Babbar magana: Buhari ya lalata Nigeria fiye da tunanin mutane - Gwamna Fayose

Babbar magana: Buhari ya lalata Nigeria fiye da tunanin mutane - Gwamna Fayose

- Gwamna Ayodele Fayose, ya yi ikirarin cewa shugaban kasa Buhari ya lalata kasar fiye da kimar da za a iya gyarata

- Gwamnan ya ce Buhari zai fuskanci fushin 'yan Nigeria a zaben 2019

- Ya ce tattalin arziki da ya habbaka a gwamnatin Dr. Goodluck Jonathan, yanzu ya karye karkashin Buhari

Gwamna Ayodele Fayose na jihar Ekiti, ya yi ikirarin cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya lalata kasar fiye da kimar da za a iya gyarata, yana mai cewa tuni 'yan Nigeria suka gaji da wannan salon mulkin kama karya na shugaban kasar.

Fayose a cikin wata sanarwa daga mai tallafa masa na musamman kan kafofin watsa labarai, Lere Olayinka, da ya bayar a ranar Litinin, gwamnan ya ce shugaban kasa zai fuskanci fushin 'yan Nigeria a zaben 2019 ba wai PDP ko sauran jam'iyyu bane za su fuskanci hakan suk kadai ba.

Gwamna Fayose ya ce: "Kasashen ketare sun ce cin hanci da rashawa ya fi kamari a gwamnatin Buhari idan aka kwatanta da lokutan baya.Su kansu 'yan Nigeria sun san cewa yan ta'adda dake fakewa da sunan makiyaya sun shiga inuwar Boko Haram ne a gwamnatin Buhari.

Babbar magana: Buhari ya lalata Nigeria fiye da tunanin mutane - Gwamnan Fayoshe
Babbar magana: Buhari ya lalata Nigeria fiye da tunanin mutane - Gwamnan Fayoshe
Asali: Depositphotos

KARANTA WANNAN: Fasinjoji 15 sun gamu da ajalinsu bayan da motarsu ta kama da wuta a kusa da Abaji

"Tattalin arziki da ya habbaka a gwamnatin tsohon shugaban kasa Dr. Goodluck Jonathan, yanzu tattalin ya karye karkashin Buhari kuma har yanzu an gaza farfado da shi. Don haka ina da tabbacin cewa zaben 2019 ba zabe bane na jam'iyya, hatta shi kansa Buhari zaben zai shafeshi don zai fuskanci matsayar 'yan Nigeria.

"Zaben 2019 zai kasance zabe ne tsakanin 'yan Nigeria da Buhari ba wai tsakanin PDP da Buhari ba, ko PDP da APC ba, musamman ganin yadda Buhari ya gaza aiwatar da wasu ayyukan azo a gani na bunkasa rayuwar yan Nigeria," a cewar gwamnan.

Gwamna Fayose ya jadda cewa "Buhari ya lalata Nigeria. Ya lalata rayukan 'yan Nigeria ba adadi. Tsananin wahalar da ake ciki a yau ya wuce a misalta shi. Babban abun ma shine, yadda ya karya aminci da yardar da 'yan Nigeria ke masa, don haka suna nan suna jiransa a 2019 don huce haushinsu."

Sanarwa: Nan bada dadewa ba, shafin Hausa.legit.ng zai sauya suna zuwa Hausa.legit.ng. Hakika wannan babban ci gaba ne kuma muna fatan zaku cigaba da kasancewa tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel