Kasar Iran Ta Farmaki Wani Jirgin Yaki, Ta Kara Yi Wa Amurka da Isra'ila Babbar Illa

Kasar Iran Ta Farmaki Wani Jirgin Yaki, Ta Kara Yi Wa Amurka da Isra'ila Babbar Illa

  • Rundunar juyin juya hali ta Iran ta kai farmaki kan wanijirgin yaki kirar F-15E na Amurka yayin da aka shiga rana ta bakwai da fara musayar wuta
  • Sojojin IRGC sun sanar da kaddamar da zayage na 22 na hare-haren kare kai da ramuwar gayya da suke kai wa kan kayayyakin Amurka da Isra'ila
  • Gwamnatin Iran dai ta sha nanata cewa ba gudu ba ja da baya a wannan yaki, inda ta ce ba za ta yi kasa a gwiwa ba a kokarin kare kanta

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Iran - Dakarun rundunar juyin juya hali na kasar Iran (IRGC) na ci gaba da kaddamar da hare-hare da makamai masu linzami kan kadarorin Amurka da ke Gabas ta Tsakiya.

Wannan na zuwa ne yayin da aka shiga rana ta bakwai da fara musayar wuta tsakanin Iran da hadin gwiwar kasashen Amurka da Ira'ila.

Kara karanta wannan

Shugaba Trump ya bayyana sharadi 1 tak da zai iya kawo karshen yakin Amurka da Iran

Jiragen Amurka.
Jiragen yakin Amurka a sararin samaniya Hoto: Kevin C CoX
Source: Getty Images

A wani rahoto da tashar Al-Jazeera ta kawo yau Juma'a, dakarun rundunar juyin juya halin Iran sun yi ikirarin kai hari kan wani jirgin yakin sojojin Amurka.

Iran ta kai hare-hare zagaye na 22

Dakarun IRGC sun bayyana haka ne yayin da suke bayani kan hare-haren makamai masu linzami, zagaye na 22, da suka kaddamar kan sansanoni da kadarorin kasar Amurka da Isra'ila.

Dakarun na Iran sun sanar da fara zagaye na 22 na aikin soji mai suna “True Promise 4”, inda suka tabbatar da kai farmaki kan wani jirgin yaƙin Amurka F-15E, kamar yadda BBC Hausa ta kawo.

A wannan sabon zagaye, sojojin Iran sun harba makamai masu linzami da dama, ciki har da Khorramshahr-4, makamin Khaibar da kuma Fateh, waɗanda aka harba zuwa wurare daban-daban a Isra'ila.

Kasar Iran ta kakkabo jirgi mara matuki

Sojojin na Iran sun kuma bayyana cewa sun harbo wani jirgin sama maras matuƙi na Isra'ila mai suna Heron drone, wanda ke shawagi a sararin samaniyar birnin Isfahan da ke tsakiyar ƙasar.

Kara karanta wannan

Makaman Iran sun dura kan tankar man Amurka a teku, ta kama da wuta

Jiragen Heron su ne manyan jirage marasa matuƙi (UAV) da Isra’ila ke amfani da su, kuma an fara amfani da su a hukumance tun shekarar 2007.

Shugaba Trump.
Shugaban kasar Amurka, Donald Trump yana jawabi a fadar White House Hoto: Donald J. Trump
Source: Getty Images

Rundunar ta yi alƙawarin ƙara faɗaɗa hare-haren zuwa wasu wurare da ta kira “sansanonin abokan gaba.”

Gwamnatin Iran dai ta sha nanata cewa ba gudu ba ja da baya a wannan yaki, inda ta ce ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen kai hare-hare kan Amurka da Isra'ila domin kare kanta.

Iran ta farmaki tankar man Amurka

A baya, kun ji cewa dakarun Iran sun sanar da cewa sun kai hari kan wani jirgi dauke da tankar man Amurka a Arewacin Tekun Farisa.

Harin ya zo ne bayan Ministan harkokin wajen Iran ya yi gargadin cewa Amurka za ta yi nadama kan harin da aka kai kan jirgin ruwansu mai suna IRIS Dena a gabar tekun Sri Lanka.

Amurka ta kai hari kan jirgin Iran ne bayan rundunar IRGC ta bayyana a cikin wata sanarwa cewa ta dakatar da zirga-zirgar jiragen ruwa ta mashigin Hormuz.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262