Yaki da Iran Ya Rikita Amurka, Minista na Neman Raba Hafsan Soja da Kujerarsa

Yaki da Iran Ya Rikita Amurka, Minista na Neman Raba Hafsan Soja da Kujerarsa

  • Ministan tsaron Amurka Pete Hegseth ya taso babban hafsan rundunar sojojin kasa, Janar Randy George ana tsaka da yaki da Iran
  • Rahotanni sun ce an bukaci George ya yi ritaya da wuri, wanda ke cikin jerin manyan jami’an soja da aka sallama tun bayan Hegseth ya hau mulki
  • Matakin na zuwa ne bayan an sallami manyan hafsoshin soja da dama, ciki har da shugabannin rundunar ruwa da sama

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Washington DC, US - Ministan tsaron Amurka Pete Hegseth ya bukaci babban hafsan rundunar sojin kasa ya yi murabus.

Hegseth ya tura wannan bukata ce ga Janar Randy George, ya sauka daga mukaminsa, kamar yadda Pentagon ta bayyana.

An bukaci hafsan sojojin Amurka ya yi murabus
Ministan tsaron Amurka, Pete Hegseth yayin jawabi a Washington. Hoto: @pete_hegseth.
Source: Twitter

Wani jami’in Pentagon da ya nemi a sakaya sunansa ya tabbatar da cewa an nemi George ya yi ritaya da wuri daga mukaminsa na shugaban rundunar sojin kasa, cewar Reuters.

Kara karanta wannan

Ana wata ga wata: Shugaban Amurka, Trump ya 'kori' Antoni Janar ana tsaka da yakin Iran

Yaushe hafsan sojojin Amurka ya fara aiki?

George ya fara rike mukamin ne tun watan Agustan 2023, kuma wannan mataki na zuwa ne a lokacin da Amurka ke cigaba da yakin da take yi da Iran.

Sallamar George na daga cikin jerin manyan hafsoshin soja fiye da 12 da aka cire ko suka yi murabus tun bayan Hegseth ya karbi kujerar minista a bara.

Rahoton farko kan wannan lamari ya fito ne daga CBS News, wanda ya bayyana yadda ake cigaba da sauye-sauye a manyan mukaman soja.

Janar George ya kammala karatu a makarantar horar da sojoji ta West Point, kuma ya yi aiki a yakin Gulf na farko da kuma hare-haren Iraq da Afghanistan.

Haka kuma, ya taba zama babban mataimakin soja ga tsohon ministan tsaro Lloyd Austin daga 2021 zuwa 2022 kafin ya samu karin girma a rundunar soji.

A watan Fabrairu na bara, George ya tsira daga farkon jerin sallame-sallamen da suka hada da manyan hafsoshin soja, ciki har da shugabannin rundunar ruwa da sama.

Kara karanta wannan

Trump ya gindaya sharudan tsagaita wuta, ya fadi rokon da Iran ta yi masa

An taso hafsan tsaron Amurka ya yi murabus
Shugaba Donald Trump na kasar Amurka. Hoto: @RealDonaldTrump.
Source: UGC

Hafsoshin soja da suka rike mukamin a baya

A wancan lokaci, shugaban Amurka, Donald Trump ya sallami shugaban hafsoshin tsaro Janar Charles “C.Q.” Brown tare da wasu manyan jami’an soja.

Tun daga lokacin, wasu manyan hafsoshi da dama sun yi murabus ko aka cire su daga mukamansu, ciki har da mataimakin George, Janar James Mingus.

An maye gurbin Mingus ne da Laftanar Janar Christopher LaNeve, wanda kafin hakan ya kasance babban mataimakin soja ga Hegseth bayan ya fito daga rundunar Eighth a Koriya ta Kudu.

Trump ya taba kimar Shugaba Macron da matarsa

A baya, kun ji cewa shugaba Donald Trump ya yi wa Emmanuel Macron da matarsa Brigitte Macron ba'a wanda suka tayar da kura a kasar Faransa.

Yan siyasa ciki har da masu adawa da Macron sun fito sun kare shi, suna cewa kalaman Trump rashin mutunci ne duk da bambancin ra’ayi a tsakaninsu.

Macron ya ce kalaman Trump ba su da kima kuma ba su dace ba, yayin da rikicin Iran ke gudana yana bukatar hankali ba zolaya ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.