Kannywood: Ina fatan rabuwa da kowa lafiya kuma na yi Aure, Maryam Yahaya

Kannywood: Ina fatan rabuwa da kowa lafiya kuma na yi Aure, Maryam Yahaya

  • Maryam Yahaya ta bayyana cewa babban burinta a rayuwa shi ne ta rabu da kowa lahiya kuma ta samu miji ta yi aure
  • Jarumar wacce ta sha fama da rashin lafiya a kwanakin baya, ta ce rashin lafiya jarabawa ce kuma zata iya faɗawa kan kowa
  • Maryam na ɗaya daga cikin jarumai mata a Kannywood da tauraruwarsu ke hasakakawa tun bayan shiga masana'antar Fim

Kano - Jaruma a masana'antar Kannywood, Maryam Yahaya ta bayyana cewa babban fatanta a rayuwa shine ta rabu da kowa lafiya kuma ta samu miji ta yi aure.

Maryam ta yi wannan magana ne yayin wata fira da BBC Hausa, inda ta ce ba wai an daina ganinta a Kannywood bane yanayi ne kawai kuma ya kan faru da kowa.

Kara karanta wannan

Ku cire ni daga bakinku: Maishadda bai yaudare ni ba, babu komai tsakaninmu – Aisha Humaira

Maryam Yahaya
Kannywood: Ina fatan rabuwa da kowa lafiya a kuma na yi Aure, Maryam Yahaya Hoto: @real_maryamyahaya
Asali: Instagram

Jarumar na ɗaya daga cikin jarumai mata a masana'antar shirya fina-finan Hausa masu ƙarancin shekaru kuma tauraruwarta na haskawa.

Sai dai a yan kwanakin nan, Maryam ta daina fitowa a fina-finan Kannywood, amma a cewarta ba kamar yadda ake tunani bane, ba ta ɗage kafa ba.

Ina son nima na yi aure - Maryam

Da aka tambayeta meye fatan da take da shi, Maryam ta bayyana cewa tana son watarana ita ma ta yi aure bayan ta rabu da abokan aikinta lafiya.

A kalamanta jarumar ta ce:

"Fatana mu rabu lafiya da kowa nima naje na yi aure, kuma ni ban ɗage kafa daga Kannywood ba, rashin lafiya ce kuma ta na kan kowa. Amma ni yanzun nagode Allah na samu lafiya."

Haka nan kuma, Maryam ta ce babban abun da ke ɗaga mata hankali a rayuwa shi ne ta tuna da mutuwa, wataran zata mutu, wannan abun na ɗaga mata hankali.

Kara karanta wannan

Idan PDP bata ci zaben 2023 ba zata iya mutuwa gaba daya, Atiku

Fim ɗin Mansoor, wanda Sarki Ali Nuhu ya bada Umarni, shi ne Fim na farko da jarumar ta fara fitowa, kuma ta haɗu da Mawaki kuma Jarumi Umar M Sharif a cikin shirin.

A wani labarin na daban kuma Kayan Masarufi uku da suka yi tashin gwaurin zabi a babbar kasuwar Najeriya

Farashin kayayyakin masarufi a kasuwar jihar Legas na sama suna ƙasa saboda kalubalen tsaro, canjin kudi da sauran su.

Karancin Man fetur ba ya cikin abubuwan da suka jawo tashin kayan, sai dai yan kasuwa sun ce rashin dai-daiton tattalin arziki ne babban dalili.

Asali: Legit.ng

Online view pixel