Gwamnatin Abba Gida-Gida Ta Soke Lasisin Yan Kannywood Gaba Daya

Gwamnatin Abba Gida-Gida Ta Soke Lasisin Yan Kannywood Gaba Daya

  • Gwamnatin Abba Kabir Yusuf na jihar Kano ta ta soke lasisin yan masa'antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood gaba daya
  • Shugaban hukumar tace fina-finai ta jihar Kano, ya yi tsoki kan wannan mataki da gwamnatin jihar ta dauka
  • Al-Mustapha ya ce sun dauki matakin ne domin tsaftace masana'antar shirya fina-finan ba wai don batawa wani ba

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Jihar Kano - Rahotanni sun kawo cewa gwamnatin jihar Kano karkashin jagorancin Abba Kabir Yusuf wanda aka fi sani da Abba Gida-Gida ta soke gaba daya lasisin yan masa'antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood.

Shugaban hukumar tace fina-finai ta jihar Kano, Abba Almustapha, ya bayyana dalilan da suka sanya gwamnatin jihar daukar wannan makali.

Gwamnatin Kano ta soke lasisin yan Kannywood
Gwamnatin Abba Gida-Gida Ta Soke Lasisin Yan Kannywood Gaba Daya Hoto: Abba El-Mustapha1
Asali: Facebook

Abin da ya sa muka soke lasisin yan Kannywood - Abba El-Mustapha

A hirar da ya yi da Freedom Radio, Almustapha ya ce sun dauki wannan matakin ne domin tsaftace harkar fim gaba dayan ta domin a cewarsa ana abubuwa babu tsari a masana'antar ta fina-finai.

Kara karanta wannan

Hukumar DSS Ta Magantu Kan Rigimar Da Ta Faru Kan Emefiele a Kotu, Ta Faɗi Matakin Da Za Ta Ɗauka

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce a halin da ake ciki a yanzu kowa a masana'antar yana amsa sunar jarumi, furodusa, mai daukar hoto ba tare da wani tsari ba saboda haka soke lasisin zai sa su samu damar yi wa lamarin tufkar hanci.

A cewarsa da wannan mataki da suka dauka, yanzu sai sun tantance mutum sun tabbatar da nagartarsa, sun tabbatar da ya cancanta kafin ma su ba shi lasisin aiki.

Har ila yau, shugaban hukumar tace fina-finan ya ce wannan zai sake basu damar sanin ta inda mutum ya shigo masana'antar ta yadda koda wani abu ya faru a gaba za su san ta ina za su faro ta.

A bangaren tallace-tallace, Almustapha ya ce akwai masu tallace-tallacen magunguna wanda a yanzu suna so sai an tantance magungunansu da kuma maganganun da suke amfani da shi na batsa da sauransu maganganu da bai kamata al'umma su ji ba.

Kara karanta wannan

'Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa da Wani Fitaccen Ƙwararren Likita Yana Kan Aiki a Arewacin Najeriya

Har wayau, a cikin bidiyon jawabinsa, shugaban hukumar tace fina-finan ya ce an soke lasisin yan gidajen gala ta yadda sai sun zo sun sabonta rijistarsu domin su kawo tsafta da kawar da bara gurbi a cikinsu.

Ya kuma tabbatar da cewar ba wai sun kawo wannan matakai don takurawa mutanen masana'antar ba ya ce suna yi ne don inganta sana'ar.

Yan Kannywood za su dara a gwamnatin Abba Kabir Yusuf, inji Abba Al-Mustapha

A baya mun ji cewa fitaccen jaruminnan na masana'antar Kannywood, Abba Ruda, wanda aka fi sani da Abba El-Mustapha, ya bayyana cewa yan wasan fina-finan Hausa za su dara a wannan gwamnati ta Abba Gida Gida.

Ya bayyana hakan a wata hira da ya yi da gidan rediyon Freedom da ke Kanon Dabo.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng