Yanzu-Yanzu: An Yi Babban Rashi A Kannywood, Jarumi Kawu Mala Ya Rasu

Yanzu-Yanzu: An Yi Babban Rashi A Kannywood, Jarumi Kawu Mala Ya Rasu

  • Shahararren dan wasan kwaikwayo na Kannywood, Aminu Mahmud da aka fi sani da Kawu Mala ya rasu
  • Marigayin ya shahara ne a shirin Dadin Kowa mai dogon zango na Arewa24, ya rasu ne bayan fama da ciwon zuciya
  • Abokin aikinsa, Murtala Karabati ya tabbatar da mutuwar Kawu Mala, inda ya ce bai taba jin wani yayi korafi a kansa ba.

Jihar Kano – Shahararren dan wasan kwaikwayo na Hausa wato Kannywood, Aminu Mahmud wanda aka fi sani da Kawu Mala ya rasu.

Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa Aminu Mahmud dai ya shahara ne a shiri mai dogon zango na gidan talabijin na Arewa24, Dadin Kowa.

Kawu Mala
Allah ya yi wa jarumin Kannywood, Kawu Mala, rasuwa. Hoto: Daily Trust
Asali: Facebook

Marigayin ya rasu ne a ranar Lahadi 7 ga watan Mayu bayan ya sha fama da ciwon zuciya na tsawon lokaci.

Kara karanta wannan

Peter Obi ba zai yi nasara a kotu ba, babban fasto ya ba Obi shawari kan zaben 2023

Mala ya kai akalla shekaru fiye da 20 yana wasan kwaikwayo kuma shahararsa ta bayyana ne a shirin Dadin Kowa na Aewa24.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Marigayin ya rasu ya bar matarsa daya da ‘ya’ya 10, tuni aka binneshi kamar yadda addinin Musulunci ya tanadar.

Abokin aikinsa yayi bayani a kansa

Abokin aikinsa, Murtala Karabiti, ya bayyana mutuwar Kawu Mala da cewa:

"A matsayin babban rashi wanda za a dade kafin a maye gurbinsa”, in ji Murtala

Ya kara da cewa marigayin zai dade a zuciyarsu basu manta da shi ba, wanda ya kawo ci gaba sosai a masana’antar Kannywood.

“Dakta, kamar yadda muke masa lakabi, abokin kowa ne, na sanshi fiye da shekaru 20 kuma a duk tsawon wannan shekarun, ba wani da ya taba fadin mummunan abu akan marigayin, muna addu’ar Allah ya gafarta masa”, n ji shi.

Kara karanta wannan

“Za Su Kashe Ni”: Matashin Da Aka Yi Safarar Sassan Jikinsa Ya Roki Gwamnatin Birtaniya Ta Ba Shi Mafaka

"Na So 'Ya'yana Su Yi Fim Amma Sun Nuna Ba Saso ", Ali Nuhu

A wani labarin, Shahararren jarumi fina-finai na Kannywood kuma mai bada umurni a masana'antar Kannywood, Ali Nuhu, ya bayyana cewa ya so ƴaƴan sa su yi harkar fim amma sai suka zaɓi bin wata hanyar daban.

Jaridar Daily Trust tace jarumi Ali Nuhu ya bayyana cewa, yaron sa Ahmad Ali Nuhu wanda ya ke da shekara 16 a duniya, amma ya nuna yana son harkar kwallon kafa yayin da ɗiyarsa Fatima, ta ke son karantar International relations a Jami'a.

Asali: Legit.ng

Online view pixel