Ronaldo Ya Lallaɓa Ya Bar Saudiyya saboda Rikicin Iran, Isra'ila? an Ji Gaskiyar Zance
- Yayin da rikici ke kara kamari a yankin Gabas ta Tsakiya,wasu rahotanni sun ce Cristiano Ronaldo ya bar Riyadh
- Majiyoyi sun ce Ronaldo mai kwallo a Al Nassr ya bar Saudiyya zuwa Madrid yayin da rikicin yankin ke tsananta a yankin
- Hakan na zuwa ne bayan hare-haren ramuwar gayya daga Iran kan Amurka da Isra’ila wanda aka fara a karshen mako
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Riyadh, Saudi Arabia - An yi ta yada cewa dan wasan kwallon kafa, Cristiano Ronaldo, ya bar Saudiyya yayin da rikicin Gabas ta Tsakiya ke kara tsananta.
Hakan ya biyo bayan hare-haren ramuwar gayya daga Jamhuriyar Musulunci ta Iran kan Amurka da Isra'ila.

Source: Getty Images
Sai dai dan jarida a bangaren wasanni, Fabrizio Romano ya karyata labarin a shafin X inda ya ce kwata-kwata babu gaskiya kan rahoton.

Kara karanta wannan
Bayan hari a Saudiyya, Iran ta gamu da farmakin Isra'ila, an gano asarar da aka yi
Rikicin Iran/Isra'ila ya dagula lamura a Saudiyya
Ma’aikatar Tsaron Saudiyya ta tabbatar da cewa jirage marasa matuka biyu sun kai hari ofishin jakadancin Amurka da ke Riyadh.
Hakan ya jawo dakatar da wasannin cikin gida da na nahiyar, inda AFC Champions League Elite ta sanar da dage wasannin zagayen 16 na yankin Yamma.
Hukumomin tsaro sun ce za su ci gaba da sa ido kan lamarin domin tabbatar da kare lafiyar ‘yan wasa da magoya baya, cewar Punch.
Yadda aka yada karya kan Ronaldo
Ficewarsa ta zo ne yayin da dubban mazauna yankin da baki ke barin Gabas ta Tsakiya sakamakon hare-haren da suka biyo bayan rikicin Isra’ila da Amurka, cewar Euronews.com.
Bayanai sun nuna cewa jirginsa mai zaman kansa ya tashi daga Riyadh da misalin karfe 8:00 na daren Litinin 2 ga watan Maris, 2026.
Majiyoyi sun nuna jirgin ya bi ta Masar da Bahar Rum kafin ya sauka Madrid da misalin karfe 1:00 na dare domin tsira daga rikicin da ke faruwa.

Source: Instagram
Gaskiyar labari kan guduwar Ronaldo daga Saudiyya
Fabrizio ya ce labarin da ake yadawa karya ne babu gaskiya kan cewa Ronaldo ya sulale zuwa birnin Madrid bayan rigima ta barke a Gabas ta Tsakiya.
Ya ce:
"Rahotannin da wasu kafafen yada labarai na duniya suka wallafa cewa Cristiano Ronaldo ya bar Saudiyya tare da iyalansa ba gaskiya ba ne.
Wannan labarin karya ne, domin a halin yanzu Cristiano yana jinya a filin atisayen Al Nassr bayan matsalolin da suka taso a wasansa na karshe.
"Cristiano bai bar Saudiyya domin komawa Madrid ba."
Dan wasan mai shekaru 41 yana taka leda a kungiyar Al-Nassr tun bayan komawarsa daga Manchester United a Disambar shekarar 2022.
Rahotanni sun ce yana samun kusan fam dubu 488,000 a kullum bisa yarjejeniyar kwantiraginsa mai tsoka da kulob din Saudiyya.
An dakatar da Ronaldo a Saudiyya
A baya, an ji cewa fitaccen dan wasan kwallon kafa a duniya, Cristiano Ronaldo ya shiga matsala kan wani rashin da'a da ya yi a Saudiyya.
Hukumar kwallon kafa ta kasar ce ta dakatar tare da kuma cin tararsa kan nuna rashin da'a da ya yi a wasan da aka gudanar a gasar kasar da ake yi.
Har ila yau, hukumar bayan dakatar da shi ta kuma ci tararsa dala dubu takwas ba tare da daukaka kara ba wanda ya jawo magana a kafofin sadarwa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

