Tirkashi: Trump Ya Fallasa Dabarar da Iran Take Amfani da Ita a Yaki da Isra'ila
- Shugaba Donald Trump ya gargaɗi duniya kan haɗarin amfani fasahar AI inda ya zargi Iran da ƙirƙirar hotunan yaƙi na ƙarya domin yaudarar duniya
- Shugaban Amurka ya yi iƙirarin cewa hotunan taron magoya bayan sabon jagoran addinin Iran Mojtaba Khamenei da ake yadawa ƙirƙirar AI ce kawai
- Hukumar FCC ta yi barazanar soke lasisin kafafen yaɗa labaran da ba sa bayar da rahotannin da suka yi daidai da manufofin gwamnatin Shugaba Trump
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Amurka - Shugaban Amurka Donald Trump ya zargi ƙasar Iran da yin amfani da fasahar AI a matsayin "makamin yaɗa labaran ƙarya" yayin da yakin Gabas ta Tsakiya ya shiga mako na uku.
Donald Trump ya ce Iran na amfani da wannan fasahar ne domin juya ra'ayin duniya kan nasarorin da take samu a yaƙin da ake fafatawa.

Source: Getty Images
Trump ya zargi Iran da amfani da fasahar AI
Shugaban kasar ta Amurka ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabi ga manema labarai a cikin jirgin shugaban ƙasa na Air Force One, kamar yadda Reuters ta ruwaito.
Trump ya gargaɗi duniya cewa fasahar AI tana da matuƙar haɗari idan ba a yi takatsantsan da ita ba, "musamman yanzu da Iran ta nace wajen amfani da ita."
Shugaban ya yi iƙirarin cewa kafafen yaɗa labarai na ƙasashen Yamma suna haɗa baki da Iran wajen yaɗa waɗannan labaran, inda har ma ya ba da misalai guda uku na abubuwan da yake ganin fasahar AI ce ta ƙirƙire su.
Misalai 3 na yadda Iran ke amfani a AI
Misali uku da Trump ya kafa hujja da su na cewa Iran na amfani da AI wajen yada labaran karya sun hada da:
1. Jiragen ruwa na "Kamikaze":
Trump ya ce Iran ta nuna wasu jiragen ruwan yaƙi masu dauke da bama-bamai waɗanda a zahiri babu su, kamar yadda ya wallafa a shafinsa na Truth Social.
Sai dai, rahoton The Sunday Guardian ya tabbatar da cewa an ga hotunan wasu jiragen ruwan Iran dake maƙare da bama-bamai suna kai hari kan wasu jiragen dakon mai a tashar ruwan Basra ta ƙasar Iraki.
2. Hari kan jirgin yaƙin USS Abraham Lincoln:
Shugaba Trump ya yi iƙirarin cewa Iran ta yi amfani da fasahar AI domin nuna cewa ta yi nasarar kai hari kan babban jirgin yaƙin Amurka na USS Abraham Lincoln.
Trump ya bayyana cewa duk wata kafar yaɗa labarai da ta wallafa wannan labarin ya kamata a tuhume ta da laifin cin amanar ƙasa.
3. Taron goyon bayan Mojtaba Khamenei:
Shugaban na Amurka ya kuma ce hotunan da ke nuna mutane kusan 250,000 sun fito taron nuna goyon baya ga sabon jagoran addini na Iran, Mojtaba Khamenei, ƙirƙirar AI ce kawai, domin a cewarsa taron ma bai taɓa faruwa ba.

Kara karanta wannan
Wata sabuwa: Ana cikin gwabza fada, Trump ya fadi bukatar da shugabannin Iran suka nema

Source: Getty Images
Alakar Trump da kafafen yada labarai
Wannan takaddama ta haifar da tsami tsakanin hukumar sadarwa ta Amurka (FCC) da gidajen rediyo da talabijin na ƙasar.
Shugaban hukumar FCC, Brendan Carr, ya yi barazanar soke lasisin gidajen yaɗa labaran da suka ƙi gyara salon rahotanninsu game da yaƙin.
Trump dai ya daɗe yana siffanta duk wani labarin da ya soki manufofinsa a matsayin "ƙarya", sannan yakan yi kira da a hukunta kafafen yaɗa labaran da yake gani ba sa yi masa adalci.
Trump ya tabo batun sulhu da Iran
A wani labari, mun ruwaito cewa, Shugaba Donald Trump ya bayyana cewa har yanzu Amurka ba ta shirya ƙulla yarjejeniyar kawo ƙarshen yaƙin da ake yi da Iran ba.
Trump ya nuna cewa ko da yake yana jin Iran na buƙatar tattaunawa, Amurka za ta ci gaba da kai hare-hare domin samun sharuɗɗa mafi tsauri.
Shugaban kasar ya bayyana hakan ne a wata hira da manema labarai, inda har ma ya yi barazanar sake farmakar matatar man fetur dake tsibirin Kharg domin nishaɗi kawai.
Asali: Legit.ng

