Babbar ribar da Najeriya ta samu a ziyarar da Buhari ya kai kasar Morocco
Gwamnatin Najeriya da takwararta na kasar Morocco sun rattafa hannaye kan wasu yarjejeniya tsakanin kasashen biyu da zasu habbaka tattalin arzikin kasashen biyu, wadanda suka kunshi cigaban iskar gas, zuba hannayen jari da kuma inganta harkar noma.
Legit.ng ta ruwaito fadar shugaban kasa ne ta sanar da wadanna riba kan riba da Najeriya zata sharba daga ziyarar da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kai ma shugaban kasar Morocci Sarki Muhammad na Shida.
KU KARANTA: Dakarun Sojin Najeriya sun yi ma masu garkuwa da mutane kisan kiyashi a Kaduna
Kaakakin shugaba Buhari, Garba Shehu ya bayyana cewa yarjejeniyar da shugaban NNPC ya sanya ma hannu tare da shugaban hukumar man fetir na kasar Morocco, Amina Benkhadra zai haifar da ginin bututun iskar gasa mai tsawon kilomita 5,660 daga Najeriya zuwa Morocco, wanda zai taikama wajen gurbatan yanayi, kare kwararowar Hamada da kuma samar da dubunnan ayyukan yi ga matasa.
Haka zalika, wani babban jami’I a gwamnatin Buhari, Ushe Orji da takwaransa na kasar Morocco, Mostafa Terrab sun rattafa hannu a wata yarjejeniya da zata samar da cigaba ga kamfanonin sarrafa taki na Najeriya, wajen iganta ayyukansu.
Bugu da kari, Ministan noma na Najeriya, Audu Ogbeh da na kasar Morocco, Aziz Akhannouch sun wakilci kasashen nasu biyu a kulla yarjejeniyar horas da jami’an noma na Najeriya da kasar Morocci za ta yi, wanda hakan zai inganta harkokin noma a Najeriya.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng