Yakin Iran: Koriya Ta Yi Gwajin Injin Makami Mai Linzami da Zai Iya Kaiwa Amurka

Yakin Iran: Koriya Ta Yi Gwajin Injin Makami Mai Linzami da Zai Iya Kaiwa Amurka

  • Shugaban Koriya ta Arewa Kim Jong Un ya jagoranci gwajin sabon injin makami mai linzami domin karfafa rundunar soji
  • Amurka da Japan sun yi Allah wadai da wannan gwaji, suna masu bayyana shi a matsayin keta dokokin majalisar dinkin duniya
  • Wannan sabon injin yana da karfin tura nauyi kiloton dubu 2,500 domin kai hari har cikin babban yankin kasar Amurka

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Koriya ta Arewa - Shugaban Koriya ta Arewa, Kim Jong Un, ya jagoranci gwajin wani sabon injin makami mai linzami mai amfani da daskararren mai, cikin nasara.

Gwajin wanda aka gudanar a ƙasa, yana nuna shirin Kim na faɗaɗa tare da zamanantar da makaman da za su iya kaiwa har cikin babban yankin ƙasar Amurka.

Kotiya ta Arewa ta Arewa ta guana da gwajin injin makami mai linzami da zai iya kaiwa cikin Amurka.
Shugaban Koriya ta Arewa, Kim Jong Un, a lokacin gwajin makami da hoton wani gwajin makami a Koriya ta Kudu. Hoto: STR/KCNA VIA KNS/AFP and Handout via Getty Images
Source: Getty Images

An yi wa Koriya ta Arewa ca

Kara karanta wannan

Yakin Iran/Isra'ila ya fara sauya salo, jami'ai daga Rasha sun dura a Amurka

A ranar Lahadi, hukumar yaɗa labarai ta ƙasar Koriya ta Arewa (KCNA) ta bayyana cewa:

"Wannan gwajin injin yana da matuƙar muhimmanci wajen ɗaukaka ƙarfin sojin ƙasarmu zuwa mataki mafi girma."

Gwamnatocin Amurka, Japan, da Koriya ta Kudu sun gudanar da tattaunawa ta gaggawa ta wayar taraho inda suka yi Allah wadai da wannan sabon matakin na Kim.

Ma'aikatar harkokin wajen Japan ta fitar da sanarwa inda ta ce:

"Wannan mataki ya keta dokokin kwamitin tsaro na Majalisar Ɗinkin Duniya kuma yana barazana ga zaman lafiyar yankin."

Ita ma Amurka ta jaddada cewa tana sanya ido sosai kan yadda Koriya ta Arewa ke ƙoƙarin ƙera makaman da za su iya doke tsarin kariyarta na samaniya.

Nasarar gwajin injin makami mai linzami

Kim Jong Un ya sanya ido yayin gwajin injin ɗin wanda aka inganta ta hanyar amfani da wani nau'in sinadarin carbon fibre, inda injin ya nuna ƙarin ƙarfi fiye da na baya.

A cewar rahoton Sky News:

"Injin ɗin yana da ƙarfin tura nauyi har kiloton 2,500, wanda hakan ya zarce kiloton 1,971 da aka samu a gwajin watan Satumba."

Kara karanta wannan

Matakai 4 da Najeriya ta dauka bayan fara yakin Iran, Amurka da Isra'ila

Masana na ganin cewa wannan ƙarin ƙarfin yana da alaƙa da ƙoƙarin ƙasar na sanya kawunan yaƙi da dama a kan makami mai linzami guda ɗaya.

Koriya ta Arewa ta yi gwajin injin makami mai linzami da zai iya zuwa Amurka.
Shugaban Koriya ta Arewa, Kim Jong Un tare da diyarsa, Kim Ju Ae, yayin duba babbar na'urar harba makamin roka. Hoto: KCNA VIA KNS / AFP via Getty Images
Source: Getty Images

Koriya Ta Arewa A Matsayin Ƙasar Nukiliya

Wannan gwajin yana zuwa ne kwanaki kaɗan bayan da Kim ya yi jawabi inda ya sha alwashin tabbatar da Koriya ta Arewa a matsayin ƙasa mai ƙarfin nukiliya.

Shugaban ya zargi Amurka da yin amfani da "ta'addanci da zalunci" a duniya, inda ya yi ishara da rikicin dake faruwa a yankin Gabas ta Tsakiya.

Kim ya ƙara da cewa:

"Ya zama dole mu ci gaba da inganta dabarunmu na kai hari domin tabbatar da cewa babu wata ƙasa da za ta iya raina mu."

Koyiya ta Arewa ta harba makamai

A wani labari, mun ruwaito cewa, Koriya ta Arewa ta harba makamai masu linzami tekun Japan, bayan ta yi gargadi kan atisayen sojan hadin gwiwa tsakanin Amurka a kusa da ita.

Harin ya zo ne yayin da ake rade-radin yiwuwar haduwar shugabannin Amurka da Koriya ta Arewa a China, lamarin da zai iya sake bude kofar tattaunawa.

Sai dai gwamnatin Kim Jong Un ta soki kokarin zaman lafiya na baya-bayan nan, tana mai cewa ba za ta canza matsaya kan mallakar makaman nukiliya ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com