Ana tsakiyar Barin Wuta, Najeriya Za Ta Amfana da Yakin Amurka, Isra'ila da Iran
- Kamfanin NNPCL ya bayyana cewa yakin Gabas ta Tsakiya ya sanya kasashen duniya tururuwar neman iskar gas din Najeriya
- Najeriya tana kokarin fadada ayyukan iskar gas dinta domin cin gajiyar kusancin da take da shi da kasashen Turai da yankin Asiya
- Mataimakin shugaban NNPCL, Olalekan Ogunleye ya ce an raja'a kan gas din Najeriya saboda inganci da bukatarsa a halin yanzu
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Amurka - Mataimakin shugaban kamfanin man fetur na ƙasa (NNPCL), Olalekan Ogunleye, ya bayyana cewa rikicin da ake yi a Gabas Ta Tsakiya ya zama wata "damar kasuwanci" ga Najeriya.
A cewarsa, kasashen duniya yanzu haka suna matuƙar neman iskar gas ɗin Najeriya (LNG) sakamakon cikas ɗin da yaƙin tsakanin Amurka da Isra'ila a ɓangare ɗaya, da kuma Iran a ɗaya ɓangaren, ya jawo wa kasuwar makamashi ta duniya.

Source: Twitter
Yadda Najeriya za ta amfana da yakin Iran
Yayin da yake jawabi a taron makamashi na CERAWeek a birnin Houston, Ogunleye ya bayyana cewa masu sayen iskar gas yanzu sun karkata akalarsu zuwa Najeriya, in ji rahoton Channels TV.
Ogunleye ya ce hakan tana faruwa ne saboda kusancin Najeriya da manyan ƙasashe masu amfani da makamashi da kuma dimbin arziƙin iskar gas da take da shi.
Ya ce:
“Najeriya tana a tsakiyar kasuwar ne. Tazarar tafiyar kwanaki 10 ce kawai tsakaninmu da Turai, muna kusa da tekun Atlantic, kuma muna kusa da Asiya.
"Muna ganin damarmakin kasuwanci a daidai wannan lokaci da ake yakin Gabas ta Tsakiya, musamman saboda ingancin gas dinmu na LNG."
Manyan ayyukan iskar gas a Najeriya
Najeriya, ta hanyar kamfanin NLNG inda NNPC ke da mafi yawan hannun jari, tana da ikon fitar da tan miliyan 22 na iskar gas a kowace shekara.
A halin yanzu, ana aiwatar da shirin Train 7 na samar da gas wanda ake sa ran kammalawa a shekarar 2027, kamar yadda rahoton CNBC Africa ya nuna.
Kamfanin na NNPC ya fara tattaunawa kan ƙara fadada shirin zuwa Train 9, tare da wani babban aikin samar da iskar gas mai ƙarfin tan miliyan 12 a shekara (mtpa).

Source: Twitter
Jan hankalin masu zuba jari na duniya
Shi ma Karamin ministan albarkatun man fetur, Heineken Lokpobiri, ya bayyana cewa gwamnatin Najeriya ta samar da yanayi mai kyau ga masu zuba jari.
A wajen taron, Lokpobiri ya bayyana cewa ya gana da manyan kamfanonin mai na duniya irin su Shell, Chevron, Total, Eni, da ExxonMobil domin su dawo su zuba jari a Najeriya.
Ya jaddada cewa, “Ɗanyen man Najeriya yana ɗaya daga cikin mafi kyau a duniya,” sannan ya bayyana cewa Najeriya a shirye take ta yi kasuwanci da kowa.
Yakin Iran zai jawo tarnaki a Najeriya
A wani labari, mun ruwaito cewa, masana makamashi da kasuwar man fetur sun ce yakin Iran da Amurka na iya jawo sabon tashin farashin fetur a Najeriya.
Sun bayyana cewa idan farashin ɗanyen mai a kasuwar duniya ya haura Dala 90 kowace ganga, lallai hakan zai shafi farashin man fetur da dizal a cikin gida.
Shugaban Petroleumprice.ng, Olatide Jeremiah, ya ce duk da Najeriya ce babbar mai fitar da ɗanyen mai a Afrika, har yanzu farashin cikin gida na dogara da kasuwar duniya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


