Kannywood: Bayan Kama Murja, Gwamnatin Kano Ta Kwace Lasisin Wata Babbar Furodusa

Kannywood: Bayan Kama Murja, Gwamnatin Kano Ta Kwace Lasisin Wata Babbar Furodusa

  • Bayan shafe dogon lokaci hukumar tace fina-finai na kokarin tattaunawa da furodusa Hajiya Amart, a karshe dai an soke lasisinta
  • Abba El-Mustapha, shugaban hukumar ya ce Amart ta raina hukumar, ta takurawa masu tura fina-finai kuma tana karbar kudin jama'a
  • A zantawar wasu furodusoshi da Legit Hausa, sun yi korafi kan yadda masu tura fina-finai ke rage darajar shirye-shiryen da suke dorawa a Youtube

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Hukumar tace fina-finai ta jihar Kano ta kwace lasisin wasu kamfanoni biyu mallakin Aisha Tijjani wacce aka fi sani da Hajiya Amart.

Ta hanyar soke lasisin ta, yanzu an dakatar da Amart daga baje kolin fina-finta ko rarrabawa, da kuma sa hannu a ayyukan masu tura fina-finai a cikin jihar.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun hallaka mutum 9, sun sace tsohon daraktan CBN da wasu 34 a jihar Arewa

Kannywood: An dakatar da Hajiya Amart daga yin fim a Kano
Abba El-Mustapha ya dakatar da Hajiya Amart daga gudanar da ayyukan fim a jihar Kano. Hoto: @abbaelmustaph1
Asali: Twitter

Babban Sakataren Hukumar, Alhaji Abba El-Mustapha, yayin wani taron manema labarai jiya, ya ce kamfanonin sune Kannywood Enterprises Limited da Amart Entertainment.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Laifukan da ake tuhumar Amart ta aikata.

A cewarsa, soke lasisin ya biyo bayan rashin bin dokokin hukumar ne da kuma bata wa mutume suna da furodusar ta yi, The Nation ta ruwaito.

An tattaro cewa hukumar na samun korafe-korafe daga kungiyar masu tura fina-finai ta jihar Kano (KADA) akan kamfanonin.

An kuma yi zargin cewa Hajiya Amart ta yi amfani da wasu jami’an tsaro wajen karbar kudi daga hannun mutane.

Kotu ta garkame 'yar Tiktok, Murja Kunya

Sakataren ya kuma kara da cewa hukumar ta gayyaci Hajiya Amart sau da dama domin a warware matsalolin amma ta ki amincewa da gayyatar.

Dakatarwar da aka yi wa Amart na zuwa ne jim kadan bayan da wata kotu a Kano ta ba da umarnin garkame Murja Kunya, shahararriyar 'yar TikTok din nan a gidan gyaran hali.

Kara karanta wannan

Badakalar N72m: ICPC ta gurfanar da tsohon shugaban ASCSN bayan Tinubu ya dakatar da shi

Wannan kuwa ya biyo bayan korafin da aka shigar akanta, na aikata laifukan da suka shafi aikata badala da bata tarbiya, inda aka yanke wa abokin badalar nata watanni shida a gidan maza.

Abun da furodusoshi suke cewa game da wannan hukunci

A zantawarsa da Legit Hausa, wani Furodusa, Haruna Gidaje ya ce ba zai iya yin magana akan soke lasisin Hajiya Amart ba amma dai batun masu tura fina-finai ke damun sa.

Ya yi nuni da cewa, furodusa zai sha bakar wahala tare da kashe kudi wajen samar da fim amma da zaran ya dora a YouTube, masu tura fina-finai za su sauke su rinka siyarwa ba tare da izini ba.

Gidaje ya ce wannan abu da masu tura fina-finai suke yi kan karya darajar fim din su, ta yadda mutane za su gwammace su je a tura masu maimakon su kalla a YouTube.

Amma ya ce ba duka ne masu tura fina-finan ke yin haka ba, wasu na tuntubar furodunsa har ma su biya shi kafin su rinka kasuwancinsa.

Kara karanta wannan

Tsadar abinci: Gwamnati ta rufe wani babban kanti a Abuja, an samu cikakken bayani

Hukumar Hisba a Kano ta gargadi 'yan iskan Gari

Tun da fari, Legit Hausa ta ruwaito cewa hukumar Hisbah a jihar Kano, ta ce ba za ta sake saurara wa 'yan iskan masu fakewa da TikTok sun lalata tarbiyya a Kano ba.

Mataimakiyar shugabar sashen mata ta Hisba, Dr. Khadijah Sulaiman ta bayyana hakan jim kadan bayan da kotun ta garkame Murja Kunya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.