Zargin almundahana: Jarumi Sadiq Sani Sadiq ya bayyana gaskiyar lamari kan tuhumar da ake masa
- Fitaccen jarumin Kannywood, Sadiq Sani Sadiq, ya fayyace biri har wutsiya kan batun kai shi kotu bisa zargin aikata almundahana
- Sadiq ya ce shi bai da labarin an kai shi kotu domin bai samu sammaci ba kuma babu wanda ya kira shi a waya ya sanar da shi
- Ya ce batun zargin da ake yi masa kuma, aikine ya hada shi da wani furodusa, inda suka samu sabani kan aikin amma shi bai damfari kowa ba
Shahararren jarumin Kannywood, Sadiq Sani Sadiq ya magantu a kan rahotannin cewa wata kotu ta bayar da umurnin kamo mata shi kan zargin almundahana.
Jarumin ya ce shi bai da labarin an kai shi kara kotu domin tun farko babu wanda ya aika masa sammaci, har sai da ya ji wai daga bakin wani dan jarida.
A wata hira da ya yi da Muryar Amurka, an jiyo jarumin yana cewa:
"Maganar kaini kotu, ban ma san an kaini kotu ba sai daga jiya da wani dan jarida ya kira ni yake cewa an kawo labarai su buga a gidan radiyonsu na Freedom, cewa wani furodusa ya bani kudin aiki kuma ban yi aikin ba. Toh daga nan ne nake ji an kaini kotu wai kotun ma har ta bayar da umurni wai a kamo ni."
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Game da batun cewa ko sammacin da kotun ta aika masa bai shiga hannunsa ba, Sadiq ya ce:
"Eh bai shiga hannuna ba kuma babu wanda ya kirani a waya ya ce mun kotu tana nema na, ko kuma aka yi mun tes ko aka kawo sammaci gidana babu daya da aka yi mun daga ciki. Kawai dai na ji sammaci wai a wajen wani dan jarida."
Da aka tambaye shi kan ko da gaske furodusan ya bashi kudin aikin, Sadiq ya kara da cewa:
"Eh toh shi wanda yake ikirarin cewa ya kai ni kotun wallahi yanzu haka idan na gan shi ma ni ba zan iya gane shi ba, ban ma san shi ba.
"Abun da na sani kawai shine shekarun baya chan kamar shekaru biyar zuwa hudu da suka shige, akwai Abdulaziz Dan samall, wani daga cikin furodusa dinmu sun zo sun kawo mun aiki da shi da wani yaro ana ce masa Maharass da wani yaro ina jin dan Azare ne kuma ina ga shine asalin mai aikin.
"Don haka sai muka yi magana da su, suka bani wani kaso na kudin aikin a kan idan an gama za su cika mun sauran kudin aikin, na saka masu ranar aiki aka zo ranar da za a yi aikin sai shi Abdulaziz ya kirani ya ce mun wannan aikin ba zai yiwu ba saboda sun samu matsala, furodusan yana da matsala ta kudi aikin ba zai yiwu ba.
"Sai nace to ba damuwa muka sake saka wani rana na aikin, bayan saka ranar, a ranar da aka zo za a yi aikin sai basu kirani ba sai nine da na fito daga gida sai na kira Abdulaziz din sai nace ya naji ku shiru me yake faruwa, sai yace mun wallahi dai har yanzun aikin nan ba zai yiwu ba dole sai an sake dagawa.
"Kun ga dagawa sau biyu kenan, toh daga nan sai raina ya baci nace ya mutanen nan za su hana ni na karbi wasu ayyukan sannan su aikinsu da zan yi na karbi sauran kudina ba a yi ba, kenan sun jawo mun asara na lokaci biyu.
"Sai suka saka rana da kansu, sai aka zo ranar da za a yi aikin ni kuma bana nan ina da wasu harkokin, ashe bayan hakan da basu same ni ba sai suka jawo wani jarumin suka bashi aikin aka yi aiki. Sai daga baya sai aka kirani wai na dawo da kudin aikin tunda ban samu fitowa na yi ba.
"Sai nace a ina aka taba yin hakan ku bani kudi sannan ku ce na dawo da shi, na saka rana sau biyu bamu samu mun yi aikin ba, ku saka sau daya danni ban samu zuwa ba kuce kun cireni sannan na dawo da kudi. Nace ba za a yi haka ba sai dai idan wani aikin kun kawo sai mu wanye.
"Sai shi furodusan yace kudinsa yake so ni kuma nace ba za a yi haka ba, nace a ka'ida ma kamata yayi ka biyani kudin asarar da ka janyo mun."
Sadiq ya ci gaba da cewa a shekarar bara sai ya dauko masa dan sanda inda bayan sun koro zance sai shima yaki goyon bayan furodusan inda yace su je su sasanta. Ana hakan ne ya kuma je ya sanar da Alhassan kwalle shugabansu na Kano.
Jarumin ya ce bayan Alhassan ya sa baki sai suka yi zai biya shi rabin kudin amma zai fara da bashi N20,000 inda sauran N30,000 din zai biyo baya. Yace bayan nan bai sake jinsa ba sai yanzu da ya ji an maka shi kotu.
Game da matakin da zai dauka, Sadiq ya ce a yanzu dai ya ce ya kira lauyansa don ya bi shari'ar sannan kuma ya bi masa hakkinsa na bata masa suna da yayi.
Kotu ta yi umarnin damko jarumi Sadiq Sani Sadiq kan zargin almundahana
A baya mun ji cewa wata kotu mai zama a jihar Kano ta bai wa dan sandan kotu umarnin cafko mata fitaccen jarumin masana'antar Kannywood, Sadiq Sani Sadiq.
Alkali Sagir Adamu na kotun shari'ar Musulunci mai zama a Hotoro masallaci ne ya bayar da umarnin damke jarumin saboda bijirewa umarnin kotun, Freedom Radio ta ruwaito.
Tun farko dai, wani mashiryin fina-finai mai suna Aliyu Adamu Hanas ya kai karar jarumin saboda ya bashi kafin alkalami na kudi domin za su fara aikin shirya wani fim, sai dai jarumin ya ki yin aikin.
Asali: Legit.ng