Bayan Shekaru 3 Da Aure Ba Tare Da Sun Ga Juna Ba, Yar Najeriya Ta Hadu Da Baturen Mijinta A Amurka

Bayan Shekaru 3 Da Aure Ba Tare Da Sun Ga Juna Ba, Yar Najeriya Ta Hadu Da Baturen Mijinta A Amurka

  • Wata matashiyar yar Najeriya da ke rayuwar aure nesa da mijinta wanda yake Baturen Amurka ta samu damar komawa kusa da shi a karshe
  • A cikin wani bidiyo da ya yadu, kyakkyawar matar ta bayyana cewa sun shafe tsawon shekaru uku kafin su hadu ido da ido a matsayin mata da miji
  • A wani bidiyon kuma ta nuna cewa ta kwashi garar kayan abinci dangin su busasshen kifi zuwa Amurka

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Wata matashiya da ke soyayya da wani bature ta samu damar haduwa da shi shekaru uku bayan aurensu.

Kafin tafiyarta, matar ta yi cikakken bidiyo don nuna irin shirin da tayi kama daga gyaran jiki har zuwa na gashi.

Mata da miji
Bayan Shekaru 3 Da Aure Ba Tare Da Sun Ga Juna Ba, Yar Najeriya Ta Hadu Da Baturen Mijinta A Amurka Hoto: TikTok/@simplicity_presh
Asali: UGC

Ta yi guzirin kayan abinci na gida Najeriya

Ana gobe za ta koma Amurka, matar ta gyara gashinta tayi kitso yayin da take rera wakar Naira Marley na zuwansa Amurka na farko.

Kara karanta wannan

Zan Siya Gida Kwanan nan A Birnin Lagas: In ji Mai Sana’ar Kifi, Mutane Sun Karfafa Mata Guiwa

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Mutane da dama da suka yi martani kan bidiyon matar sun yaba mata. Ta yiwa bidiyon take da:

“Idan kana cikin soyayya mai tazara a tsakani kawai ka yarda da tsarin Allah baya taba gazawa.”

A wani bidiyo na daban, yar Najeriyar ta bayyana cewa daga cikin abubuwan da ta tafi da su Amurka harda busasshen kifi, agushi, ogbono da sauran kayan abinci.

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun yi martani

Cita ta ce:

"Toh dai ina mijin naki kuma me yasa kike tsaye a waje sannan baku yi bidiyo tare a gidansa ba."

Sarah Goodluck ta ce:

"Ina tayaki murna, zai zo kaina kwanan nan da iznin Yesu."

Clemzi Clement ya ce:

"Na so wannan. Na taya ki murna faaa."

Shakys12 ta ce:

"Mun kai shekara 1 amma har na gaji da jira, kin cancanci haka yar'uwa."

Kara karanta wannan

Bacin rana: Wani ya yi aikin dana sani, ya kashe masoyiyarsa saboda katin ATM

Matarka Ce? Bidiyon Mai Hoto Da Ya Kamo Wata Amarya Ta Baya Ya Haddasa Cece-kuce

A wani labarin, wani mai daukar hoto ya sha caccaka daga jama’a sakamakon wani abu da ya yiwa wata amarya wanda bai kamata ba a yayin daukar hotunan aurensu.

Wasu sabbin ma’aurata ne suka dauko hayar mai hoton domin ya zo ya dauki hotunan shagalin bikin nasu.

Sai dai kuma, a yayin daukar hoton, mai hoton ya aikata wani abu da sam bai yiwa angon dadi ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel