Ba Sauki: Iran Ta Kai Hari Mai Zafi kan Sansanin Sojojin Amurka
- Amurka ta kai hari kan wani wurin tsaftacen ruwan sha a tsibirin Qeshm na kasar Iran yayin da ake ci gaba da gwabza fada
- Rundunar dakarun kare juyin juya halin Musulunci ta Iran (IRGC) ta mayar da martani ta hanyar kai farmaki kan sansanin sojojin Amurka
- Ministan harkokin wajen Iran Iran, Abbas Araghci, ya yi Allah wadai da harin na Amurka inda ya bayyana cewa taba abubuwa masu muhimmanci na kasar ba zai tafi a banza ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Birnin Tehran, Iran - Rundunar dakarun kare juyin juya halin Musulunci ta Iran (IRGC) ta sanar da cewa ta kai hari kan sansanin sojojin Amurka da ke Juffair, a kasar Bahrain.
Rundunar IRGC ta bayyana cewa ta kai harin ne ta hanyar amfani da makamai masu linzami.

Source: Twitter
Tashar Aljazeera ta kawo rahoton harin da rundunar IRGC ta kai kan sansanin na sojojin Amurka a kasar Bahrain a ranar Asabar, 7 ga watan Maris 2026.
Rundunar IRGC ta bayyana cewa wannan hari ya kasance ramuwar gayya ce kan harin da Amurka ta kai wa wata matatar tsaftace ruwa a tsibirin Qeshm na ƙasar Iran.
An yi Allah wadai da harin Amurka
Tunda farko Ministan harkokin wajen Iran, Abbas Araghchi, ya bayyana cewa harin na Amurka ya katse hanyoyin samar da ruwa ga ƙauyuka kusan 30.
Abbas Araghchi ya bayyana hakan ne a shafinsa na X yayin da yake yin Allah wadai kan harin da Amurka ta kai wurin tsaftacen ruwan.
Ministan ya bayyana cewa Amurka ta aikata laifi babba kan harin da ta kai a wurin wanda yake samar da ruwa ga kauyukan yankin.
"Amurka ta aikata babban laifi na rashin tausayi ta hanyar kai hari kan wurin tsaftace ruwan sha a tsibirin Qeshm. Hakan ya shafi samar da ruwa a ƙauyuka 30."
"Kai hari kan kayayyakin more rayuwa na Iran wani mataki ne mai haɗari wanda zai haifar da gagarumin sakamako. Amurka ce ta fara yin hakan, ba Iran ba."
- Abbas Araghchi

Source: Twitter
Halin da ake ciki a Bahrain
Ma'aikatar harkokin cikin gida ta ƙasar Bahrain ta sanar a shafinta na X cewa an kunna kararrawar gargaɗi kan yiwuwar kawo harin sama, inda ta buƙaci mazauna ƙasar su kwantar da hankulansu kuma su nemi mafaka a wurare mafi kusa da su.

Kara karanta wannan
Akwai matsala: Majalisar Dinkin Duniya ta hango abin da zai faru sakamakon yakin Amurka da Iran
Sanarwar na cewa:
"An kunna ƙararrawar gargaɗi. Ana kira ga 'yan ƙasa da mazauna ƙasar su kwantar da hankulansu kuma su garzaya zuwa wurare mafi tsaro."
Iran ta farmaki jirgin Amurka
A wani labarin kuma, kun ji cewa rundunar juyin juya halin Iran (IRGC) ta kasar Iran na ci gaba da kai hare-hare kan kadarorin Amurka da ke yankin Gabas ta Tsakiya.
Dakarun rundunar juyin juya halin Iran sun yi ikirarin kai hari kan wani jirgin yakin sojojin Amurka a jerin hare-haren da suke kai wa tun bayan barkewar yaki.
Rundunar ta yi alƙawarin ƙara faɗaɗa hare-haren zuwa wasu wurare da ta kira sansanonin abokan gaba.
Asali: Legit.ng
