Amurka: Ɗan Bindiga Ya Tare Limamin Masallaci, Ya Bude Masa Wuta da Bindiga
- Wani dan bindiga ya bude wa motar Imam Shuaib wuta a jihar Utah ta kasar Amurka a lokacin da ake gudanar da azumin Ramadan
- 'Yan sanda da jami'an FBI sun fara bincike domin gano dan bindigar da kuma dalilin kai wannan hari na kisan gilla kan limamin
- Hukumar CAIR ta yi alkawarin bayar da ladar dalar Amurka 5,000 ga duk wanda ya bayar da bayanin da zai kai ga kamo maharin
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Amurka - Wani mahari da ba a tantance ko wanene ba ya buɗe wa motar limamin cibiyar Musulunci ta Utah, Imam Shuaib, wuta a garin Sandy da ke jihar Utah a daren ranar Litinin.
Jami'an ƴan sandan Sandy sun tabbatar da cewa maharin ya yi harbi "sau da dama" a kan motar limamin lokacin da ya tsaya a kusa da motarsa.

Source: Getty Images
An budewa motar limami wuta a Amurka
Ko da yake harsasai da dama sun samu motar, Imam Shuaib bai samu rauni ba kamar yadda jaridar The National ta ruwaito.
Imam Shuaib ya bayyana cewa maharin ya fito ne daga motarsa sannan ya buɗe masa wuta. Ya ce tsinci harsasai takwas waɗanda duka suka huda motarsa, amma cikin ikon Allah bai sami rauni ba.
Limamin masallacin ya bayyana cewa:
"Ya ajiye motarsa kusa da tawa, ya fito daga motar, sannan ya buɗe wa motata wuta... harsasai takwas aka tsinta a cikin mota tawa, kuma duka sun huda ta, amma ba su same ni ba."
'Yan sandan Amurka sun yi martani
Sajan Michael Olsen na rundunar ƴan sandan Sandy ya bayyana cewa sun haɗa gwiwa da hukumar bincike ta FBI domin gano maharin da kuma dalilin kai wannan hari.
Wannan hari ya auku ne a dare na shida na watan Ramadan, wanda hakan ya ƙara jefa fargaba a zukatan musulman yankin.
Sakamakon wannan hari, rundunonin ƴan sanda a birane daban-daban na jihar Utah sun tura jami'ai domin kare masallatai irin su Khadeeja Islamic Center, Masjid Al-Noor, da Madina Masjid a cikin kwanaki masu zuwa.
Al'ummar musulmi sun jaddada cewa ba za su daina taruwa domin ibada ba duk da wannan barazanar, cewar rahoton Fox 13.

Source: Getty Images
Akwai ladar $5,000 bayan kai wa liman hari
Cibiyar CAIR, wadda ita ce babbar cibiyar kare haƙƙin musulmi a Amurka, ta yi alkawarin bayar da dalar Amurka dubu biyar ($5,000) ga duk wanda ya bada bayanin da zai kai ga kamo maharin.
A sanarwar da ta fitar a shafinta na X, CAIR ta kuma yi kira ga jami'an tsaro da su ƙara tsaurara matakan kariya ga limamin da daukacin al'ummar musulmi a yankin.
Wannan lamari ya jawo hankalin duniya kan yadda ake samun ƙaruwar kyamar musulmi a wasu sassan duniya, musamman a cikin wannan watan mai alfarma.
Limami da aka harba a Amurka ya mutu
A wani labari, mun ruwaito cewa, Antoni Janar na New Jersey ya sanar da rasuwar wani babban limamin masallacin New Jersey da aka harba da bindiga.

Kara karanta wannan
DSS na shirin gayyatar yaran El Rufa'i, matar Dadiyata ta yi magana kan dauke mijinta
An harbi Hassan Sharif a wurare daban-daban a jikinsa a harabar masallacin da ke Newark, yamma da New York, inda ya mutu jim kadan bayan kai shi asibiti.
Rahotanni sun nuna cewa tun bayan barkewar fada tsakanin Isra'ila da Hamas, aka samu karuwar yawaitar kai hare-hare kan Musulmi a Amurka.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

