Bidiyoyi da hotunan bikin zagayowar ranar haihuwar jaruma Maryam Yahaya a Dubai

Bidiyoyi da hotunan bikin zagayowar ranar haihuwar jaruma Maryam Yahaya a Dubai

  • Hotuna da bidiyoyin shagalin bikin zagayowar ranar haihuwar fitacciyar jaruma Maryam Yahaya a Dubai sun birge masoyanta
  • A kyawawan hotunan da bidiyon, an ga jaruma ta yi shiga cike da aji tare da gayu inda ta karkace da kek cike da murna da farin ciki
  • Kyawawan hotuna da bidiyoyin da ta wallafa a shafinta na Instagram alamu ne na cewa jaruma ta dawo tsaf cikin hayyacinta bayan doguwar jinyar

Allah mai iko, a shekarar da ta gabata jaruma Maryam Yahaya tayi shagalin zagayowar ranar haihuwarta a gadon asibiti inda take kwance magashiyyan, amma wannan shekarar ta yi shi a Dubai.

Al'adar jarumar ce a kowacce shekara, tana gayyato kawaye da abokan arziki domin su taya ta shagalin bikin zagayowar ranar haihuwarta, inda ake shiga ta kece raini tare da kade-kade da raye-raye duk don taya ta murna.

Kara karanta wannan

Bayyanar bidiyo da hotuna motar jaruma Nafisa Abdullahi ta N30m ta dauka hankali

Maryam Yahaya
Bidiyoyi da hotunan bikin zagayowar ranar haihuwar jaruma Maryam Yahaya a Dubai. Hotuna daga @real_Maryamyahaya
Asali: Instagram

Shagalin bikin ranar zagayowar haihuwar jarumar ya saba daukar hankali a kowacce shekara.

Sai dai a cikin hukuncin Allah, shekarar da ta gabata Allah ya jarabceta da ciwo wanda ya kai ta kwanciya asibiti har ba a samu damar yin wannan shagalin ba da aka saba.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Duk da rashin lafiyarta a shekarar da ta gabata, ta dauko tsofaffin hotunanta inda ta wallafasu a shafinta na Instagram yayin da masoyanta suka dinga taya ta murna tare da yi mata fatan samun lafiya.

Bayan watannin da ta dauka tana jinya, Maryam Yahaya ta warke kuma ta samu lafiya, sai dai tun kafin ta mayar da jkinta, ta cigaba da raye-raye tare da daukan hotunan da ta saba, lamarin da ya janyo mata cece-kuce.

Bayan wani lokaci, jarumar ta dawo ras inda kuma ta koma harkar fim dinta gadan-gadan har Ubangidanta Ali Nuhu ya samar mata da gurbi a sabon shirinsa mai dogon zango mai suna Alaka.

Kara karanta wannan

Tashin hankali: Yadda matar aure tayi mutuwar farat daya a ƙuryar ɗakin kishiyarta

A wannan shekarar kuwa, Maryam Yahaya ta zo da wani sabon salo wanda ba a saba gani ba inda tayi shagalin bikin ranar haihuwarta a birnin Dubai dake Hadaddaiyar Daular Larabawa, UAE.

Hotuna da bidiyo: Alkawari ya cika, an daura auren 'Yaradua da Yacine kan sadaki sisin gwal 24

A wani labari na daban, 'dan tsohon shugaban kasar Najeriya, Umaru Musa Yar'adua, Shehu Yar'adua ya yi wuff da Yacine Muhammad Sheriff a Maiduguri dake jihar Borno a yau Asabar, 23 ga watan Yulin 2022.

An daura auren a gidan Sheriff wanda yake kusa da barikin Giwa kuma ya samu halartar shugaban kasa Muhammadu Buhari wanda ya samu wakilci daga ministan sufurin jiragen sama, Hadi Sirika, Gwamna Babagana Umara Zulum da takwarorinsa na jihar Kebbi da Jigawa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel