Bidiyon tsofaffin jaruman kanywood a wajen shagalin sunan tsohuwar jaruma Fati Ladan

Bidiyon tsofaffin jaruman kanywood a wajen shagalin sunan tsohuwar jaruma Fati Ladan

  • Allah ya azurta tsohuwar jarumar masana'antar fina-finan Hausa, Fati Ladan, da samu karuwar diya mace
  • An yi gagarumin bikin suna wanda ya samu halartan manyan tsoffin jarumar irin su Sadiya Gyale, Fati KK, Fauziyya Mai Kyau da Wasila
  • Tsoffin abokan sana'ar tata sun yi mata kara matuka inda suka sha rawa suka girgije tare da yi mata liki

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Tsohuwar jarumar masa’antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood, Fati Ladan, ta samu karuwar diya mace a gidan aurenta.

Tuni dai aka yi shagalin suna na gani na fada, taron da ya samu halartan manyan tsoffin jaruman masana’antar da suka yi mata kara.

Shagalin sunan jaruma Fati Ladan
Bidiyon tsofafin jaruman kanywood a wajen shagalin sunan tsohuwar jaruma Fati Ladan Hoto: Instagram/ mufeeda_rasheed1/FimMagazine
Asali: UGC

A cikin wani bidiyo da shafin mufeeda_rasheed1 ta wallafa a Instagram an gano tsoffin jarumar kamar su Sadiya Gyale, Fauziyya Mai kyau, Fati KK, Wasila da sauransu suna taya mai jego rawa tare da yi mata likin kudi.

Kara karanta wannan

Kaduna: 'Yan bindiga sun sako shugaban kauye don ya tara N100m ya karbi mutanensa 30

Hakazalika, an gano angon karni wato mijin Fati Ladan wanda ya kasance shugaban kungiyar matasan arewa, Yerima Shettima a wajen shagalin inda yake yiwa matar tasa liki.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mai jego Fati Ladan ta yi shigarta ta kamala tamkar sabuwar amarya yayin da fuskarta ke dauke da farin ciki da annashuwa.

Ga bidiyon shagalin a kasa:

Aure ya kullu: Bidiyoyi da hotuna daga shagalin bikin Lilin Baba da kyakkyawar amaryarsa Ummi Rahab

A wani labari na daban, alkawarin Allah ya cika a tsakanin jarumi kuma fitaccen mawaki a masana'antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood, Shu'aibu Ahmed Idris, wanda aka fi sani da Lilin Baba da kyakkyawar amaryarsa, jaruma Ummi Rahab.

A ranar Asabar 18 ga watan Yuni, ne dubban jama’a suka shaida daurin auren manyan jaruman guda biyu.

An yi shagulgula da dama domin raya wannan rana inda amarya Ummi ta fito shar da ita saboda tsabar kyawu da haduwa.

Kara karanta wannan

Likafa ta ci gaba: Matan marigayi Alaafin na Oyo sun baje kolin sabbin gidajen da suka mallaka

Asali: Legit.ng

Online view pixel