Najeriya da Morocco Sun Tattago Babban Aiki, za a Kashe kusan Naira Tiriliyan 34

Najeriya da Morocco Sun Tattago Babban Aiki, za a Kashe kusan Naira Tiriliyan 34

  • Najeriya da Morocco za su rattaba hannu kan yarjejeniyar IGA a wannan shekara ta 2026 domin aikin bututun iskar gas na dala biliyan 25
  • Aikin zai haɗa ƙasashe 13 na Afirka, inda zai zama gada ta makamashi tsakanin nahiyar Afirka da kasuwannin Turai
  • Za a kafa hukumar kula da aikin a Najeriya, yayin da kamfanin aiwatar da aikin zai kasance a Morocco ƙarƙashin haɗin gwiwar NNPCL da ONHYM

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Morocco – Gwamnatocin Najeriya da Morocco sun shirya tsaf domin sanya hannu kan yarjejeniyar haɗin gwiwa (IGA) kan aikin gina bututun iskar gas na Afirka (AAGP).

Za a rattaba hannu kan wannan yarjejeniyar aikin, wanda zai lakume kimanin dala biliyan 25, kusan Naira tiriliyan 34, a cikin wannan shekara ta 2026.

Kara karanta wannan

Duk da tsagaita wuta, Trump ya sake yin babbar barazana ga Amurka

Najeriya da Morocco sun za su kulla yarjejeniyar aikin bututun gas na dala biliyan 25
Tsohon shugaban NNPCL, Mele Kyari da shugabar hukumar ma'adanai ta Morocco, Amina Benkhadra suna sanya hannu kan aikin bututun gas. Hoto: Jalal Morchidi/Anadolu Agency via Getty Images
Source: Getty Images

Najeriya da Morocco za su kulla yarjejeniya

Shugabar hukumar ma'adinai ta kasar Morocco, Amina Benkhadra, ce ta bayyana hakan a wata tattaunawa da kamfanin dillancin labarai na Reuters.

Wannan aiki, wanda aka amince da shi kusan shekaru goma da suka gabata, an tsara shi ne domin ya zama wata gadar makamashi da za ta hada Afirka da Turai.

Bututun zai iya ɗaukar iskar gas kusan cubic mita biliyan 30, inda za a yi amfani da biliyan 15 wajen samar da wutar lantarki da bunƙasa masana'antu a Morocco da sauran ƙasashen yammacin Afirka.

Yadda aka tsara gudanar da aikin $25bn

Bayan sanya hannu kan yarjejeniyar IGA, za a kafa wata babbar hukuma a Najeriya wadda za ta haɗa wakilan ministoci daga dukkan ƙasashe 13 da bututun zai ratsa. Wannan hukuma za ta kula da tsare-tsare da dokokin tafiyar da aikin.

Haka kuma, za a kafa wani babban kamfani a Morocco wanda zai haɗa hukumar ONHYM ta Morocco da kamfanin NNPCL na Najeriya domin kula da fannin kuɗi da gine-gine.

Kara karanta wannan

Muhimman abubuwa 5 da Amurka da Iran suka gaza warwarewa a zaman sulhu a Islamabad

Bututun zai bi ta cikin teku da kuma tsandauri, inda kashi na farko zai haɗa Morocco da filayen iskar gas na Mauritania da Senegal.

Kashi na biyu kuma zai haɗa ƙasar Ghana da Cote d'Ivoire, kafin kashi na ƙarshe ya isa filayen iskar gas na Najeriya.

Benkhadra ta bayyana cewa ba a dogara ga babban jarin kuɗi na lokaci ɗaya ba; an tsara kowane kashi na aikin ne domin ya iya tsayuwa da kansa.

Za a gina bututun gas da zai ratsa kasashe 13 na Afrika.
Shugabar hukumar ma'adan Morocco, Amina Benkhadra tana jawabi a taron kulla yarjejeniyar aikin gina bututun gas da Najeriya. Hoto: Jalal Morchidi/Anadolu Agency via Getty Images
Source: Getty Images

Tasirin aikin ga tattalin arzikin Afrika da Turai

Wannan babban aiki na dala biliyan 25 yana samun goyon bayan ƙungiyar ECOWAS, kuma an riga an kammala binciken yiwuwar aiwatar da shi da kuma tsare-tsaren injiniyanci.

Amina Benkhadra ta bayyana cewa:

"Aikin yana jan hankalin masu saka jari saboda girmansa, tsarin sa na kashi kashi, da kuma muhimmancinsa ga tsaron makamashi na duniya."

Ko da yake har yanzu ba a kammala samun dukkan kuɗaɗen da ake buƙata ba, kamfanin da za a kafa shi ne zai jagoranci nemo jari ta hanyar bashi da kuma hannun jari.

Kara karanta wannan

An kama ɗan shekara 15 da ake zargi da hannu a kashe Janar a harin Borno

Ana sa ran aikin zai bunƙasa tattalin arzikin yammacin Afirka ta hanyar samar da wutar lantarki mai rahusa da kuma sauƙaƙa hakar ma'adinai a yankin baki ɗaya.

Kasashe na neman gas din Najeriya

A wani labari, mun ruwaito cewa, NNPCL ya bayyana cewa yakin Gabas ta Tsakiya ya sanya kasashen duniya tururuwar neman iskar gas din Najeriya.

Najeriya tana kokarin fadada ayyukan iskar gas dinta domin cin gajiyar kusancin da take da shi da kasashen Turai da yankin Asiya.

Mataimakin shugaban NNPCL, Olalekan Ogunleye ya ce an raja'a kan gas din Najeriya saboda inganci da bukatarsa a halin yanzu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com