Yadda Harin Ramuwar Iran Ya Tilastawa Isra'ila Ɓoye Jirgin Netanyahu a Jamus
- Isra’ila ta mayar da jirgin gwamnati zuwa Jamus bayan Iran ta rike wuta wajen kai harin ramuwar gayya ƙasar Yahudawan
- Iran ta nanata cewa ba za ta saurara wa kowa ba bayan harin Amurka da Isra'ila ya hallaka Ayatollah Khamenei
- Jirgin “Wing of Zion” na dauke da na’urorin sadarwa na zamani masu tsaro, kuma shi ne jirgin da Benjamin Netanyahu ke hawa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Ƙasar Germany –Gwamnatin Jamus ta tabbatar da cewa ƙasar Isra'ila ta ajiye jirginta na gwamnati a ƙasar domin kariya yayin da ake fuskantar hare-hare daga Iran.
Mai magana da yawun Firaministan Jamus, Friedrich Merz, ya ce an ba Isra’ila damar ajiye jirgin ne bayan sun nemi hakan a hukumance.

Source: Getty Images
TRT ta wallafa cewa da yake magana a wani taron manema labarai a Berlin, Stefan Kornelius ya bayyana cewa babu wani jami’in gwamnatin Isra’ila a cikin jirgin lokacin da ya sauka a ranar Asabar, 28 ga watan Fabrairu 2026
Jamus ta amince da buƙatar Isra’ila
Reuters ta ruwaito cewa Kornelius ya ce gwamnatin Isra’ila ta tuntubi Jamus domin neman izinin ajiye jirgin a Berlin, kuma gwamnatinsa ta amince da buƙatar.
Ya ce:
“Gwamnatin Isra’ila ta tambaye mu ko za su iya ajiye jirgin nan a nan. Mun amince da buƙatar.”
Ya ƙara da cewa ma’aikatan jirgin kaɗai ne suka zo tare da shi, babu Firaminista Benjamin Eko wani babban jami’i a cikinsa.
Jirgin, wanda ake kira “Wing of Zion,” ya bar Isra’ila a ranar Asabar, lamarin da ya haddasa ce-ce-ku-ce a shafukan sada zumunta cewa ko Firaminista Benjamin Netanyahu na kan hanyarsa ta zuwa Jamus.
Sai dai daga baya aka tabbatar da cewa babu wani jami’in gwamnati a cikinsa, illa jirgin ne kawai aka adana saboda tsaro.
Jirgin Isra'ila ya yi shawagi kafin zuwa Jamus
Bayanan bin diddigin jirage sun nuna cewa jirgin ya tashi daga Isra’ila da yammacin Asabar 28 ga watan Fabrairu, 2026.

Source: Facebook
Rahoton ya ce jirgin ya yi ta shawagi na tsawon sa’o’i a saman Tekun Bahar Rum kafin daga bisani ya nufi Jamus.
Ya sauka a birnin Berlin a wannan dare bayan ya gaza sauka a Isra'ila yayin da Iran ke kara harba bama-bamai.
An ƙera jirgin Boeing 767 domin manyan shugabanni da shugaban ƙasa da Firaministan Isra’ila, inda ake amfani da shi wajen tafiye-tafiye zuwa ƙasashen waje.
Rahotannin kafafen yaɗa labarai na Isra’ila sun ce jirgin na ɗauke da na’urorin sadarwa na zamani masu matuƙar tsaro, wanda ke bai wa shugabanni damar gudanar da harkokinsu ko da suna sama.
Matakin mayar da jirgin zuwa Jamus na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da tashin hankali tsakanin Isra’ila da Iran, lamarin da ya sa aka ɗauki ƙarin matakan tsaro domin kare muhimman kadarorin gwamnati.
Iran za ta rama harin Amurka da Isra'ila
A baya, mun wallafa cewa Iran ta tabbatar da mutuwar jagoran addinin kasar, Ayatollah Ali Khamenei, a hare-haren Amurka da Isra’ila da aka kai masu hari gida.
Gwamnatin Iran ta ayyana kwanaki 40 na zaman makoki da hutun kwanaki bakwai domin jimamin wannan babban rashi da ya same su tare da zaman makoki.
Rundunar tsaron ƙasar ta IRGC ta yi alkawarin ɗaukar fansa kan waɗanda ta ce sun kashe jagoran addini na ƙasar ba tare da an yi masu laifin komai ba.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


