“Za Su Kashe Ni”: Matashin Da Aka Yi Safarar Sassan Jikinsa Ya Roki Gwamnatin Birtaniya Ta Ba Shi Mafaka

“Za Su Kashe Ni”: Matashin Da Aka Yi Safarar Sassan Jikinsa Ya Roki Gwamnatin Birtaniya Ta Ba Shi Mafaka

  • Bayan kammala shari'ar Sanata Ike Ekweremadu, matarsa Beatrice da Dr Obeta, sabon bayani ya billo
  • Wanda abun ya ritsa da shi, David Nwamini, ya ce baya so ya dawo Najeriya saboda yana tsoron rayuwarsa na cikin hatsari
  • Nwamini ya ce za a iya kama shi ko ma a kashe shi da zaran na yawo kasar don haka ya fi so ya zauna a Birtaniya

David Nwamini, mai shekaru 22 wanda shine musababbin shari'ar safarar sassan jiki na Sanata Ike Ekweremadu da matarsa Beatrice Ekweremadu ya ce baya so ya koma Najeriya.

Jaridar Vanguard ta rahoto cewa ya so ya ci gaba da kasancewa a kasar Birtaniya domin "suna iya kama shi ko su kashe shi a Najeriya."

Sanata Ike Ekweremadu, David Nwamini da Beatrice Eweremadu
“Za Su Kashe Ni”: Matashin Da Aka Yi Safarar Sassan Jikinsa Ya Roki Gwamnatin Birtani Ta Ba Shi Mafaka Hoto: BBC Pidgin
Asali: UGC

Nwamini ya shigo rayuwar ahlin Ekweremadu da idon duniya bayan an dauke shi zuwa kasar Birtaniya daga Najeriya domin baiwa diyar sanatan mai shekaru 25, Sonia koda.

Kara karanta wannan

Shugaba Buhari Ya Kara Yin Muhimman Nade-Nade Saura Kwana 24 Ya Sauka Mulki

A cikin tsare-tsaren, sai Nwamini ya tunkarin hukumomin kasar Birtani domin neman ceto ga rayuwarsa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wannan ci gaban ya yi sanadiyar kama dan majalisar da matarsa, inda aka tura kowannensu magarkama.

Nwamini ya tuna cewa bai da masaniya a kan dukka tsare-tsaren domin yana ta kamun kafa don ya tafi Landan din.

Jaridar Punch ta nakalto Nwamini na cewa:

"Shi (Dr Obina Obeta) bai fada mani ya kawo ni nan bane saboda wannan dalilin. Bai fada mani komai game da hakan ba.
"Da ba zan yarda da duk wannan ba. Jikina ba na siyarwa bane."

Ya ci gaba da bayyana cewa an yi masa tayin aiki a kasar Birtaniya.

Ya ce:

"Na damu da tsaron lafiyata a Najeriya. Wadannan mutanen za su iya yin komai. Ina tunanin za su iya kama ni ko su kashe ni a Najeriya.

Kara karanta wannan

Shehu Sani ya Bada Muhimman Shawarwari 4 da Za su Iya Taimakon Bola Tinubu a Mulki

"Shirina a yanzu shine yin aiki sannan na samu ilimi da kuma buga kwallon kafa," in ji David yana mai cewa baya son karbar diyya daga muggan mutane domin zai kawo masa bakar kaddara."

Nwamini ya tuna cewa an tunkari mahaifinsa inda aka yi masa barazana kan ya sa shi hakura da shari'ar.

Diyar Ekweremadu ta magantu a kan garkame mahaifanta

A gefe guda, mun ji cewa Sonia Ekweremadu, diyar Sanata Ike Ekweremadu ta ce ta shiga damuwa a kan hukuncin da kotun Birtaniya ta yankewa iyayenta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel