“Mun Barranta Da Rarara”, Mawakan Kannywood Sun Ziyarci Buhari a Daura

“Mun Barranta Da Rarara”, Mawakan Kannywood Sun Ziyarci Buhari a Daura

  • Wasu daga cikin mawakan Kannywood sun kai ziyara ga tsohon shugaban kasar Najeriya, Muhammadu Buhari, a gidan sa da ke garin Daura, jihar Katsina
  • Mawakan, bisa jagorancin Ali Jita, sun ce sun kai ziyarar ne domin sanar da Buhari cewa har yanzu suna goyon bayansa duk da cewa wa'adin mulkinsa ya kare
  • Wannan ziyarar ta su na zuwa ne jim kadan bayan da shahararren mawakin siyasa, Dauda Kahutu Rarara, ya caccaki gwamnatin Buhari

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Daura, Jihar Katsina - Shararrun mawakan Kannywood kuma masoyan tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari da jam'iyyar APC, sun kai masa ziyara a garin Daura dake jihar Katsina, inda yake zaune a halin yanzu.

Kara karanta wannan

Rikicin Rivers: Fubara ya gana da Wike, Ya ce ‘mai gida na har gobe’

Mawakan, a karkashin kungiyar 'Murya Daya', sun ziyarci Mista Buhari ne domin ci gaba da nuna goyon baya da biyayya a gare shi, duk da karewar wa’adin mulkinsa.

Mawakan Kannywood sun gana da Buhari
Mawakan Kannywood sun ziyarci Buhari a Daura, sun nuna goyon bayansu gare shi, tare da juya wa Rarara baya Hoto: Buhari Sallau
Asali: Twitter

Tawagar ta samu jagorancin shugabanta, fitaccen mawaki Ali Jita.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ziyarar ta zo ne a daidai lokacin da daya daga cikin abokan sana'arsu, Dauda Kahuta Rarara, ya fusata a baya-bayan nan, inda ya zargi gwamnatin Mista Buhari da gazawa wajen cika alkawuran da ta daukar wa 'yan Najeriya.

Mawakan Kannywood sun yi mubayi'a ga Buhari

Wani na hannun damar daya daga cikin mawakan, Suleiman Hassan, wanda ya ke da masaniya kan wannan ziyarar, ya shaida wa Premium Times ranar Talata cewa, mawakan sun je Daura ne domin mubayi’a ga Buhari tare da barranta daga kalaman mawaki Rarara.

Ya ce:

“Eh, ziyarar ta kasance don gaishe da tsohon shugaban kasar ne kawai. Amma kuma, sun je ne don sanar da tsohon shugaban kasar cewa har yanzu suna tare da shi".

Kara karanta wannan

Miyagu sun kai kazamin hari gidan babban jigon PDP kuma tsohon kwamishina, sun jefa bama-bamai

"Ba a yi maganar Rarara a wajen ziyarar ba, amma tsohon shugaban kasar ya ji abin da Rarara ya fada game da shi da gwamnatinsa. Ya fi kowa cin gajiyar gwamnatin Buhari a mawakan arewa”.

“Na Yi Nadamar Tallata Buhari”, Rarara

Shahararren mawakin siyasa, Dauda Kahuru Rarara ya caccaki Buhari kan irin yadda ya gudanar da mulki a kasar.

Rarara ya bayyana haka ne a cikin wani faifan bidiyo da hadiminsa, Rabi’u Garba Gaya ya yada a kafar sadarwa.

Me Rarara ke cewa kan Buhari?

Kahutu ya ce Buhari sai da ya kashe kasar nan sannan ya sake ta bayan ya lalata komai a kasar.

Ya ce ya kamata mutane su fito su fadi gaskiya amma sun gagara, inda ya ce a lokacin PDP an bayyana cewa kasar a mace ta ke don haka mutane su ka amince da Buhari.

Asali: Legit.ng

Online view pixel