Cigaban ilimi: BUK ta kaddamar da gidan talabijin da rediyo a jahar Kano

Cigaban ilimi: BUK ta kaddamar da gidan talabijin da rediyo a jahar Kano

Shugaban jami’ar Bayero ta Kano, Farfesa Muhammad Yahuza Bello ya bayyana cewa tashoshin rediyo da gidajen talabijin na jami’a suna da muhimmin rawar da zasu taka wajen magance matsalar labarun kanzon kurege a Najeriya.

Bello ya bayyana haka ne yayin bikin kaddamar da tashar rediyo ta jami’ar Bayero mai zangon FM da gidan talabijin na jami’ar a sashin koyon aikin jarida a ranar Talata, 19 ga watan Feburairu, inda yace cigaban zai taimaka wajen horas da daliban jarida yadda ya kamata.

KU KARANTA: Zulum ya yi kira ga jama’an Borno su dauki azumi a ranar Litinin don neman taimakon Allah

Cigaban ilimi: BUK ta kaddamar da gidan talabijin da rediyo a jahar Kano
Cigaban ilimi: BUK ta kaddamar da gidan talabijin da rediyo a jahar Kano
Asali: Facebook

Farfesa Yahuza Bello ya kara da cewa tuni sun kulla wata yarjejeniya da gidan rediyon BBC domin horas da ma’aikatan tashoshin biyu, haka zalika yace hukumar jami’an na duba yiwuwar dabbaka sabon dokar fasa digirin koyon aikin jarida zuwa digirori 7, a kakan karatu mai zuwa.

A jawabinsa, shugaban sashin koyon aikin jarida na farko a BUK, kuma shugaban kwalejin kula da karatun gaba da digirin farko, Farfesa Umaru Pate ya bayyana cewa gidauniyar MacArthur Foundation ce ta tallafa ma jami’ar wajen samar da tashoshin biyu tare da zuba kwamfutoci 150.

Cigaban ilimi: BUK ta kaddamar da gidan talabijin da rediyo a jahar Kano
Cigaban ilimi: BUK ta kaddamar da gidan talabijin da rediyo a jahar Kano
Asali: Facebook

Pate yace BUK na daga cikin jami’o’i 12 da suka ci moriyar wannan tallafi na MacArthur a tsakanin Najeriya da kasar Ghana, don haka ya bada tabbacin za’a bayar da kulawar da ta dace ga kayan aikin, kuma za’a tabbata an yi amfani dasu ta hanyar da ta dace.

Daga cikin manyan baki da suka halarci taron akwai Ciroman Kano, Alhaji Nasir Ado Bayero, shugaban jami’ar Yusuf Maitama Sule Farfesa Mustapha Ahmad Isa, Daraktan gidauniyar MacArthur, Kole Shettima, Farfesa Lai Oso da shuwagabannin gidajen rediyo na Kano.

A wani labarin kuma, tsohon gwamnan jahar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya yi kira ga kotun kolin Najeriya da ta sake yin nazari tare da sake duba shari’ar gwamnan Kano da idon basira, wanda ta baiwa Abdullahi Umar Ganduje.

A watan da ta gabata ne kotun koli ta tabbatar da Abdullahi Umar Ganduje a matsayin halastaccen gwamnan jahar Kano, kotun ta tabbatar da hukuncin kotun daukaka kara ta yanke a kan sharia’ar, da ma kotun sauraron koke koken zabe.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel