace Bidiyon Jarumar Kannywood, Ta na Shirin Zuwa Kotu

  • Shahararriyar jarumar Kannywood, Hadiza Aliyu Gabon ta zargi wani gidan talabijin da sata tare da watsa bidiyonta ba da izini ba
  • Hadiza Gabon ta shaidawa gidan talabijin da ya shirya ji daga lauyoyinta, lamarin da ake ganin jarumar fim din ba ta dauka da wasa ba
  • Legit Hausa ta fahimci cewa gidan talabijin ya dauki bidiyon hirar da Gabon ta yi da mawaki Abdu Boda ya watsa ba tare da samun izini ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Da alama dai gidan talabijin na Tozali (Tozali TV) ya matukar fusata shahararriyar jarumar fina-finan Hausa, Hadiza Aliyu Gabon.

A safiyar yau Laraba ne jaruma Hadiza Gabon ta yi ikirarin cewa gidan talabijin ya sace mata wani bidiyo da ta dora a shafinta na YouTube.

Kara karanta wannan

"An bata mani suna:" Martanin tsohon Sanata kan zargin fitar da bidiyon tsiraici

Hadiza Gabon ta aika sako ga wani gidan talabijin da ya sace mata bidiyo
Hadiza Gabon ta shirya daukar mataki kan wani gidan talabijin da ya sace bidiyonta. Hoto: adizatou
Asali: Instagram

Gidan talabijin ya fusata Hadiza Gabon

A wata sanarwar gargadi da ta aikewa gidan talabijin ta shafinta na Istagram, jarumar ta nuna ba za ta lamunci wannan satar ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hadiza Gabon ta shaidawa Tozali TV cewa ya shirya ji daga lauyoyinta bayan abin da ta kira da "satar bidiyo tare da watsawa ba tare da izini ba."

Sakon jarumar ya ce:

"@Tozalitv kun sace min 'bidiyo' dina kun saka a gidan talabijin dinku ba tare da izinina ba. To ku sani, lauyoyina za su tuntube ku."

Wani bidiyo aka sacewa Gabon?

A nazarin da Legit Hausa ta yi kan wannan sako da ta wallafa, mun fahimci cewa jarumar na magana ne a kan bidiyon shirinta na 'Dakin tattaunawa da Hadiza Gabon.'

Wannan shirin dai ya yi tashe a baya bayan nan, inda jarumar ke yin hira da jaruman Kannywood, mawaka, 'yan kasuwa, 'yan siyasa da sauran manyan mutane.

Kara karanta wannan

Ma'aikata za su wataya: Tinubu ya sanya ranar fara biyan sabon albashin N70000

A sakon da ta wallafa, ana iya ganin bidiyon da gidan talabin 'sata' ya watsa ba tare da izinin jarumar ba, kuma hira ce tsakanin Gabon da mawaki Abdu Boda Katsina.

Kalli sakon Gabon a kasa:

Gabon ta maka magidanci a kotu

A wani labarin, mun ruwaito cewa jaruma Hadiza Gabon ta yi karar wani mutum, Bala Musa a gaban wata kotun majistare da ke jihar Kano.

Jarumar ta zargi Bala Musa wanda ma'aikacin gwamnati ne da bata mata suna bayan da ya yi ikirarin cewa ta cinye masa kudi da sunan za ta aure shi.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.