Abba Gida Gida Ya Nada Yar Jin Kai Fauziyya D Sulaiman Babbar Mai Tallafa Masa

Abba Gida Gida Ya Nada Yar Jin Kai Fauziyya D Sulaiman Babbar Mai Tallafa Masa

  • Gwamnan jihar Kano ya bai wa Fauziyya D Sulaiman a matsayin babbar mai ba shi shawara kan harkokin mabukata da gajiyayyu
  • Fauziyya ta shahara sosai wajen tallafawa mabukata da gajiyayyu musamman a shafukan soshiyal midiya
  • Marubuciyar na da wata gidauniyar taimako mai suna ' Creative helping needy foundation'

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Jihar Kano - Mai girma gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, wanda aka fi sani da Abba Gida-Gida ya nada babbar mai ba shi shawara ta musamman kan harkokin gajiyayyu.

Gwamnan ya nada Fauziyya D Sulaiman, yar jin kai kuma shugabar gidauniyar ' Creative helping needy foundation' a matsayin mai tallafa masa kan harkokin mabukata da gajiyayyu.

Abba Gida-Gida ya nada Fauziyya D Sulaiman mukami
Abba Gida Gida Ya Nada Yar Jin Kai Fauziyya D Sulaiman Babbar Mai Tallafa Masa Hoto: Fauziyya D. Sulaiman
Asali: Facebook

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da marubuciyar ta wallafa a shafinta na Facebook inda ta mika godiya a kan wannan mukami da gwamnan na Kano ya bata.

Kara karanta wannan

Shugaban 'Yan Bindiga Ya Ayyana Kansa a Matsayin Gwamnan Jihar Arewa? Gaskiya Ta Bayyana

Dalilin nada Fauziyya mukamin SSA, Sanusi Oscar

Babban mai ba gwamnan shawara na musamman kan harkar Kannywood, Sunusi Hafiz (Oscar 442) ne ya gabatarwa Fauziyya da takardar nadin nata.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Oscar ya kuma bayyana cewa gwamna ya ba ta mukamin ne saboda yana bibiyar shafinta kuma yana ganin aikin tallafi da jin kai da take yi.

An tattaro cewa

Ta rubuta a shafin nata:

"ABUN KAMAR DA WASA
"Dazu wani ya kirani ya gaya mun suna meeting (ganawa) da mai girma Gwabnan Kano Abba Kabir Yusif, ya yi ta ambaton irin aikin da na ke yi saboda yana bibiyar shafina, ya ce tabbas kina abu mai kyau ki ci gaba na yi godiya.
"Da laasar kuma sai abokin aikina Nasir Nid ya shigo office yana dariya ya ce Uwar marayu mai girma gwabna ya baki mukami akan aikinki na jinkai, na ce tsokanata ka ke ya yi, ya yi ta rantsuwa muna dariya.

Kara karanta wannan

Gwamnan PDP Ya Bayyana Mutanen da Suka Kitsa Kai Hari Ɗakunan Ɗalibai Mata Na Jami'a Suka Yi Lalata da Su

"Zuwa can sai ga kiran Sunusi Oscar ya ce mun hajiya Fauziyya mai gurma Gwabna ya baki mukamin SSA, na ce ni kuma, ya ce eh yanzu haka muna meeting da shi zan kira ki idan mun kammala, zuwa can ya kira ya ce mu hadu.
"Bayan mun hadu ya bani takardarnan ya ce mai girma Gwabna ne ya ce a baki, na rike baki da mamaki na ce ni da ba yar siyasa ba yaya zaa bani mukami, sai ya ce eh ai daman ba akan siyasa aka zabe ki ba, mai girma Gwabna ya baki mukami akan aikin da ki ke yi na tallafi da jinkai domin yana ganin aikinki yana bin fejinki hankalinsa yana tashi akan duk abun da ki ke sakawa, ga takardar ki amsa.
"Na amshi takardar na kalla, na ce yanzu wannan daga hannun gwabna ta ke, ya ce kwarai kuwa duk Kano wa ya isa ya yi rubutu da jan biro idan ba gwabna na.

Kara karanta wannan

Ganduje Ya Yi Magana Kan Sabon Rikicin Da Ya Ɓarke a Jam'iyyar APC, Ya Gana da Gwamnan Arewa

"Kamar dai yadda ku ke ganin wannan takarda mai girma Gwabnan Kano ya bani mikamin SENIOR SPECIAL ASSISTANT NEEDY AND VULNERABLE, ina godiya kwarai da gaske ga mai Girma Gwabna.
"Ina neman addu'ar ku bisa wannan nauyi da Mai girma Gwabna ya dora mun yan'uwa, Allah ya sa ya zama alkairi ga al'ummar jahar Kano, Allah ya bani ikon cinye jarrabawar da ke tattare da wannan nauyin Amin ya Allah."

Legit.ng ta tuntube ta don jin karin bayani daga gareta amma bata amsa kiran da aka yi mata ta wayar tarho ba a daidai lokacin kawo wannan rahoto aka kuma mun tura sako ta shafinta na soshiyal midiya amma ba amsa.

Abba Gida-Gida ya saki miliyan 854 don auren zawarawa a jihar Kano

A wani labarin, mun ji a baya cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf ya amince da sakin Naira miliyan 854 domin daura auren zawarawa a jihar Kano.

Abba Gida-Gida ya ce sun yanke wannan hukunci ne yayin zaman majalisar zartarwa na jihar Kano wanda ya gudana a ranar Laraba, 23 ga watan Agusta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng