2023: Rahama Sadau da Mansurah Isah Sun Yi Musayar Yawu Kan Tawagar Kamfen Tinubu

2023: Rahama Sadau da Mansurah Isah Sun Yi Musayar Yawu Kan Tawagar Kamfen Tinubu

  • Jerin sunayen tawagar yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na APC ɓangaren mata da aka fitar ya ta da yamutsi a Kannywood
  • Rahama Sadau ta nesanta kanta da lamarin wanda aka hangi hotonta, sai dai Mansurah Isah ta maida mata da martani
  • A ranar Asabar da ta gabata, ɗiyar Marigayi MKO Abiola kuma jigo a APC ta fitar da tawagar matan karkashin Aisha Buhari

Tawagar mata ta yakin neman zaɓen ɗan takarar shugaban ƙasa a inuwar APC, Bola Tinubu, da aka fitar ranar Asabar ta bar baya da ƙura a masana'antar shirya fina-finai.

A daftarin mai ƙunshe da shafuka 70, an ga sunayen jaruman Kannywood da Nollywood aƙalla 33 da suka samu shiga jirgin kamfen APC na mata.

Mansurah Isah da Rahama Sadau.
2023: Rahama Sadau da Mansurah Isah Sun Yi Musayar Yawu Kan Tawagar Kamfen Tinubu Hoto: Mansurah Isah, Rahama Sadau
Asali: Instagram

Jaruma Rahama Sadau na ɗaya daga cikin waɗanda sunansu ya shiga tawagar, sai dai da take martani kan lamarin a shafinta na Instagram, Jarumar ta nesanta kanta daga shiga tawagar, inda ta yi ikirarin cewa, "Ƙarya ce mai girma."

Kara karanta wannan

Fitacciyar Jarumar Kannywood, Rahama Sadau, Ta Maida Zazzafan Martani Kan Sa Sunanta a Kamfen Tinubu

A rubutun da ta yi, Sadau tace, "Wannan ƙarya ce babba, ba ni da masaniya kan lamarin, ban san yadda sunana ya kutsa ya shiga jerin sunayen ba. Bani da alaƙa da batun ta ko ina."

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Mansurah Isah ta maida martani

Da take martani kan kalaman Rahama Sadau a shafinta na Instagram ranar Lahadi, Mansurah Isah, ɗaya daga cikin jaruman da sunansu ya shiga, tace sunan dake ciki Rahama MK ne ba Sadau ba.

A rubutun, Mansurah Isah tace:

"Rahama, sunan da kika gani a jerin ba naki bane tun farko, sunan Rahama MK ne amma tun da ke kaɗai suka sani mai suna Rahama daga Kannywood, sai suka ɗauka kece, karki damu ba ke bace."

A nata ɓangaren, Rahma Sadau ta maida martani da cewa na sama da Mansurah Isah sun kira sun bata hakuri a keɓance.

Kara karanta wannan

Shugaba Buhari Zai Karrama Gwamna Zulum Da Wata Lambar Girma Ta Ƙasa

Sadau ta rubuta cewa, "Mansura Isah, ina baki shawara ki bar abun nan ya wuce saboda na sama da ke sun kira a keɓance sun nemi afuwa kan kuskuren da aka yi da gangan. Ba bukatar ki ari bakin wani ki ci masa albasa."

A wani labarin kuma mun tattara muku jerin sunayen matan Kannywood da suka shiga tawagar kamfen APC ta mata

Jam’iyya mai mulki a Nijeriya ta APC , ta saki jerin sunayen mambobin yakin neman zaben shugaban kasa na sashen Mata a ranar Asabar.

Wasu jaruman wasan kwaikwayon Kannywood kimanin 13 sun samu shiga jerin mambobin kwamitin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel