Rikicin birnin kudus: Wani matashin Falasdinu ya caka ma Sojan Isra’ila wuka (Hotuna da bidiyo)
Wani Sojan Isra’ila ya sha da kyar bayan da wani matashin Falasdinu ya caka masa wuka a kafada a ranar Lahadi 10 ga watan Disamba a birnin Jerusalem, kamar yadda Legit.ng ta ruwaito.
Sai dai jami’an tsaron Israila sun yi nasarar cafke matashin yayin da yayi yunkurin tserewa, inda suka bayyana sunan shi, Yassin Abu Al-Qarah, wanda a kwanakin baya ya bayyana matsayinsa game da birnin kudus a shafinsa na Facebook, inda yace ‘Na bada jini nag a birnin kudus’.
KU KARANTA: Rashin Kamo Shekau ba shi ne dalilin da yasa Buratai ya canza ni ba – Manjo Janar Attahiru
A yanzu dai, jami’in da aka kwantar na cikin mawuyacin hali, inda yake samun kulawa a asibitin yahudawa dake birnin na kudus, inji rahoton muryar Amurka.
Ga bidiyon nan, kamar yadda Muryar Amurka ta kawo shi:
Ana sabunta rikici a tsakanin Isra’ilawa da Yahudawa yankin birnin kudus tun bayan matakin da shugaban kasar Amurka Donald Trump ya dauka na ganin ya mayar da babban birnin kasar Israila daga Tel Aviv zuwa birnin kudus, wanda hakan ke alanta cin mutunci ga Musulman Falasdinu.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng