Duba kuga yadda aka kasa kudaden da NLNG ta samar wa kasar nan a 2017

Duba kuga yadda aka kasa kudaden da NLNG ta samar wa kasar nan a 2017

- Kudin ya haura dala biliyan 2.1 da aka samu a shekarar 2016

- Rahoton ya nuna cewa dala biliyan 16.5 ne aka biya gwamnatin tarayya a matsayin ribar hannun jarin ta daga matatar man fetur ta kasa tun shekarar 1999

Duba kuga yadda aka kasa kudaden da NLNG ta samar wa kasar nan a 2017
Duba kuga yadda aka kasa kudaden da NLNG ta samar wa kasar nan a 2017

Gwamnatin tarayya, jiha da kananan hukumomi sun samu ribar dala biliyan 3.1 daga ribar hannayen jari, kudin haraji, ribar masana'antu da kuma wasu hanyoyin samun kudi na Nigeria Liquefied Natural Gas (NLNG) a 2017.

Kudin ya haura dala biliyan 2.1 da aka samu a shekarar 2016.

An samar da NLNG a 1989 don habaka fadada albarkatun gas da ake fitar wa, mallakin Gwamnatin tarayya, matatar man fetur ta kasa ke wakilta a kashi 49 cikin dari, kamfanin Shell na wakiltar da kashi 25.6,Total Gaz Electricite Holdings France na da kashi 15, sai Eni na da kashi 10.4.

DUBA WANNAN: An kashe dan shugaban ISIL

Majiyar mu ta ruwaito cewa a jiya ne bayanin kudin kamfanin ya fito na shekara 2018, wanda ya nuna ribar hannun jarin da NLNG ta biya matatar man fetur ta kasa, na kashi 49 dinta ya kai dala miliyan 798.1 a 2017, inda yafi na shekara 2016 da ya kama dala miliyan 365.1,mafi karanta a cikin shekaru 10 da suka gabata.

Rahoton ya nuna cewa dala biliyan 16.5 ne aka biya gwamnatin tarayya a matsayin ribar hannun jarin ta daga matatar man fetur ta kasa tun shekarar 1999.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng