Kannywood: Saleem Tijjani Ibrahim Ya Angwance Da Zukekiyar Amaryasa Kaltume

Kannywood: Saleem Tijjani Ibrahim Ya Angwance Da Zukekiyar Amaryasa Kaltume

  • Saleem, dan marigayi daraktan fina-finan Hausa, Tijjani Ibrahim ya angwance da dalelliyar amaryarsa
  • An kulla aure tsakanin Saleem Tijjani Ibrahim da amaryarsa Kaltume a ranar Juma'a, 25 ga watan Yuli inda aka sha shagali
  • Masoya da abokan arziki ciki harda abokan sana'ar mahaifinsa sun yi masa kara wajen raya wannan rana mai muhimmanci a rayuwarsa

Jigawa - An daura auren Saleem, babban dan fitaccen darakta masana'antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood, Marigayi Tijjani Ibrahim da kyakkyawar amaryarsa.

Saleem Tijjani Ibrahin ya angwance ne da kyakkyawar matarsa mai suna Zubairu a ranar Juma'a, 25 ga watan Nuwamba a babban masallacin Juma'a na Garu, fadar sarkin Dutse da ke jihar Jigawa.

Mujallar Fim ta rahoto cewa dandazon jama'a sun shada daurin auren wanda aka kulla kan sadaki naira 50,000.

Kara karanta wannan

'Diyar Shugaban Kasa, Hanan Buhari, Ta Bude Gidauniyar Kanta Yau a Aso VIlla

Ango Saleem, amaryarsa da yan taya murna
Kannywood: Saleem Tijjani Ibrahim Ya Angwance Da Zukekiyar Amaryasa Kaltume Hoto: Mujallar fim
Asali: UGC

Barwan Dutse shi ya yi waliyin amarya inda ya baiwa Saleem aurenta sannan Wamban Dutse da Farfesa Ado Bala suka karbar mashi auren.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dandazon jama'a sun halarci daurin auren

Daurin auren ya samu halartan manyan mutane da suka hada da Group Captain Suleiman Adamu mai ritaya, Alhaji Dr. Ishaq Hadejia (Manajan Daraktan gidan Talbijin na Jigawa), Ma’ajin Hadejia.

Sauran mutanen sun hada da Danburan Dutse, ma’aikatan Gidan Talbijin da Rediyo na Jigawa, ma’aikatan Hukumar Ruwa ta Jihar Kano, ma’aikatan Gadawur Global Investment Ltd da sauransu.

Da yake jawabin godiya, ango Saleem ya nuna jin dadinsa tare da nuna dumbin godiya ga mahaifa, yan uwa da abokan arziki da suka taya shi raya wannan rana.

Mujallar Fim ta kuma rahoto cewa Saleem mika godiya ta musamman ga abokan aikin mahaifinsa yan Kannywood da suka hada da Farfesa Umar Farouk Jibril, Dakta Ahmad Muhammad Sarari, Alhaji Bashir Nayaya.

Kara karanta wannan

Soyayya Ruwan Zuma: Kalaman Soyayyar Da Matar Osinbajo Tayi Masa a Cikarsu Shekaru 33 da Aure

Sai kuma Nasir B. Muhammad, Mika’il Isa Bin Hassan (Gidigo), Tijjani Ahmad (Continuity), Amin M. Auwal, Bello Minna, da Murtada Arewa24.

Jaruma Halima Atete Ta Angwance Da Hadadden Angonta

Mun kawo a baya cewa shahararriyar jarumar Kannywood, Halima Atete ta shiga daga ciki a ranar Asabar, 26 ga watan Nuwamba.

Tun a ranar Laraba, 23 ga watan Nuwamba ne aka fara shagulgulan bikin inda aka yi wani dan kwarya-kwaryan liyafa kuma abokan sana'arta sun mata kara sosai.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng