Matsalar Tsaro ta Ta’azzara, Shugaban Sojoji ya girgiza gidan Soja, an Taba Janarori

Matsalar Tsaro ta Ta’azzara, Shugaban Sojoji ya girgiza gidan Soja, an Taba Janarori

  • An samu wasu ‘yan sauye-sauye da aka yi a gidan sojan kasa wanda ya taba manyan jami’ai
  • Shugaban hafsun sojojin kasa ya nada wasu sababbin GOC da kuma shugabannin makarantu
  • Sauyin ya shafi wasu Manjo Janar da dama da tsirarrun sojojin da ke matsayin Birgediya Janar

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Abuja - Rundunar sojojin kasa na Najeriya ta bada sanarwar yin wasu sauye-sauye a gidan soja da nufin a inganta yadda jami’an tsaro suke gudanar da aiki.

Legit.ng Hausa ta samu labarin wannan sanarwa da ta fito daga shafin Darektan harkokin yada labarai na sojojin kasa, watau Janar Onyema Nwachukwu.

Birgediya-Janar Oyema Nwachukwu yace Shugaban hafsun sojojin kasa, Laftana-Janar Faruk Yahaya ya amince da wadannan canjin wurin aiki da aka yi.

Wadanda sauyin ya shafa sun hada da manyan jami’an sojojin da ke Hedikwata, jami’an GOC da shugabannin makarantun horas da soji da sauran jagorori.

Kara karanta wannan

Martanin gaggawa: Sojoji sun sheke tsageru 30 da suka kai kan jami'an fadar Buhari

An taba manyan Janarori

Manjo Janar UT Musa zai bar wurin aikinsa, zai zama sabon GOC na dakarun 82 Div. Shi ma Manjo Janar TA Lagbaja zai karbi rikon dakarun I Div a Kaduna.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Manjo Janar OC Ajunwa ya zama GOC na Hedikwatar sojoji na 81 Div. An kuma dauke Manjo Janar AS Chinade daga makarantar nan da ake horas da kurata.

Sojoji
Manyan Jami'an Sojoji Hoto: @NigerianArmy
Asali: Facebook

Haka zalika Daily Trust ta rahoto cewa a Hedikwatar sojojin da ke Abuja, Manjo Janar OW Ali zai koma bangaren gudanar da aikin sojoji, ya bar inda yake.

Daga yanzu Manjo Janar AA Adesope ya zama shugaban sashen kasafin kudi, tattalin arziki da akanta, Manjo Janar US Mohammed ya koma sashen bincike.

Sauyin ya shafi irinsu Manjo Janar S. Mohammed, Manjo Janar, JA Ataguba. Sai Manjo Janar PB Fakrogha, Manjo Janar MO Enendu da Manjo Janar AE Attu.

Kara karanta wannan

Dakarun Sojoji Sun Kashe Yanta'adda 30 A Abuja - Hedkwatan Sojoji

Rahoton yace an canzawa Manjo Janar BE Onyeuko wurin aiki, ya zama darektan sayen kaya.

Wasu canji da za a gani

Sababbin shugabannin dakaru sun kunshi Manjo Janar AM Alabi, Manjo Janar A Mohammed, Manjo Janar E Akerejola, da kuma Manjo Janar AA Fayemiwo.

Manjo Janar PI Eze, Manjo Janar AA Adeyinka da Manjo Janar PP Malla za su kula da makarantu.

Wadanda suke matsayin Birgediya Janar da aka ba mukamai a gidan sojan su ne; DH Ndahi, FS Etim, EA Orakwe, JO Are. An yi kira gare su da suka kara kwazo.

An taba asusun ECA

An wayi gari da labarin cewa Gwamnatin Tarayya ta dauki Dala Biliyan 1 daga asusun kudin rarar mai. Ana adana wannan kudi ne saboda bacin-rana.

Ministar kudi, Zainab Ahmed ta kare zargin da ake yi wa Gwamnatin Muhammadu Buhari, tace an cire kudin ne saboda ayi maganin matsalar tsaro a Najeriya.

Kara karanta wannan

An Yi Jana’izar Daya Daga Cikin Sojojin Da Yan Bindiga Suka Kashe A Abuja, Hotuna

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng