Isra'ila Ta Jibge Dakaru, Ta Kakaba wa Musulmi Takunkumin Shiga Masallacin Kudus

Isra'ila Ta Jibge Dakaru, Ta Kakaba wa Musulmi Takunkumin Shiga Masallacin Kudus

  • Isra’ila ta takaita shigar Falasɗinawa zuwa masallacin Kudus a Juma’ar farko ta watan Ramadan domin su yi sallah
  • An kayyade mutum 10,000 kacal daga Yammacin Kogin Jordan ne ke da izini na musamman da zai ba su damar shiga masallacin
  • Ta kuma saka adadin mutanen da za ta bari su shiga masallacin, su ma sai suna da takardar neman izini ta musamman

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Kasar Palestine – Isra’ila ta kakaba tsauraran matakai kan shigar Falasɗinawa zuwa harabar Masallacin Kudus da ke Gabashin Kudus da ta mamaye.

Ta jibge tarin jami'ai tare da hana Musulmin sallah a Juma’ar farko ta watan Ramadan, inda ake fatan a samu sallah.

Isra'ila ta sa wa Musulmi takunkumi kan shiga masallacin Kudus
Wasu daga cikin Musulmin da ke sallah a Baitul Mukaddas duk da takurar Yahudawa Hoto: Dr. Muhammad Salah
Source: Facebook

Aljazeera ta wallafa cewa daruruwan mutane ne suka yi jerin gwano a mashigar Kalandiya kusa da Ramallah, suna fatan samun damar shiga domin gudanar da sallar Juma’a.

Kara karanta wannan

'Sai kun biya N100m': 'Yan bindiga sun rubuta wasika, za su yi wa'azi a Ramadan

Isra'ila ta hana Musulmi salla a Kudus

TRT ta wallafa cewa sai dai hukumomin Isra’ila sun bayyana cewa ba za su bari mutum 10,000 daga Yammacin Kogin Jordan da aka mamaye su shiga.

Su ma ba za su shiga ba sai suna da takardar izini ta musamman. Wannan adadi kadan ne idan aka kwatanta da dubunnan masallata da ke shiga masallacin a shekarun baya.

Isra'ila ta kuma gindaya sharudda cewa yara ‘yan kasa da shekara 12 kawai, maza masu shekaru sama da 55, da mata masu shekaru 50 zuwa sama ne za su cancanci neman izinin shiga.

Rahotanni sun ce zuwa safiyar Juma’a, kimanin Falasɗinawa 2,000 ne kacal suka samu nasarar tsallakawa ta mashigar Kalandiya zuwa Kudus.

Sun tsallake ne a daidai lokacin da sojojin Isra’ila ke cikin shirin ko-ta-kwana a dukkanin mashigai da ke raba Yammacin Kogin Jordan da Gabashin Kudus.

Miliyoyin musulmi na fatan shiga masallacin Kudus

Akalla miliyan 3.3 a mashigar 'Kalandiya a Yammacin Kogin Jordan da aka mamaye, don haka barin mutum 10,000 kawai su yi sallah a Juma’ar farko ya shiga hakkinsu aini=un.

Kara karanta wannan

DSS na shirin gayyatar yaran El Rufa'i, matar Dadiyata ta yi magana kan dauke mijinta

A shekarun baya, an saba ganin masallata har 250,000 suna taruwa a wannan wuri mai tsarki. Amma a bana, ana sa ran adadi kadan ne daga Yammacin Kogin Jordan.

Isra'ila ta ce mutum 10,000 kawai za ta bar su yi sallah a masallcin
Firayim Ministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu Hoto: Benjamin Netanyahu
Source: Facebook

Ana kuma sa rai da cewa wasu mutanen kalilan daga Gabashin Kudus da kuma Falasɗinawa ‘yan asalin Isra’ila za su samu damar shiga masallacin.

Sababbin takunkuman na zuwa ne a daidai lokacin da hukumomin Falasɗinu, kungiyoyin kare hakkin dan Adam da Majalisar Dinkin Duniya ke gargadin kan yankin.

Sun ce akwai karuwar tashin hankali daga Yahudawa 'yan kama wuri zauna da sojojin Isra’ila a Yammacin Kogin Jordan da Gabashin Kudus da aka mamaye.

Yahudawa sun kai hari masallacin Kudus

A wani labarin, kun ji cewa wasu 'yan Isra'ila tsaurin ra’ayi sun kai hari a harabar Masallacin Al-Aqsa da ke Gabashin Kudus, lamarin da ya jawo fargaba a yankin.

Rahotanni sun ce mutanen sun kutsa cikin masallacin ne tare da rakiyar jami’an tsaron Isra’ila da suka ba su kariya, sannan suka kaddamar da harin ana kallonsu.

Sanarwar da ta fito daga ofishin kula da harkokin masallacin ta bayyana cewa kimanin Yahudawa 130 ne suka shiga harabar wurin ibadar a wannan karon.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng