Nazarin Shekarar 2023: Jerin Jaruman Kannywood 5 da Suka Riga Mu Gidan Gaskiya
- Akalla jaruman Kannywood shida ne suka rigamu gidan gaskiya daga watan Janairu zuwa Disambar shekarar 2023
- A yayin da shekarar ke neman karewa, Legit Hausa ta yi waiwaye kan silar mutuwar jaruman da abubuwan da suka faru a baya
- Masana'antar Kannywood ta girgiza da rasuwar jarumin barkwanci Kamal Aboki, amma ta fi girgiza a lokacin da Aminu S. Bono ya rasu
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Mutuwa ta ratsa masana'antar shirya fina-finan Hausa (Kannywood), inda ta rinka yin dauka dai dai daga watan janairun 2023 har zuwa watan Nuwamba.
Kamar yadda rahotanni suka bayyana, akalla jaruman Kannywood shida ne suka riga mu gidan gaskiya a cikin wannan shekarar, inda mutuwar mai ba da umurni, Aminu S Bono ta fi girgiza masana'antar.
A cikin wannan wallafar, Legit Hausa ta yi nazarin jaruman Kanywood da suka rasu a shekarar 2023, sanadin mutuwarsu da kuma abubuwan da suka faru bayan mutuwar ta su.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ga jerin sunayen jaruman:
Janairu, 2023 - Kamal Aboki
A ranar 16 ga watan Janairu, 2023 Allah ya karbi rayuwar jarumin barkwanci, Kamali iliyasu Usman wanda aka fi sani da Kamal Aboki sanadin hatsarin mota a hanyar Borno.
Rahotan mujallar Fim Magazine ya bayyana cewa mutuwar Kamal ta girgiza Kanywood kasancewarsa matashi wanda tauraruwarsa ta fara haskawa.
Kamal ya fara wasan barkwanci a shafinsa na Instagram, daga bisani ya koma TikTok da Youtube, har dai ya fara fitowa a shirye-shirye da suka hada da 'Wuf'.
Janairu, 2023 - Abdulwahab Awarwasa
Ana tsaka da jimamin rasuwar Kamal Aboki, sai kuma mutuwar jarumi kuma furodusa a Kanywood, Abdulwahab Awarwasa ta sake jefa masana'antar cikin alhini.
Awarwasa ya rasu ne a ranar 23 ga watan Janairu bayan fama da rashin lafiya, kuma ya fito a shirin fim din 'A Duniya', kamar yadda jaridar Leadership Hausa ta ruwaito.
Mayu, 2023 - Kawu Mala (Aminu Muhammad)
A yammacin ranar Lahadi, 7 ga watan Mayun 2023 Allah ya dauki rayuwar Malam Aminu Muhammad wanda aka fi sani da Kawu Mala a shirin 'Dadin Kowa' na tashar Arewa24.
Rahoton jaridar Aminiya ya bayyana cewa ciwon zuciya ne ya yi silar ajalin jarumin, wanda ya bar mata daya da yara 12. Kannywood ta kadu da rasuwar Kawu Mala saboda dattakonsa.
Oktoba, 2023 - Hajiya Binta Ola
A safiyar ranar Laraba, 4 ga watan Oktoba, 2023, shugaban hukumar tace fina-finan Hausa, Abba El-Mustapha ya sanar da rasuwar dattijuwar jaruma a Kannywood, Hajiya Binta Ola.
Legit Hausa ta ruwaito cewa Binta Ola ta rasu a daren ranar Talata, kuma an yi jana'izarta a safiyar Laraba. Ola ta na a cikin shirin 'Dadin Kowa' na Arewa24 da wasu shirye-shirye da dama.
Nuwamba, 2023 - Samanja (Usman Baba Pategi)
Duk da kasancewarsa tsohon jarumi, wanda ya yi shuhurarsa a shekarun 1980, masana'antar Kannywood da Najeriya ta girgiza da rasuwar Samanja mazan fama (Usman Baba Pategi).
Sashen Hausa na VOA, ya ruwaito cewar daya daga cikin 'yayan Samanja ne ya sanar da rasuwar jarumin a ranar Lahadi, 12 ga watan Nuwamba 2023.
Shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya mika sakon ta'aziyyar Samanja wanda ya tsohon sojan Najeriya ne, inda Tinubu ya roki iyalan Pategi, Kannywood da masoyansa su dauki dangana.
Nuwamba, 2023 - Aminu S. Bono
Ba a gama jimamin rasuwar Samanja Mazan Fama ba, Kannywood ta sake girgiza da rasuwar babban darakta kuma jarumi, Aminu S. Bono, wanda ya rasu a ranar 20 ga watan Nuwamba, 2023.
Shugaban hukumar tace fina-finai, Abba El-Mustapha ne ya sanar da rasuwar Aminu S. Bono a shafinsa na Facebook, mutuwar da aka juma ba a ji irin ta a masa'antar ba.
Bayan rasuwar jarumin, furodusa Abdul Amart Mai Kwashewa ya sayawa iyalan Bono gida, yayin da mawaki Dauda Kahutu Rarara ya dauki nauyin karatun 'ya'yan marigayin, kamar yadda Legit Hausa ta ruwaito.
Wasu mata na shiga harkar fim don bunkasa karuwancinsu - Saudat Amin
Jarumar fina-finan Hausa, Saudat Amin ta gazgata wani ikirari da mawaki Abdullahi Amdaz ya yi na cewar ana kawalci da zinace-zinace a masana'antar Kannywood.
Saudat Amin ta ce ko ita sai da aka yi mata kan ta waye da ta shiga masana'antar, inda ta tabbatar da cewa mata da yawa na shiga harkar fim don bunkasa harkar karuwancinsu.
Asali: Legit.ng