Za a gina layin mai daga Najeriya har Morocco
- Najeriya da Morocco sun shiga wata yarjejeniya
- Za a gina layin mai daga Najeriya zuwa Kasar Morocco
- Wannan na cikin abin da aka tattauna yayin da Shugabannin Kasashen biyu suka hadu
Najeriya da Morocco sun shiga wata yarejeniya, inda aka shirya cewa za a gina layin mai tsakanin Kasashen biyu. Wannan dai yana cikin tattaunawar da Shugabannin Kasashen suka yi a ganawar su.
Ministocin Kasashen wajen wadannan Jihohi sun ce ba karamar nasara za a samu wajen wannan yarjejeniyar ba. An bayyana cewa hakan zai kawo cigaba da kuma samun wutan lantarki a Kasashen biyu.
KU KARANTA: DSS ta saki na kusa da Buhari
Muddin aka samu wutar lantarki, za a samu karuwar Kamfani a Kasashen biyu. Haka kuma zai kawo cigaba matuka a Kasar Najeriya da Morocco. An dai yi kwanaki biyu ana ganawa tsakani Kasashen biyu.
A nan gida kuma, Kwamishinan Hukumar kula da masu gudun hijira, Hajiya Sadiya Umar Farouk ta raba kayayyakin abinci ga ‘yan gudun hijirar da ke Kasar Borno da kewaye. Shugaban Kasa Muhammadu Buhari yana kokarin ganin wadannan mutane sun koma gidajen su bayan rikicin Boko Haram ya afka da su
A biyo mu a shafin mu na Tuwita @naijcomhausa
https://youtu.be/wXmmTEAKDxo
Asali: Legit.ng