Muna Taya Murna: Jarumar Kannywood Ta Cika Shekaru 30, Ta Yi Kalamai Masu Ratsa Zuciya

Muna Taya Murna: Jarumar Kannywood Ta Cika Shekaru 30, Ta Yi Kalamai Masu Ratsa Zuciya

  • Jarumar Kannywood da Nollywood Rahama Sadau ta cika shekaru 30 da haihuwa, ta yi kalamai masu ratsa zuciya
  • A ranar 7 ga watan Disamba 1993 aka haifi Rahama Sadau a jihar Kaduna, kuma ta fara shuhura a fim a shekarar 2013
  • Sadau na daya daga cikin jaruman fim a Afrika da suka samu damar fitowa a finan-finan kasashen waje, musamman Indiya

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Kaduna - Fitacciyar jarumar fina-finan Hausa (Kannywood) da na Kudu (Nollywood) Rahama Sadau, ta saki wasu zafafan hotuna yayin da ta ke murnar cika shekara 30 da haihuwa.

Rahama Sadau ta yi kaurin suna a masana'antar Kannywood bayan fitowa cikin manyan fina-finai da suka hada da Rariya, Gani ga Wane, Jinin Jikina da sauran su.

Kara karanta wannan

"Ina bakin ciki matuka": Gwamnan Kano ya yi alhinin mutuwar Asm'u Sani da kansa ta kashe

Rahama Sadau
Jarumar Kannywood, Rahama Sadau ta cika shekara 30 da haihuwa, ta saki zafafan hotuna. Hoto: Rahama Sadau
Asali: Facebook

An haifi Sauda a ranar 7 ga watan Disam, 1993 a jihar Kaduna, kuma tauraruwarta ta fara haskawa bayan fitowa a fim din Gani ga Wane a shekarar 2013, rahoton Wikipedia.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kalaman Rahama Sadau ranar haihuwarta

Da take murnar zagayowar ranar haihuwa na cika shekaru 30, Rahama ta wallafa wasu zafafan hotuna a shafukanta na sada zumunta, inda ta taya kanta murna.

Jarumar ta wallafa cewa:

"Na cika shekaru 30.
"Ina matukar farin ciki da dukkanin soyayya da damarmakin da na samu tsawon wadannnan shekaru na rayuwata.
"Ina rokon Allah ya sanya albarka a wannan shekarar da ma wasu masu zuwa nan gaba, in samu dawwamammen farin ciki, koshin lafiya, yalwar arziki da karin damarmaki."

Sadau ta ci gaba da cewa:

"Ina rokon Allah cikin kaunarsa ya karbi dukkanin addu'o'in da na yi da wadanda zan yi nan gaba.

Kara karanta wannan

Dan Kano mai shekaru 26 da ya auri Ba'amurkiya mai shekaru 49 ya shiga aikin sojan Amurka

"Ina rokon Allah ya ci gaba da lullube ni da albarkarsa da dukkanin wadanda ke kusa dani."

Duba hotunan da ta wallafa a kasa:

Rahama Sadau
Zafafan hotunan Rahama Sadau na cika shekaru 30. Hoto: Rahama Sadau
Asali: Facebook
Rahama Sadau
Zafafan hotunan Rahama Sadau na cika shekaru 30. Hoto: Rahama Sadau
Asali: Facebook

MOPPAN ta dakatar da Rahama Sadau

Rahama Sadau ta samu gagarumar nasara inda ta fito a cikin wani fim din Indiya mai suna Khuda Hafiz, lamarin da ya sa ta kara yin kaurin suna.

A ranar 3 ga watan Oktoba, 2016 ne kungiyar masu shirya fim ta MOPPAN ta dakatar da Sadau bayan fitowa a wata wakar soyayya da mawaki Classiq Q.

A wakar anga jarumar na rungumar mawakin, lamarin da MOPPAN ke ganin ya saba wa al'ada da tarbiyar Musulunci, sai dai daga baya ta nemi afuwar kungiyar.

Mata na shiga fim don bunkasa karuwancin su - Saudat

A wani labarin, jaruma Saudat Amin ta ce sai da ta sayar da sarkokin zinaren da aka ba ta lokacin aurenta don ta yi fim, amma a karshe aka cinye kudin.

Batu kan jarumai mata da ke shiga Kannywood kuwa, jarumar ta ce wasu matan na shiga fim don bunkasa sana'ar karuwancinsu, Legit Hausa ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.