Bidiyo: Matashin Dake Kaunar Jaruma Maryam Yahaya, Yake Fatan su Mutu Rana Daya

Bidiyo: Matashin Dake Kaunar Jaruma Maryam Yahaya, Yake Fatan su Mutu Rana Daya

  • Bidiyon wani matashi yana nuna tsabar kaunar da yake yi wa jaruma Maryam Yahaya ya bayyana kuma ya ba mutane mamaki
  • A bidiyon, matashin yace yana matukar kaunarta kuma yana fatan Allah ya dauki ransa a duk lokacin da zai dauki rayuwar jarumar
  • A cewar, ba yana nufin ya ta kasance a karkashin inuwarsa ba, kawai ta kasance a raye domin idan babu Maryam, toh shima babu shi

Bidiyon wani matashi wanda ke bayyana zunzurutun kaunarsa ga jarumar fina-finan Kannywood, Maryam Yahaya, ya bai wa jama'a mamaki.

A bidiyon da @kannywoodcelebrities.ng suka wallafa a Instagram, an ga matashin yana bayyana tsantsar kaunarsa ga matashiyar jarumar mai tashe.

Maryam Yahaya
Bidiyo: Matashin Dake Kaunar Jaruma Maryam Yahaya, Yake Fatan su Mutu Rana Daya. Hoto daga @kannywoodcelebritiesng
Asali: UGC

Me yake cewa a bidiyon?

Matashin da har a yanzu ba a gano sunan shi ba, yace ba zai iya rayuwa babu jaruma Maryam Yahaya a karkashin inuwar sa ba.

Kara karanta wannan

Mafi tsufa a raye: An gano wani tsoho dan Najeriya mai shekaru 126 a raye kuma da karfinsa

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Duk a cikin bidiyon, ya bayyana fatansa na cewa Allah ya dauki ransa a duk ranar da zai dauki rayuwar Maryam Yahaya.

A yayin bayyana sirrin zuciyarsa, matashin yace:

"Hakika, ba zan iya rayuwa babu Maryam Yahaya ba, ba ina nufin ta rayu a karkashin inuwata ba.
"Ba zan iya rayuwa ba muddin ba na jin motsinta. Ko da a birnin Kiev take. Shiyasa nake addu'a, duk ranar da Allah zai dauki ran Maryam Yahaya, toh ya dauka tare da nawa ran saboda in har babu Maryam, toh babu ni.

Bidiyoyi da hotunan bikin zagayowar ranar haihuwar jaruma Maryam Yahaya a Dubai

A wani labari na daban, Allah mai iko, a shekarar da ta gabata jaruma Maryam Yahaya tayi shagalin zagayowar ranar haihuwarta a gadon asibiti inda take kwance magashiyyan, amma wannan shekarar ta yi shi a Dubai.

Kara karanta wannan

Jarumi Ali Nuhu Ya Bayyana Hotunan Matashin Ɗansa Dake Kwallo a Ingila, Ya Birge Jama'a

Al'adar jarumar ce a kowacce shekara, tana gayyato kawaye da abokan arziki domin su taya ta shagalin bikin zagayowar ranar haihuwarta, inda ake shiga ta kece raini tare da kade-kade da raye-raye duk don taya ta murna.

Shagalin bikin ranar zagayowar haihuwar jarumar ya saba daukar hankali a kowacce shekara. Sai dai a cikin hukuncin Allah, shekarar da ta gabata Allah ya jarabceta da ciwo wanda ya kai ta kwanciya asibiti har ba a samu damar yin wannan shagalin ba da aka saba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel