Shugaba Saleh na Iraqi ya soki harin makamai masu linzami da Iran ta kai

Shugaba Saleh na Iraqi ya soki harin makamai masu linzami da Iran ta kai

Shugaban kasar Iraqi Barham Saleh a ranar Laraba 8 ga watan Janairu, ya soki hare-haren makamai masu linzami da Iran ta kai a sansanin sojojin Amurka da wasu sojojin kasashen ketare da ke kasar sa.

Saleh ya nuna fargabar yiwuwar 'tabarbarewar lamura' a yankin gabas ta tsakiya, ya yi Allah wadai ta keta hakkin kasarsa da ake yi tare da mayar da Iraqi filin yaki da kasashen biyu ke neman yi kamar yadda LIB ta ruwaito.

Sanarwar da ofishinsa ta fitar ya ce; "Munyi tir da hare-haren makamai masu linzami da aka kai a wasu sansanin sojoji da ke Iraqi kuma muna sake jadada rashin amincewar mu da keta 'yancin kasarmu da ake yi tare da neman mayar da Iraqi filin daga da bangarorin biyu ke neman yi."

Idan ba a manta ba dai a baya, Legit.ng ta ruwaito cewa gwamnatin Amurka ta tabbatar da cewa babu wani baamurke da aka kashe sakamakon hare-haren makamai masu linzami da Iran ta kai a sassanin sojojin Amurka da ke Iran.

DUBA WANNAN: Trump ya yi amai ya lashe kan barazanar kai hari wuraren tarihi a Iran

Kazalika, Shugaba Donald Trump na Amurka ya sake jadada cewa ba zai taba bari Iran ta samu makaman nukiliya ba muddin yana shugaban kasar Amurka.

Ya kuma bayyana cewa a shirye ya ke ya zauna a teburin sulhu da Iran duba da cewa akwai alamun ba yaki suke so ba tunda harin na su bai kashe kowa ba.

Trump ya kuma ce Amurka ba za ta mayar da martani da karfin soji ba sai dai za ta tsaurara takunkumin kasuwanci a kan Iran tare da kira da sauran kasashen Turai da NATO su bayar da gudunmawa don ganin an samar da zaman lafiya a yankin Gabas ta Tsakiya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel