‘Yan Bindiga Sun Sace ‘Yan Wasan Kwaikwayo, Sun Bukaci a Fanshe su da Daloli

‘Yan Bindiga Sun Sace ‘Yan Wasan Kwaikwayo, Sun Bukaci a Fanshe su da Daloli

  • Kungiyar Nollywood na alhinin wasu ‘Ya ‘yanta masu shirya wasan kwaikwayo da aka dauke
  • Ana zargin ‘Yan bindiga sun dauke ‘yan wasan kwaikwayon a wani kauye a kusa da garin Enugu
  • ‘Yan bindigan sun bukaci a biya $100, 000 kafin a sake ganin Cynthia Okereke da Clemson Cornell

Enugu - A ranar Asabar, 30 ga watan Yuli 2022, jaridar The Nation ta kawo rahoto cewa an sace wasu ‘yan wasan kwaikwayo na Nollywood a Najeriya.

‘Yan bindiga sun yi awon gaba da Cynthia Okereke da Clemson Cornell bayan sun baro wajen shirya wasan kwaikwayo a garin Ozalla da ke jihar Enugu.

Mai magana da yawun bakin kungiyar ‘yan wasan kwaikwayon Najeriya na AGN, Monalisa Chinda, ta tabbatar da wannan labarin a shafin Instagram.

Monalisa Chinda take cewa an nemi wadannan tsofaffin ‘yan wasa kuma abokan aikinta bayan sun baro garin Ozalla inda ake shirin wasan kwaikwayo.

Ta tabbata inji Shugaban AGN

Rahoton yace shugaban kungiyar AGN na kasar nan, Emeka Rollas ya yi kira ga ‘yan wasa da su daina yin nisa da birane domin shirya wasannin kwaikwayo.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A jawabin da Rollas ya fitar, ya yi kira ga abokan aikinsa da su guji abin da zai jefa su a hadari.

‘Yan Wasan Kwaikwayo
Cynthia Okereke da Clemson Cornell Hoto: www.premiumtimesng.com
Asali: UGC

“Mutane biyu na kungiyar ‘Yan wasan Najeriya, Cynthia Okereke da Clemson Cornel (watau Agbogidi) sun bace.
‘Yanuwansu sun tabbatar da ba su dawo daga wajen shirya wasan kwaikwayo a garin Ozalla, da ke jihar Enugu ba.”
“Ana zargin an yi garkuwa da wadannan mutane biyu ne, kuma hakan ya kara jefa tsoro a kan lafiyar ‘yan wasan fim.”

Za a biya Dalolin kudi

Daga baya labari ya fito daga Premium Times cewa wadanda suka yi garkuwa da ‘yan wasan sun bukaci a biya su kudin fansa $100, 000 na Dalar Amurka.

Shugaban AGN, Emeka Rollas ya tabbatar da cewa an bukaci a biya $100, 000. Rollas ya roki Ubangiji ya kawo agaji, sannan yace suna tuntubar jami’an tsaro.

An yi canji a gidan soja

A ranar Juma'ar nan da ta wuce ne aka ji labari an samu wasu ‘yan sauye-sauye da aka yi a gidan sojan kasa wanda ya taba manyan jami’an kasar nan.

Shugaban hafsun sojojin kasa, Janar Farouk Yahaya ya nada wasu sababbin GOC da kuma shugabannin makarantu da rundunonin sojojin kasan Najeriya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel